← Book details Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 59

Sashe 29

Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh bazan sake ba,komai bazan Saka tabawa naka ba saina tambayeka,Amma Dan Allah Yaya Hafiz da gaske baturen Nan zai sake zuwa site din aikinku?

Tsoki Hafiz din yayi Yana fincike hannunsa daga nata Yana wucewa cikin haushin ma Bata lokacinda da yayi Dan ya dauka tuban gaske tayi Ashe sbd me gidansu da shi Yama kasa iya riqe sunansa take magana Wanda Rabon da su gansa anjima sosai Dan tini aikin site din ya tsaya cak Anma Dena project din kwata kwata dukansu an sallamesu Se yanzu ne zaa sake tayarda aikin an mayar dasu aikin masu rabo kuwa har Lagos zaa tafi dasu.

Gefen dakinsu ya nufa ya shanya takarmansa kafin ya shige dakinsu Yana kokarin qarasa shirinsa ya fita abinda yake gabansa.

Ita kuwa juyar da idanuwanta tayi tana juyawa ta koma dakin dadah tana cewa

"Babbah nidai kace Yaya Hafiz koba yau ba idan baka Nan karya Dakar Maka ni,
Nida nakeson auren bature tayaya zai aureni idan akaimun Tambo."

Batareda babban ya kalletaba Yana fitowa daga dakin yace

"Bama ze fara dukanki ba bare tambon ai yasani sarai,
Yadai samu sa'ar dokarmun ke a Baya yanzu kuwa Babu yanda zaayi Ina kallan tsaleliyar budurwa a gabana Ina jiran ganin aurenta ya dakarmun ita, ko kudi aka basa bazai dakeki ba indai Ina Nan."

Dadi zancen yayi mata ta juyo tana kallan Dadah data karasa Saka mata zip tana cewa

"Dadah ko Babbah Baya Nan Dan Allah ki ringa tinawa Yaya Hafiz zancen Nan Koda nayi masa lefi"

Miqewa dadah tayi tana nufar gaban tsohuwar madubinta ta dauko turaren Ameenatun dasu Hafiz ke Siya mata Baya taba yankewa tareda duk wani abu da sabuwar budurwa ke buqata kwata kwata basa wasa da lalurarta ko buqatunta sbd tini suka manta da ba uwarsu Daya ubansu Daya da itaba Dan kaunar da suke mata kusan duk Neman da sukeyi Dan inganta rayuwarta ne duk da ta renasu sosai har gwara Yaya Abdul tana girmamasa sosai akan Hafiz data Rena sbd biye mata dayake yi kusan Babu ranar da basa fada tin kafin suyi wanna girman,
Da suka girma kuwa tini suka koma yanzu shiri anjima fada yace Saiya karyata ko balla mata kafafu.

Fesa mata turaren me sanyin kamshi daidai dadah tayi tana dauko mata hijab gogagge kalan kayanta ta miqa mata tana cewa

"Ki Dena shiga sabgarsa tinda Kinga dai bakyason tabo ko Daya a jikinki,
Idan Baki Dena ba ko a hanyar rakaki makaranta Saiya miki dukan ba sanin kowa bare me cetan ki."

Bata fuska tayi tana qarasa Saka hijabin tace

"Ai Babbah yace ko a waje karya taba masa ni"

Takarmanta dadah ta fitar mata kofar daki tana cewa

"Zo ki tafi kinyi latti sosai"

Jin haka ya Sakata fasa Saka takarman tana dawowa Baya ta dauko wayar Dadah din ta danna Taga karfe Hudu saura mintina kadan ita da ake fara tarewan latti karfe biyu da rabi.

Dadah na ganin ta ajiye wayar tana narke fuska tafara daga murya tana Kiran Hafiz.

"Hafiz fito ka Kaita makarantar ka roqi malam Dan Allah ayi mata hakuri bazata sake latti ba uzuri ne yasakata lattin."

Hafiz Dake daki Yana Saka kayansa Yana jinsu yayi musu shiru Dan babu hakurin da zaije bawa malam Dan kullum haka takeyi duk ya lalace ya qare a hanyar makarantarta bawa malamai hakuri da uzurin karya Baya hanyar bokonta Baya hanyar islamiya kaman mara aikin yi.

