← Book details Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 59

Sashe 52

Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haroon dayake kallan Dad Lameenu dayake numfashi ahankali ahankali alaman ba cikakkiyar lafiya mayar da kallansa yayi gurin Dad dinsa Wanda ya dago jajayen idanuwansa yayi masa kallo Daya na tsaftan gaske ya tabbatarda Haroon ne a gabansa take ya daga hannu ya sauke masa wani mahaukacin Marin Daya Saka gefen bakin Haroon din fashewa da jini.

Dagowa yayi bakinsa na jinin ya Kalli Dad din sedai wani Marin Dad ya sake saukar masa Mai zafin dayafi na farko.
#MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
51
Radadin Marin Kai tsaye a zuciyarsa yake sauka wadda take tarwatsewa aduk lokacinda mahaifinsa ya Saka masa hannu duk shekarun dayake dasu Wanda da yayi auren wuri da tini ya Tara Yara biyu ko uku.

Jajir idanuwansa sukai a karo na farkon dayaji zuciyansa na tabbatar masa da shidin ba komai bane a Gurin Dad Kuma har abada bazai taba zama komai ba a gurinsu,

A zero yake gabansu Kuma a haka zaici gaba da zama..

Yanda zuciyarsa ke radadi da qunan dayake tafasa jininsa haka ta Dad dinsa ke tafasa ya kallesa da jajayen idanuwansa yace

"Ayau nayi baqin kasancewa Wanda ya haifeka,
Nayi baqin ciki da Dana sanin barinka a qarqashin inuwata sbd har abada bazaka taba zama me amfani ba,
A yanda Aleena ta haifeka ba komai cikin kanka haka ka girma Babu komai a cikin kan naka dayekeda amfani ko buga Maka lissafi Mai amfani........

Tsananin 'dacin maganganun ya Saka Haroon rintse idanuwansa dasuke tsananin radadi sbd Jan da suke qarawa hannuwansa na rawa kansa na sarawa ahankali ahankali Yana qara qarfi.

Dad Lameenu da ayau tsaban shock baida karfi ko kadan a zaune yake Yana Jan numfashin wahala da 'dacin zuciya Bude Baki yayi yace

"Ban taba daukan karshenmu a hannunka zai faro ba Haroon sai ayau din,
Ban taba sanin jinin kafiran dayake yawo a jininku na mahaifiyarku zai taba aiki a kanku ba wataran sai yau,
Haroon Ashe bakada Imani bakada ha nkali???
Tin yaushe ne Jamaal yake acikinmu batareda mun saniba???
Tin tsawon yaushe muke kirari muna dabawa kanmu wuqa a gabansa batareda mun saniba??
Jamaal da yayi alkawarin saiya mayar damu mabarata kafin ya San sirrinmu kenan yanzu Daya San hatta yanda muke kalan numfashinmu kana tinanin a mabaratan zai barmu yanzu???
Wlh Jamaal Saiya tabbatarda ko Baran idan munyi bazaa bamu sadakar ba..... innalillahi wainna ilaihirrajiun,. innalillahi wainna ilaihirrajiun,

Kallan Mam yayi jininsa na sake hayewa a rikice yace

"Wlh mamman Jamaal bazai rasa hada kwararan shedu akanmuba,
Bazai rasa recording na wasu maganganunmu ba......

Kirjinsa ne ke Neman rikewa Dan haka BB Dake tsaye Yana jiquwa da zufan Shima yowa kan Lameenu Yana masa fifita duk da sanyin AC Daya cike office din tsaf Amma dukkaninsu a jiqe suke da zufa.

Mam dayakeji zuciyarsa na tinkudo masa baqin cikin duniya da bacin Rai kallan Haroon yayi Wanda jikinsa keta tsananin rawan Dayake nuna da ciwonsa yafara tasowa Daman gashi tinda ya dawo mum Atee ta Dora daga inda ta tsaya.

