← Book details Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 59

Sashe 27

Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sauran likitocin ma gaba Daya jikinsu sanyi yayi musulman ciki suna ambatar

"innalillahi wainna ilaihirrajiun da allahu Akbar"

Kafiran ciki kuwa tausayinta Dana Dr Jamaal ne yake rufesu sbd tasha wuya sosai itama a iyama lokacinda ta fara zuwa asibitin kadai bare rayuwarta ta Baya.

Ficewa likitocin suka fara ganin Dr Jamaal din a tsaye bayan sun rufeta har fuska sun gama rubuta komai a file dinta anyi signing anrufe an ajiye a gefe shikenan ita ta huta da gwagwarmayar duniya.

Mum dinsa ce kadai ta rage ta tako ahankali batareda ta iya cewa komaiba sai hawayen Daya ciko idanuwanta Yana gangarowa ta rungumesa ahankali cikin mutuwar jiki tana basa hakuri hawayenta na Kara gudu.

Fashewan kukan umma me sautin daya sake karya zuciyar kowa ne ya sauka cikin kunnuwansa take ya rintse idanuwansa dasukai wani mummunan ja yanajin dukkanin zuciyarsa na kakkaryewa tana watsewa.

Siddeeq ne ya rungume umma Yana tarota jikinsa sbd kukan datakeyi hadda na mijinta data rasa a ranar kukan Bai fitoba sai yanzu data rasa yarta taji abinda ya dunkule a zuciyarta ya fashe mata.

Wani irin kuka me cin Rai da qunci me tsanani takeyi sautinsa na karya dukkanin zuciyoyin sauran likitoci da Jamaar Dake gurin Amma Babu me iya cewa komai sbd tana buqatan yin kukan.

A ciki ma mum ce keyiwa Jamaal din kukan dashi zuciyarsa Bazata iyaba sbd Jin ma yakeyi baida sauran emotions kwata kwata bayajin komai face dutse a zuciyarsa.

Labarin na Isa gurinsu Dad da Haroon gabaki dayansu asibitin suka dungumo cikin tashin hankali musamman Haroon Dan kuwa JAMAAL ne a ransa,
Jin yakeyi rasuwar fadilan Shima tana gigita kansa da nutsuwansa dan haka a rikice ko Gani sosai bayayi suka iso asibitin.
##MAMUH

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
26
Shi kansa Dad da Dad Lameenu cikin damuwan halinda Jamaal yake ciki suke,
Mum Atee da Ayesha ma tini suka iso motansu mummy Sarat na bayan tasu Dan haka take asibitin ya cika da familyn seelahs cikin damuwa da tashin hankalin yau wace irin Rana ce?
Mahaifinta ya rasu yau,
An daura mata aure yau itama ta rasu a yau din.

Haroon na isowa kallo Daya yayiwa Dan uwansa yaji idanuwansa sun ciko da Hawaye masu tsananin zafin gaske suna gangarowa ya rungume Jamaal din.

Dad ma na isowa rungumesa yayi Yana kallan mum Dake hawaye sosai sbd tausayin fadilan da wuyar datasha tareda tausayin danta Dan shine yake cikin azabar zuciya yanzu me tsanani ta sani.

Dakin gawar suka bari suka koma office dinsa gaba dayansu familyn kowa fuskansa Babu dadi Dan tausaya masa bisa ba rashin dayayi Dan kuwa Babu Wanda Bai tabbatarda irin so da matsayin da fadila take dashi a rayuwarsaba.

Umma siddeeq ne kadai a tareda ita sai mum data koma gurinsu daga baya Dan ummanma itace abar tausayi fiyeda kowa Dan itace tayi rashinda sai me karfin Imani ne zaiyisa Rana Daya Bai zauce ba.