Sake qwala kiransa Dadah tayi yanaji yayi kaman Baya gidan Dan yakai malaman suna ganinsa suke sauya fuska.

Babbah Daya fito bandaki sarai ya hango Hafiz din a daki yace

"Yana jinki Kaita ne bazaiyiba idanma kin takurasa haka zaibi hanya Yana mangaremun yar budurwa Dan haka muje na Kaita da kaina ai mun Saba ba akanta farau latti ba hakama ai uzuri ne,wuce maza muje.

Saka takarmanta tayi ta fito dadah na miqo mata jakarta tana cewa "A dawo lafiya yar budurwan Babbah"

Hafiz Dake kallansu ta window da harara yabi Bayan Ameenatoun Yana cewa

"Duk anbi an sangarta yarinya Bata ganin girman mutane Dan an renasa ace kullum Saiya Rakata makaranta saikace qaramar yarinya,
Duk an ishemu da wata yar budurwan Babbah da Dadah mtseww"

Dadah Dake jinsa cewa tayi

"Idan ka gama yi mana fada ubanmu saika fito ka wuce inda zaka tafi ka dawo da wuri ka biya mata ku dawo tare."

Yana Jin Hakan ya fito baice komaiba ya fice Yana gyara zaman rigar shaddarsa a jikinsa dan qamshin turarensa me arha na tashi Dan gurin fira zasu gurin budurwansa.

Yana fita Dadah ta bisa da kallan mamaki tana girgiza Kai Dan tasa wannan Doron dayake dagawa Yana qamewa fira zasu.

Yana fita Abdul ya shigo gidan sanye da kayansa na aikin securityn Bankin first bank kadai dayake ta gurarensu.

Gaida Dadah yayi Yana cewa

"Budurwan gidan ta fita ne naji gidan tsit."

"Taje makaranta Babbah ya tafi Rakata jiya da shekaran jiya bataje ba tana fama da yatsarta datai tintibe Se yau ya Sena mata ciwo ta shirya ta tafi"

Yana Jin Hakan yashigewansa Yana cewa

"Wannan budurwan daya bita da Kun cire mata shi Dan Babu Wanda zaiso ta ahaka Kun gama lalata kayarku"

Banza tayi masa ya shige ya tube ya fito sanyeda da wando dogo ba Riga da kwandon kayan wankansa ya wuce Bandaki bayan ya debi ruwa a bokita Dan Shima wankan zeyi ya fice fira zashi Shima yau din Dan ya kwana biyu Bai ziyarci budurwansa ba.

A hanyar makaranta Saida Babbah ya Siya mata agwaluma cikin bakar leda ta Karba ta Saka jaka suka Isa tana Dan narkewa babban shikuma Yana ganin Hakan ya Bada himmar yiwa malam bayanin rauni taji jinya sukai sosai.

Malam iliya ya Saba da wannan karfin halin na Babbah Dan haka baiyi musu ba yace Allah ya tsare gaba ta wuce aji kawai.

Wucewa tayi Babbah na mata adduar adawo lfy da adduar Allah ya Bata ilimi fiyeda kowa makarantar.

"Amin" tace masa tana wucewa gaba kadan kadan tasake cewa

"Babbah kasa Yaya Hafiz yazo daukan fa"

"Tin kafin a tashi zan korosa"

Dariyar mugunta tayi tana wucewa aji da sauri.

Tana shigowa ajin kawarta ta musamman ta tarbota cikin murna daga Nan sukai gurin zamansu.

Dayake sune manyan makarantar da zasuyi sauka a kwanakin kusa a tacesu shiyasa su kadai ne ajinsu daban Amma sauran makarantar kusan aji Daya suke sedai kowa da karatunsa da ake masa Yana bayarwa ranakun laraba da litinin.

Tin kafin lokacin tashi ya qarasa yi Babbah ya ringa Kiran Hafiz a wayarsa me malatsai Yana cewa yaje ya taho da Ameenatou din.