"Haroon kaman yanda ka ha'ince ni kabi shawaran Dan uwanka da mahaifiyarsa kuka sakani wannan baqin cikin wlh saina nin ka masa Wanda yafisa Dan bazaka auri wannan yarinyarba wallahi indai nine na haifeka,
Bazaka samu farin cikin dakake tinanin zaka samu ba idan ma ka gujeni ka komawa mahaifuyarka,

Kaman yanda kuka rusamu wlh dakai zamu dawwama acikin wannan baqin cikin da rashin Dan kuwa idan baka sani ba ka sani wannan ciwon haukan Daya kwakwalwanka Babu inda zan zaka Daya wuce na tattara ka na aikaka asibitin mahaukata Koda kanka zai Bude,

Idan har lissafina ya buga daidai Dan uwanka yanda yake kwararren likita na tabbata ya karanci yanayinka Kuma bazai rasa bincike akan abinda ya fahimta tareda Kai ba Dan haka zuwa yanzu yasan mummunan Nisan da qwaqwalwanka yayiba a Juyewa Dan haka ka Saka aranka Babu maganar aurenka gobe wlh....

Dad Lameenu dayake cikin mawuyacin hali har lokacin dagowa yayi yace

"Yanda Babbah ke son 'yarsa har abada bazai tabawa me tabin kwakwalwa auren yarsa ba kome zaayi kuwa Dan Haka takardun asibitinka kawai zamu basa a Daren ba sai gobe ba,
Maza ma ka fice ni ko ganinka Haroon a yanzu banason yi qaramin hawan jini yakeyi,
Ka cucemu Kaci amanar mu Kaci amanar kaunar da mahaifinka yake Maka.

Zuwa lokacin Haroon ba iya hannuwansa kadai ne suke rawa ba dukkanin jikinsa jijjiga yakeyi sosai hakama kansa tini yayi wani irin mugun nauyi Yana Neman inda zai fara bugasa bakinsa yakeson budewa Yayi magana Amma Dad Shima ko ganinsa bayason yi a lokacin sbd zai iya masa Baki idan Bai bar gurinba Dan haka Dad dinne ya fice Kai tsaye ko gabansa Baya Gani sbd Shima jininsa yayi mugun hawan Daya wuce misali.

Daqyar yakai kansa cikin gida yayi samansa ya shige bedroom dinsa Dan har lokacin Babu kowa a gidan Yan biki suna gurin bikin.

Dad Lameenu ma BB ne ya taimaka masa ya fice.

BB ne ya dawo office din ya kama Haroon daya qanqame gabaki Daya Yana rawan jiki sosai yakaisa har palonsa ya dawo ya rufe office din ya fice daga Mansion din.

Haroon rarrafawa yafara yi idanuwansa na ganin duhu da haske yafara kokarin Kai kansa bedroom Amma ya kasa sbd wani kifewa da yayi akan console mirror dayake hanyar bedroom din ya fado masa ya fashe.

Bugawa kansa keyi sosai hakama hannuwansa rawarsu ta tsananta sosai har tayi muni hakanan ya sake dafawa ya tashi cikin glass din Yana dafa Bango ya Isa kofar dakinsa yana shiga ya zube qasa Yana buga kansa sosai a tiles idanuwansa Dake rufe suna sake birkicewa.

Siddeeq kaman yasan abinda yake faruwa a mansion din ya dawo daukan Haroon sbd acanma Haroon jikinsa ya rikice zazzabi Mai karfin gaske da Bai taba yin irinsa ba ya rufesa Wanda ya bawa siddeeq tsoro hakama mum datake Kiran yayan nata Babu me dauka siddeeq din ta kira tanajin Jamaal ba lafiya taji hankalinta ya tashi Amma Kuma wannan Karan rashin daukan wayar Haroon yafi daga hankalinta fiyeda ciwon Jamaal Dan haka tace siddeeq ya dubo mata mansion din zuciyarta takasa samun nutsuwa.

Koda siddeeq ya Isa halinda ya samu Haroon yayi mugun girgizasa Dan Bai taba ganinsa a irin wannan mugun halinba duk tsananin ciwonsa kuwa.

Da gudun gaske ya qaraso inda yake ya tallafosa sedai Haroon din yayiwa kansa mummunan rauni jini Tako ina Dan haka a haukace ya daukosu gaba Dayansa ya fito dashi Bai tsaya wata wata ya Saka mota sbd ba qaramin munu lamarin yayi ba ya fice dashi zuwa asibitin SEELAHs din da gudun gaske.