Ganin Halinda umman ke kokarin shiga ya Saka mum Bada umarnin a kwantar da ita cikin gaggawa Dan taimaka mata.
Bayan an kwantar da umman harma anyi mata allurai da wasu abubuwan an samu tayi bacci ta baro gurinta ta dawo gurin Jamaal Daya kebe kansa a dakin dayake cikin lafiyayyar office dinsa ta fara kokarin yi masa nasiha da basa karfin gwiwan bawa zuciyarsa hakuri.

Gida kowa ya koma sbd Shirin janazah dinta wadda zaayi a Seelahs din bisa ga umarnin Dad tinda ta riga ta zama matar dansa.

Kafin lokacin yayi Yan uwan umman su uku tini suka iso daga garinsu mata biyu namiji Daya.

Su kansu sun tausayawa Jamaal sosai bayan yar uwarsu dasuke cikin tsananin tausawa rashin datai.

Fadan halinda Jamaal ya shiga Baya misaltuwa Dan kuwa ya kebe kansa daga kowa baya buqatan kowa Baya son kusanci da kowa ko kadan.

Abu Daya da suka sani shine Babu Wanda yaga hawayensa bayan Dan uwansa idanma yayi sbd ya nesanta kansa da kowa bayan Haroon Babu Wanda yasake ganin ko fuskansa.

Yanayin jikin umma Daya rikice da Kuma shi kansa Jamaal din Daya rufe kansa ya Saka dole aka daga jana'iza din har zuwa da safe dakuma yayan baban fadilan Dayake hanyar isowa Shima.

Sai dare sosai Jamaal ya baro asibiti tareda Haroon suka iso gida bayan Haroon yaje ya kamawa Yan umman din masauki hakama Dan baba ma Daya iso duka guri Daya aka saukesu tinda gidan ya kone Babu yanda zaa iya kwana cikinsa.

Koda suka iso gida karfe kusan Sha biyu na dare Dan haka Kai tsaye part din Jamaal din suka nufa.

Mum da Dad ne a palon suna magana cikin Dan daga murya sbd bacin ran da mum ke ciki me tsananin gaske tace

"Kasan Hakan shine yayi sanadin rasa ran yarinyar Nan bawai gobaran da aketa yadawa ya kasheta ita da mahaifinta ba?

Tayaya zaace acikin asibitin iya oxygen dinta ne datake amfani dashi ake gurbatawa da Poison,
Shin bakai tinanin halinda 'danka zai shiga ba idan ya rasa macen dayake so fiyeda komaiba?
Tayaya kake tinanin zaka fuskancesa idan yasan sakamakon Poison datake shaqa a oxygen ne ta rasu,
Tayaya kake tinanin zai amsa zancen kaman kasheta ne Akai Kai tsaye Babu kwana kwana?
Bakaji tausayin yarinyar Nan ba tsawon rayuwarta rayuwa takeyi cikin wahalar rashin numfashi sai an Siya mata??

Cikin nutsuwa batareda daga hankali ba Dad din ya kalleta da idanuwansa yace

"Ko zan me kike nufi da wainnan kalaman naki?
Me kike nufi da oxygen nata?
Ke da kike likita kikasan aikinki har kikasan akwai poison a iskan datake shaqa meyasa Baki sanar masa shi 'dan naki ba kika bari har ta rasa ranta....

Katsesa mum tayi hawayen idanuwanta suna qara gudu tace

"Ban taba son sanin 'yayana Susan waye Asalin mahaifinsu ba sbd Hakan zai tarwatsa zuciyansu,Amma wlh tallahi Babu ranar da bana danasanin Kaine uban yayana masu tsafta,
Me kake tinani?
Na fito na fadawa JAMAAL Ina tinanin mahaifinsa yasan Menene yake damun matar da zai aura sbd shine yasan meye ne yake damun oxygen datake shaqa??
Bazan fada masa ba Amma koman Daren dadewa yayanka zasusan waye Asalin mahaifinsu Wanda Baya barin komai ba dalili,
Yanzu data bar duniyar saika ringa kwana da Shirin koyaushe danka zai iya sanin waye ya kashe masa matarsa data mutu a ranar da aka daura masa aure da ita...

