← Book details Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 59

Sashe 44

Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tinda yake a rayuwansa wannan shine aiki mafi wahalan dayakesha mara sauko ko kadan a duk shekarun Nan,
Shi kansa sbd baqar wahalan dasuke Sha a wannan aikin yakejin bazai taba samun nutsuwa ko Kwanciyar hankali ba matiqar ba Gano abinda suke Neman sukaiba kaman yanda yasan har abada uwayen gidan nasa bazasu taba samun baccin nutsuwa da Kwanciyar hankali ba idan ba burinsu na shekarun cika yayi ba.

Cikin girmamawa yace

"Sir Haroon barka da dawowa"

Batareda Jamaal ya amsa ba Dad Lameenu ya Kalli siddeeq Wanda Shima Kai tsaye ya juya daga office din ya fice tareda Turo musu kofar.

iPad din hannunsa ya ajiye gabansu tareda bayanan daya samo akan bincikensu ya fara da cewa

"Ranka ya Dade na samu tabbacin 'yayan matar sir Omar Daya gudu da abinda ta haifa a daren yanada nasa 'yayan guda biyu Kuma dukkaninsu Maza ne sedai Kuma matarsa an bani tabbacin kafin barinsu gombe a wancan lokacin ta haihu Wanda nakeda tabbacin ba haihuwa tayi ba babyn sir Omar dinne"

Cikin zaquwa Dad Lameenu yace

"Bayanin inda suke shine babban abinda muke buqatan Jin idan an samo"

Hakama Menene asalin abinda aka haifa din?
Mace ne ko namiji??
Hakurina da bugawan zuciya akan wannan lamarin ya kusa kamani BB a gaggauta samo mana inda suke sbd tashin aikinmu yau da aka samu shi kadai bazai riqe mana matsayinmu da tsagwaran dukiyar da muka rasa ba muna tsananin buqatan dukiyarmu Dake hannun Omar.

Dad da Shima abinda yake ransa kenan ya Kalli Haroon dayake tsaye har lokacin gabansu Yana kallan fuskokinsu da bakinsu yace

"Haroon ya qara muku kudin Daya kamata banason aurensa yazo duk tsanani duk wuya batareda an samo mana inda suke ba,
Idan Kuma bamu samo Hakan ba to tabbas lokacin zuwansa garemu yayi Dan bazai taba yiyuwaba ayi auren 'dana dayake matsayin dansa batareda yazo ba,

Zuwansa Nigeria kuwa ba abune da zai taba yiyuwaba yazo ya tafi batareda ya kaiwa abinda ya Haifa da cikinsa ziyara ba Wanda shi da kansa zai kaimu ga Magajinsa batareda ya saniba.

Kallan Haroon ya sake yi Yana sake cewa

"Ka Basu duk adadin kudaden da suke buqata kaje ka fara Shirin aurenka Dan daga lokacinda Omar ya sauka a Nigeria dukkanin motsinsa a tafin hannunmu zai zama."

Gyara Kai Jamaal yayi Yana kallan BB dayakejin bazai iya barinsa ya sake ahakan iskan yanci ko Daya ba Amma Kuma Yana buqatan sanin abinda yake faruwa kafin komai Dan kuwa zantukansu sun Saka kansa daukan zafi.

Gyada Kai BB yayi Yana Jin nutsuwa da farin cikin Suma wahalallen burinsu ze Kai karshe sbd a saukake ma auren Haroon din zai kawo Omar har gida Kuma zuwansa kaman bayyanar abinda yake boye ne.

Maganganun sauran ayyukansu dasu BB din keyi ne suka fara Kai tsaye tareda tambayan huldan datake hannun BB din da yaransa ya tabbatar musu da komai Yana tafiya lafiya kalau duk da an kama wasu yaransa Amma ya tura yaronsa Daya Daya bari aka kamasa aka Saka cikinsu Sbd ya hanasu fadan komai sedai aka wayi gari sun rasu dukansu su biyu sai shi Dayan yaron nasa sun fito dashi Dan haka Babu matsala Tako ina.