Yana Isa aka karbi Haroon din da gaggawa Dan tini ya fice hayyacinsa Wani jijjiga kawai yakeyi sosai kaman me wani ciwon daban.

Fadan tashin hankalin da siddeeq ya shiga a wannan lokacin bamai yiyu bane sbd ya shiga tsoro Mai girma wannan Karan da ciwon Haroon din ga Jamaal a kwance ba lafiyan Shima.

Haroon sosai ya wahala cikin azaban ciwonsa Babu uwa Babu Uba Babu wani nasa sai siddeeq Wanda ya tsayu akansa har Saida ya dawo daidai sbd cikin qanqanin lokaci Allah ya mayar dashi kaman ba shine angon da zaa daurawa gobe ba.

Duk karfin zuciyarsa siddeeq sai dayaji tausayin Haroon ya karyasa sbd bayan dawowansa daidai Hawaye ne masu tsananin zafi da radadin zuciyan gaske suke gangaro masa batareda yace komaiba.

Sallan magrib siddeeq yake yaji daga can ya koma hotel ua dubo yanayin Jamaal Wanda ya Riga ya miqe haryayi wanka yayi Sallah
Siddeeq din na zuwa ya sanarwa da Jamaal halinda Haroon yake ciki.

Karban key Jamaal yayi shi kadai ya nufi asibitin gurin Dan uwansa.

Zuwansa asibitin Haroon na ganinsa hawayen tsananin kaunar Dan uwansa daya tabbatarda duk duniya ko mum dinsa Kila Baya kaunarsa yanda Jamaal din yake sonsa ne suka ciko idanuwansa suna gangarowa.

Jamaal Daya kasa masa maganar abinda ya faru ayau din sbd ganin yanayinsa daukansa yayi suka baro asibitin Babu me magana shiru kowa da abinda yake tinanin Amma dai shi Haroon zuciyarsa da jikinsa gaba Daya a Sanyaye suke sbd rayuwarsa yasan daga yau ta dena moruwa ne sbd aurensa dayasan har abada Dad bazasu taba barin ayi aurenba,

Rasa Ameenatou garesa tamkar zare control na tabin kwakwalwansa ne kaman yanda su Dad suka fada Dan haka idan har tabbas gobe ya tabbata ya rasa Ameenatou to ya cire Rai daga komawa daidai,
Yasan Jamaal da mahaifiyarsu zasu shiga tsananin qunci da baqin ciki akan Hakan Amma Shima kansa a yanzu yasan ko da auren Ameenatou ko Babu tabbas tabin kwakwalwa ne a tattare dashi me tashi Kuma me tsananin gaske.

Rintse idanuwansa yayi ahankali maganganun Dad da fushinsa da Bai taba Ganin irinsaba suna dawo masa a kunnuwansa take yaji ciwonsa na Neman sake dawowa ya dago jajayen idanuwansa ya Kalli Jamaal dayake tuqi a natse Shima zuciya da kansa duka a jagule da lissafi kala kala.

Cikin wata murya me sanyin gaske data Saka zuciyar JAMAAL sanyi akan fushi da bacin ran dayake ciki akansa
yace

"Jamaal,
Kayi mun alkawarin ganin na auri macen danake so matiqar ba Allah yariga yayi cewan ba matata bace,
Ko ban auri AMEENATOU a gobe ba Kai inason ka sheda itace macen danake so fiyeda komai a duniya bayan Kai da mum,
Son AMEENATOU wata jarabtace da Allah ya jarabceni da ita,
AMEENATOU itace macen da zanso har karshen rayuwata Kuma itace mace Daya da bayan ita Babu macen da Nima zan iya so.

Ko ban auri AMEENATOU ba bazan iya rabuwa da ita ba Dan haka Dan Allah Jamaal Karka bari su dadi su hanani samun farin cikin aurenta,

Aurenta shine Abu na karshe da zanzo kafin rayuwata tabar duniya.......
Chapter 52 · 0% Book details