← Book details Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 59

Sashe 18

Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan gyara tsayuwa BB yayi Yana kallan Lameenu Daya zuba masa ido Yana jiran sauran bayanin yaji Shima wani zufa ya tsitsifo masa sbd abinda zai fada yace

"Cikin gawawwakin da aka samu an samu tantancewa da tabbacin akwai ta matar sir Omar din Amma Kuma Babu ciki a jikin gawar Wanda ni Kuma ta tabbatarda naga tsohon ciki a tareda ita a Daren........

Ruwan da Mam ke Sha ne suka dawo ta hancinsa gaba Daya ba shiri sbd mummunan tashin hankalin da Bai taba Jin irinsa ba.

Lameenu kuwa take bugun zuciyarsa ya Nemi tsayawa cak sbd firgicin da Bai taba samun kansa ciki ba.
#MAMUH#
#AMEENATOU
#DR J SEELAH
#DESTINED
#LOVE
#ROMANCE
#LIFE
#REVENGE
#HAROON SEELAH
#IDENTICAL TWINS
#ZAFIN KAI
#THE SEELAHS

ASHNA BEAUTY SKINCARE
Free class free class 
Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta
Carwash
Airfreshner
Liquid soap
Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058
Karku Bari wannan damar ta wuceku

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
17
Shi kansa BB zufan yaje hadawa zuciyarsa na tsalle Dan yasan ansamu babbar matsala data jawo musu wani Sabon aikin me girma daban.

Mam kuwa bayan ta hanci da ruwan suka biyo bar cikin kansa sukai yaji Yana Neman zaucewa da sauri ya dago idanuwansa da suka sauya take zuwa jajir ya Kalli BB dukkanin jikinsa na Neman sakewa daqyar ya hado kalmomi a bakinsa cikin sanyi da nutsuwan son fahimtar komai daki daki yace

"Wane ciki kake Bada tabbacin ka Gani a jikin matar Omar?
Na haihuwan Dan mutum kokuwa na samun qoshi datai a gidan??".

Kansa ya saukar kasa bayan ya Kalli lameenu Wanda shi kwata kwata Neman rasa gane komai yakeyi
Ya Dan sake saukar da kansa qasa yace

"Tabbas cikin haihuwa ne a jikinta,
Kuma kaman yanda Daya daga cikin securities dinmu Dake ganin gidan ya tabbatar mana tabbas tana daukeda juna biyu tsoho matar Sir Omar din..

Hakama a Daren Koda muka shiga ni naga cikin da idanuwana sedai abinda yasa ban fada ba na dauka ba amfani tinda itada cikin sun tafi kenan sai gashi ance Babu ciki a jikin gawarta hakama baa samu gawar baby Koda konanniya ce a gidan,
Gashi Babu sauran mutum biyu Daya kamata Suma ace an samu gawarsu a gidan,
Dame aikinta Daya Wanda kowa ya tabbatarda masu aikinta biyu ne hakama a Daren ranar shi Sir Omar din yayi baqo Wanda bamusan ko wayeshi din ba a gun sir Omar din
a cikin gidan ya kwana muma da idonmu mun gansa mun sumar dashi Amma baa samu gawarsu ba.....

Jinin Mam da lameenu wata irin qunar masifaffen tashin hankali sukeyi musamman Lameenu da idanuwansa suka rufe baiga cikinba da Saiya tabbatarda a tsakiyar cikinta zai kutsa azabbiyar wuqarsa me barka kayan cikin mutum ya tabbatarda mutuwar haihuwar magaji ko magajiyar Omar jeden seelah.

Mam kuwa a Karan farko da zufar tashin hankali mara misaltuwa ta rufesa sbd babbar babbar uwar matsala da budaddiyar masifa ta riga ta fadowa rayuwarsu tinda Omar ya rufesu akan samun haihuwarsa hakama idan har Babu ciki a jikin gawa Kuma Babu gawar baby a gidan to ta tabbata Omar ya boye abinda aka haifar masa hakama idan ya boye abinda ya Haifa Hakan na nufin ya San wani abu Dan bazai yiyu Babu komaiba Omar ya boye musu haihuwarsa ta farko daya kamata ace sune sukaiwa abinda aka haifar huduba Dan shine kaf yakewa nasu yayan huduba.