Juyawa Jamaal yayi ya fito idanuwansa basa ganin gabansa sosai sbd Ja da tashin hankalin Daya tsinci kunnuwansa daji batareda ya tsaya jin sauran abubuwan da hankalinsa yake Neman kasa dauka duk da ya Dade da sanin ba imani a lamarinsu Dad bare tausayi sbd abinda sukaiwa fadila da har yanzu baida sheda ko tabbacin sune sukai Amma ayau da kunnuwansa Yana Jin abubuwan da baisan tayaya ma zaace sune suke aikatawanba,

Haroon ya San dukkanin wannan abin dayake faruwa kenan ya boye masa tinda gashi suna maganar a gabansa batareda sanin ba Haroon dinne ba.

Yana fitowa Kai tsaye mota ya nufa Yana miqawa siddeeq hannu ya basa key batareda ya Juyaba,
Kirjinsa yake Jin ya toshe masa Babu iska ko kadan Babu abinda yake buqatan so kaman ya fita daga Mansion din.

Siddeeq na ganin Hakan ya miqa masa key din motar Haroon Daya fito dashi Dan fitarsu idan sun gama.

Saida siddeeq ya nuna masa motar ya nufi inda take tin kafin ya Isa ya Budeta Yana Isa shiga kawai yayi ya tayar da reverse ya fice daga Mansion din Yana saukar da duka glasses din motar sbd iska ta shigesa.

Yana ficewa siddeeq ya Ciro wayarsa Yana shakkar abinda ya faru daga cikin office din Amma dai koma Menene Haroon Yana buqatan sani Dan dawowa sbd ansamu matsala ga dukkanin alama.

Su Dad kuwa farin ciki da zaquwan auren ne gaban Daya ya mamayesu sbd ga dukkanin alama sanadiyar auren zasu samu abubuwa da dama dasuke so suke fata,
Haroon ya fara zama abin Alfaharin da zai sake fitar da sunan seelahs da tsayuwarsu hakama dawowan Omar dasuke fata ta sanadin auren da dole zaizo ko Dan Yan jarida dazasu yada maganar auren koina da rashin zuwansa auren 'dan farko da zaayi a Seelahs din tinda na Jamaal kaman auren boye ne da ba kowa ya saniba Amma wannan da kansu zasu Kai masa gayyata ta musamman da matsayin zamansa wakilin ango da zai karba auren da hannunsa.

******Haroon dayake tareda mahaifiyarsa tana jinyarsa cikin tsananin so da kauna da kulawa tareda tattali Jin yayi zuciyarsa ta karaya Da yanda tin farko ya zabi mahaifinsa akan mahaifiyarsa,

Bata taba nuna masa banbanci tsakaninsa da Jamaal ba sedai shine Karan kansa ya zabi mahaifinsa akanta sbd sonsa dayakeji cikin ransa fiyeda komai.
#MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
44
Mum Aleena datake Jin batason sake rabuwa da 'danta sbd halinda yake ciki na tsananin buqatan kulawansu dan sai sunyi da gaske zasu iya rabasa da depression din Daya kamasa,

Drug kuwa da suka samu a jininsa Basu sanar masa ba itada Jamaal sbd sunason tantance shine yake Sha da kansa kokuwa sbd sun kasa yadda ko sanin tayaya zai zama Yana Shan kwayoyi irin wainnan.

Siddeeq Kuma ya tabbatar musu da Babu kwayoyi mayen ko makamancin Hakan da Haroon yake Sha Amma Kuma duba da depression dayake ciki da tsananin matsi a Hannunsu Dad zai iya samun kansa da Shan kwayoyin Dan samun fita hayyaci ya Dena Jin komai.

Tin daga ranar da Haroon din ya taho aranar ya ringa yiwa mum din kuka kaman karamin yaro cikin ciwo da tsananin buqatan again Dan uwansa akan bayason rasa Ameenatou kaman yanda ya rasa fadila,
Shi a yanzu ba yabon mahaifinsa yake nema ba Ameenatou kawai yakeso a rayuwarsa.

A gaban Mahaifiyarsu Jamaal ya Sakasa sukaiwa juna alkawari.