Hafiz idan akwai abinda yafi zafi da takaici Yana cikinsa Dan kuwa a gaban budurwansa yake babbah keta masa wannan Kiran Dan haka dole yayi sallama da ita ya nufi hanyar makarantar Yana tafe Yana masifa da bacin Rai.

Yana Isa ana tashinsu suka kamo hanyar gida Yana Jin kaman ya mata shegen duka a hanya Amma Yana Hana kansa sbd balain Babbah dazai tarar a gida.

Ita kanta dayake tasan a siqe yake da ita Dan haka ta matso kusa dashi tana fada masa Dan Allah idan zaije fira gobe suje tare Taga matarsa su Saba mana.

Duk yanda zata Saka fushinsa sauka ta sani Dan itace ke kunnasa Kuma ta saukesa Dan haka kafin su Isa gida tini suka shirya fira sukeyi sosai hadda dariya.

Dayake magrib ta matso sosai suna Isa gida Baima shiga ba ya juya ya masallaci dagacan Kuma akwai inda zashi.
FOR MORE PAGES FOLLOW ME AT MAMUHGEE @AREWABOOKS
#MAMUH#
#AMEENATOU
#HOTLOVESTORY
#HOTROMANCE
#ZAFIN KAI
#TWINS

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
29
Da daddare Bata wani ci abinci ba furan babbah kadai tasha kadan tace batacin abinci ta koshi,

Rakata wanka dadah tayi sbd Bata iya zuwa bandaki ita kadai da daddare sai anrakata Dan haka tana Gamo wanka doguwar Riga kadai ta Saka ta Kwanta bacci Dan Allah yayi mata baccin wuri Dan haka yawanci Se dare Hafiz ke samun cikakkiyar yanci a cikim gidan daga wahalan Ameenatou da takaicinta.

Dakinta shine a tsakiyar nasu Babbah Dana su Yaya Hafiz din sbd duka duka gidan dakuna uku rak sai bandaki da tsakar gida da kitchen dinsu karami.

AMEENATOU BABBAH wadda kusan kowa ya sani da budurwan Babbah kaf wainda ke garin shedu ne Kuma zasu Bada sheda a koina cewan Babu yar gata Kuma sangartacciyar da gata yayi mata yawa a garin kamarta,

Babbah fadan tsananin son dayakewa yar budurwan tasa bama Mai yiyuwa bane,hakama dadah akanta kowa ya sheda yakuma tabbatarda son da ake cewa ana yiwa auta na musamman ne Dan kuwa kauna da banbancin datake nunawa akan Ameenatou daban yake a ranta akan sauran yayan nata.

Su Hafiz kuwa dasuke yannanta sunfi kowa Bata kariya da tattalin tarbiyanta da kiyaye huldodinta da kowa,
Bata zuwa gidan kowa,Bata yawo baa aikenta komai yimata sukeyi,
Tin tana yarinya sune suke Rakata makaranta su daukota haryanxu data zama budurwan datake nanatawa Rakata akeyi makaranta kuma a koma a rakota gida ko Daya daga cikinsu Kokuma Babbah da kansa Wanda duk manyancinsa babu ruwansa zuwa yakeyi takakka idan aka Daketa a makaranta shiyasa kowama ya gaji ya shafa mata lafiya basa dukanta sbd sharia ce da zance Baya karewa har gaban manyan gari Kona makaranta
Babbah Sam Sam Baya yadda da laifin Ameenatou Koda sama da kasa zata hade kuwa Baya yadda da tayi lefi Kuma wani lokacin Yana sane da batada gaskiyar Amma Baya yadda sedai idan sun dawo gida yayi mata fadan kafin ya lallasheta daga baya.

Duk da su bamasu hali bane Suna rufin asiri sbd su Hafiz na aikin karfi hakama babban duk da manyanci sosai Yana Dan babbuga sanaar dabbobin Daya Saba Babu wani samu sosai Amma sbd inganta rayuwan Ameenatou Babu Wanda yayi qasa a gwiwan Nema.
Chapter 29 · 0% Book details