Wace sabuwar masifar ce wannan ta bullo musu?
Me Lameenu yayi?
Tayaya zaace yaje yayi aiki irin wannan da kansa Amma ya kasa tantance ciki a jikin Amina..

Cikin wani irin mafi girman tashin hankali da sake jiquwa a zufan gaske duk ac Daya gama cika palon Lameenu yace

"Kenan nakudar haihuwa takeyi a Daren Kokuma wani abin na damunta sbd a dakinta me aikinta Daya take tareda ita hakama Shima Omar ya fito a cikin Daren har harabar gida...... innalillahi wainna ilaihirrajiun.

Wani kallan baqin ciki da tashin hankali Mai tsananin gaske Mam yayiwa Lameenun Yana Jin inama dashi su BB suka hada suka kashe cikin duhun ya huta da baqin cikin dayake ji yanzu akan wannan shirmen da baqar ranar Daya nuna musu Dan samun haihuwan Omar itace babbar baqar kaddarar data sake Hawa kansu tinda Babu yanda zaayi ko sun kashe Omar dukiya ta zama tasu yanzu yanada me gadons gaba Daya,

Kashe Omar batareda sun tabbatarda sun gane inda abinda aka haifar masa yake ba kaman aikin banza ne Dan haka dole saisun fara kawar da magaji ko magajiyarsa sun tabbatarda babu me gadonsa bayansu kafin su kawar dashi,

Gaba Daya yanzu lameenu ya jiqa masu aiki ya dawo musu dashi Baya,
Ta Ina zasu fara da sanin inda ma zasu Gano mutanen biyu Dan idan ma akwai haihuwan ko Babu a bakinsu zasu tabbatarda komai a zahiransa.

Lameenu ma Jin yayi zuciyarsa da gangar jikinsa na rawa sosai akan ta inda zasu fara Neman wannan haihuwar da itace tayi musu shamaki yanzu da cikar buri bama Omar din ba Dan kuwa shi fitowarsa kadaice ta shiga tsakaninsa da mutuwarsa Dan kawar dashi ya zama dolen dole tinda yasan komai dabai kamata ya sani ba akansu.

BB kansa ma cikin baqin ciki da zafin zuciyar samun wannan babbar matsalar a aikinsu yakeji duk da yanzu ko zasu rayukan mutane dari saisun Nemo inda mutum biyun Nan suke Dan wannan Karan Mam seelah ne da kansa sai cike aikin batareda barin matsala ya kawar da matsalarsu.

Dayake Lameenu yasan shine ya Bude kofar wannan sabuwar masifar data samesu Kuma yasan Mam Bai taba samun matsala a abu ba idan ya tashi aiwatarwa a natse yake cikakkiyar aikinsa ba damuwa Dan haka duk yashiga damuwa kan tashin hankali Amma dai koma yayane yasan bazasu taba samun baccin nutsuwa daga Nan har shekaru masu zuwa matiqar Mam Bada hannunsa ya kawo karshen jinin Omar ya batar dashi a duniya ba.

Babban arzikin Omar yaci shine Basu taba sanin qanwar mijin Ayshatu kanwar kasim yake aure ba,
Hakama Basu taba sanin waye ma mijin Ayshatu din ba bare inda yake Dan haka suka bazama sakin mahaukaciyar dukiya Baji ba Gani Mai aikin gidan Omar jeden suke nema da baqonsa,
Amma dai me aikin sukafi Maida hankali nema itada aka sani sbd shi baqon haryanxu basuda tabbacin wayeneshi?
Daga Ina yake?
Meye alaqarsa da Omar din?
Yaya kamanninsa suke?
Dan haka Maryama suke nema ido rufe Baji ba Gani,
Ta bangare Daya kuwa su aje matsalar Omar a gefe saisun gama data abinda ya Haifa din Wanda suke da tabbacin Yana sane ya boyesa koma inane sbd kada su sani.