Idan Haroon yayi masa alkawarin dawowa ga mahaifiyarsa Dan samun lafiyansa da rayuwar nutsuwa da Kwanciyar tare Kuma da cika burin Mum dinsu na ganin yayanta duka biyu a tareda ita to shi Kuma yayi alkawarin zuwa ya gyaro dukkanin abinda Haroon yakeso Dan samun yabo daga Dad dinsa da Kuma zama abin alfaharinsa tareda tabbatar da aurensa da yarinyar Amma ana daura auren zasu taho tare.

A daidai wanna gaban Babu abinda Haroon bazai iya yiba akan samun Ameenatou da samun nutsuwan zuciyansa data Dan uwansa da mum Dan haka ya amince da dawowa cikinsu gaba Daya bayan auren take mum ta rungumesa cikin farin ciki da Jin dadi sosai tana Jin kaman tinda ta haifesa sai yanzu ne zata samu zaman datakeson yi da 'danta hakama zata kaman yanda ta kaunaci fadila take taji tana kaunan Ameenatou har cikin ranta duk da Bata taba ganinta ba Amma tayi masa alkawarin inshallah da ita zaayi aurensa.

Daman ba wani zama zasuyi a Poland dinba Nigeria zasu taho sbd bikin auren Da Haroon din kwata kwata yaji Baya son a dauko lokaci ayi kawai ya tahowansa kusada mahaifiyansa Dan haka sauki kawai sukeson ya Dan samu su taho saiga Kiran siddeeq Wanda ya sakashi shiga fargaba da tsoron abinda Jamaal yaji Dan haka shine ya dagawa mum hankalin komawansa baima jirata ba washe garin ranar ya Siya ticket dinsa ya tahowansa Dan bayason abinda zai janyo fushin Jamaal ya lalata masa komai adaidai lokacinda ake gap da samun abinda yakeso.

Jamaal kuwa a ranar Bai kwana a Lagos ba ya wuce Abuja tareda siddeeq ko su Dad din Basu saniba Dan idan Yana ganinsu zuciyarsa kasa riqe koshi waye din takeyi gwara ya tafi ya Jira zuwan Haroon Daya San duk inda yake idan har baida gaskia Yana hanyar dawowa.

Kwana Daya saiga Haroon din ya diro Amma Bai yadda ya Hadu da Jamaal din ba Kai tsaye Nasarawa ya wuce sbd bayason suyi hayaniya Kuma baisan Menene yaji bama tukuna bare yasan ta inda zai fara.

Da yamma sosai ya iso Dan haka wanka da sallah kawai yayi Bai tsaye komaiba ya wuce gidan Babbah.

Zaune suke a tsakar gidan sai lallabata dadah keyi sbd taqi Shan magani daga ciwon Kai zazzabi ya maqale kwana biyu anata fama da ita.

Zuwansa ya Saka Abdul sakin ajiyan zuciya hakama Hafiz Babbah Baya Nan
cikin sakewan fuska da nutsuwa ya qaraso Hafiz na janyo masa kujeran zama Yana masa barka da zuwa.

Yaya Abdul ya fara bawa hannu suka gaisa cikin tsananin kulawa Yana tambayarsa kwana biyu ko numbernta Baya shiga.

Murmushi ya sake Yana cewa aikin dayake gabansa ne ya sakashi kashe dukkanin wayoyinsa sbd aikin ya koma babba fiyeda yanda suke tsammani.

Gurin dadah ya Maida kallansa Yana gaidata cikeda girmamawa da kulawa kafin idanuwansa suka koma kan Ameenatoun Dake zaune sanye da Riga da wando na bacci ko hula Babu a kanta ko inda yake Bata juyo ta kalla ba maganinta take kokarin Sha tana kasawa sbd batason magani ko kadan.

Hafiz Dayafi kowa shiga damuwan bayan Ameenatou tambayarsa siddeeq yayi suna sake shiga wata firar Amma gaba Daya hankalinsa na kan Ameenatou da yayi magana tayi masa shiru kaman Bata ji ba Kuma kowa yasan ta jisa Daman sun San sai anyi Hakan.

Dadah ce ta Dan rarrasheta tana cewa
Chapter 44 · 0% Book details