Wani numfashin me sanyi da nutsuwa Dad din ya sauke zaiyi magana Haroon dayake gaba ya shigo Yana kallan mum dinsu da kalaman dayake ji abakinta Dan kuwa bazai taba yadda da Dad dinsa zai iya kisa ba duk da Barnar dasuke aikatawa bayan fage Amma mahaifinsa bazai iya kashe Rai ba bare macen da already tana fama a tsakanin Rai da mutuwa.

Jamaal kuwa idanuwansa dasuka qarasa rinewa gabaki Daya ya dago ya zubawa Dad din Wanda ya miqe tsaye Yana kallan jamaal din zufa na joqosa daga kuryan jikinsa.

Mum ma mummunan faduwa gabanta yayi zufa na tsitsifo mata Dan kuwa Bata fatan Jamaal yaji abinda suke fada.

Dad Jamaal din yake kallan Yana kokarin danne abinda yake ransa Yana ambatar sunansa cikin kulawa zeyi magana Jamaal din ya juya ya kallo Mum ya Bude bakinsa da yayi masa wani irin mummunan nauyi Kai tsaye yace

"Results din fadila duka sun tabbatarda oxygen nata ne yayi sanadin komai har rasuwanta right??

Wani mugun zufa da faduwan gaba ne ya Saka mum juyawa ta Kalli Dad Wanda Shima ita yake kalla kafin ya matso zaiyiwa Jamaal din magana Jamaal ya katsesa da sake jefawa mum tambayarsa.

Numfashi ta sauke zuciyarta na nauyi ta matso tareda kamo hannunsa Daya cikin tsananin sanyi da baqin ciki tace

"Eh, oxygen nata shine yaringa poisoning nata ahankali harta rasu Amma muna Saka ran daga karfin da yayi mata ne da oxygen din shiyasa ya zama kaman poison ya mata illa..

Baice komaiba zame hannunsa yayi daga cikin nata ya zari keys din hannun Haroon ya juya ya fice.

Duk yanda Haroon yaso binsa kasawa yayi sbd mamaki da shock din dayake ciki Shima duk da Babu tabbacin Dad dinne itama mum kawai zargi ne sbd Dad baiso aurenba da farko.

Koda ya Isa asibiti Kai tsaye file din fadila ya dauko yafara dubawa ko Gani sosai bayayi kafin ya fito ya nufi lab dinsu a cikin Daren ya buqataci sabon awo tsakanin oxygens din sabo da tsoho Dana fadila.

Haroon baro gida yayi ya biyosa asibiti Amma Sam kwata kwata ya kasa samun ganinsa Dan kuwa a cikin Daren gaba Daya ya daga hankalin asibitin akan sabon awo da komai Wanda ya bawa likitoci da ma'aikatan lab dinsu tsoro da shiga tashin hankali Dan kuwa da farko binciken boye Akai baa son daga zancen.

Koda asuba tayi tsaban tashin hankali har an hada results din Wanda ya tabbatarda mutuwar fadila due to gurbatan oxygen nata ne.
##MAMUH

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
27
Wani mummunan jiri ne ya dibi Jamaal din Wanda sai alokacin ya fashe Da kukan Daya girgiza Haroon da mum dinsa da isowanta kenan asibitin cikin tashin hankali da tsananin tsoro sbd Kwana sukai itama da Dad din cikin tashin hankalin fitina da maganganun da suka Sakata Jin son barin qasar a ranar.

Duk wani sheda ko alaman inda poison din ya samu shiga oxygen dinta Jamaal yayi daga daren zuwa safe Bai gane ba sai Abu Daya wato yawan zuwan BB asibitin Wanda ya samu tabbacin duk karshen wata yake zuwa so Daya dubiyan kaninsa yaronsa da suka karya da gangan suka ajiyesa asibitin yaqi warkewa sbd Daya kusa warkewa saisu sake lalata gyaran.
Chapter 27 · 0% Book details