**********Ahankali ahankali Suma cikin tsananin rashin Kwanciyar hankalin zuciya da tsananin son cikar buri lokaci da shekaru suka ja musu batareda sun samu sanin inda Maryama take ba Amma dai Basu taba cire Rai kona daqiqa bane daga tsananta bincikensu Wanda duk tsawon shekarun da aka dauka wannan burin koyaushe karfi da zaquwa yake qarawa ransu sbd kullum dukiyar Omar tamkar hakin da ake bawa ruwa takeyi sai yaduwa take sake yi tsananin Sonta da maitarta na karuwa ransu tana yaduwa a jini da gangar jikinsu tareda tsiruwa a zuciyarsu duk kuwa da daukaka da tarin arzikin da Suma suketa qaruwa a rayuwarsu.

*****************
Shekaru sun tafi a yanzu Sunan SEELAHs Babu inda Bai shiga ba Dan kuwa sunyi wata irin kafuwar da Babu Wanda zai iya girgizasu idan ba ubangijin Daya Basu ba,

Sunyi suna me karfin gaske,
Sunada power fiyeda yanda ake tinani,
Sune masu fada aji,
Masu taka Wanda suka so,
Masu yin yanda suke so,
Nera da dollar sun zaunu a SEELAHs kaman basusan meye matsala ba a rayuwarsu,

Tin shekarun da suka gabata suka tashi daga inda suke suka sauya anguwar datafi kowace anguwa tsaro da tarin asalin masu nerar data amsa sunanta nera,

Kaman yanda gidajensu suke a jere acan Baya hakama yanzu mansions dinsu a jere suke guda uku sbd duniya su uku ta sani haka zasu cigaba da zama su ukun har sai Omar yabar duniya Dan haka Koda suka tashi barar da dukiya aka Gina mansions din da Omar sukayi duk da har lokacin Bai taba dawowa Nigeria ba duk da ya bayyana Amma inda yake rayuwa yanzu komai dukiyar dasuke ji Dan ita Basu Isa su tinkaresa da matsala ba a gurin sbd shi kansa ya goge sosai yanzu baida wani sanyi ko kawaici kaman Omar din Baya sosai yake tafiyarsa business dinsa da rayuwarsa batareda ya waiwayo Nigeria hakama Yana sane yaqi waiwayo yarsa yafison yagama ganin gudun ruwan Yan uwansa Dan Yana bayyanarda ita zata zama cikin hadari duk tsaron dayakeda shi bazai iya wasa da rayuwarta ba ya daukota ba Dan yasan ko Babbah zai rasa ransa Yana can Yana kulawa da ita cikin Kwanciyar hankali da tsaro musamman dasuka samu tabbacin su kawun sun bace Babu me labarin inda suke duk bincike kuwa su kansu Basu Gano inda suke ba Dan haka ma ya kyalesu sai koma ya lafa zai nemeso duk inda suke.

***********
DR JAMAAL SEELAH Wanda aka Fi sani da DR JEEY SEELAH matashin likitan daya qware sosai a aikinsa,
Likita ne da ba iyayensa kadai ba dukkanin mutane suke tsananin alfahari dashi sbd qwarewansa akan aikinsa duk da ta bangare Daya mutum ne Mai tsananin zafin Kai da Baya daukan reni barema kallan kadai idan kayi kaine kake Rena kanka sbd asalin abinda ake kira da kwarjini da Asalin class me sakaka kama kanka kawai daga ganinsa.

Duk duniyarsa mutum uku ne kadai suke ganin Asalin dariya ko kyakkyawar murmushinsa Dake kashe me kallansa,
Chapter 18 · 0% Book details