← Book details Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 59

Sashe 47

Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farin ciki da dokin datake ciki itada Haroon ya wuce duk inda ake tinani sbd karfi da yaji duk yanda Babbah da Dadah suka Kai basa ganin laifi ko illan komai datakeyi Saida suka ringa Jin kunya da mamakin irin son datake wa Haroon Wanda ya Sakasu shiga tsoro da duqufa da adduar Allah yasa irin girman son dayake mata ya tabbata a rayuwar auren nasu yakuma barsu tare har karshen rayuwarsu.

Haroon a wannan lokacin yana cikin kwanakin farin cikin rayuwarsa me tsananin gaske da Bai taba samun kansa a cikinsu ba Wanda Hakan ya sanyaya zuciyar 'dan uwansa da mahaifiyarsa akansa wadda Bata isoba har lokacin Amma ta sheda farin cikin Da Haroon dinta yake ciki Wanda takejin a matsayinta na uwa a garesa tayi missing Daman basa wannan farin cikin dasuke Gani tareda shi sedai tana Jin dadi har ranta daya samesa sanadin macen dayakeson.

Jamaal tausayin dan uwan nasa ne ya Sanyaya zuciyarsa bata cikin farin ciki ko walwala kwata kwata Dan Bai taba ganinsa a irin wanna kyakkyawar yanayinba tsawon rayuwarsu Dan haka yake tayasa farin cikin Samun abinda shi Bai samuba Dan kuwa a nasa labarin Bai taba samun farin soyayya a tareda wadda yaso din ba, duk lokacinda suka dauka a tare lafiyanta koyaushe itace abinda take gaban soyayyarsu Dan haka har suka rabu Basu taba samun kansu a cikin irin wannan farin cikin ba Dan haka baisan Menene yanayinba da yanda ake samun Kai acikinsa.

Koda yaushe a waya suke maqale da juna suna magana tana nuna masa duk abinda akai mata na gyaran Amarya Wanda kullum take sake sauyawa sosai tana fita budurwan datake cikin Hutu da gyara sosai Dan tinda suka taho Lagos din Bata sake fita ko gate ba daga gyara sai Hutu da AC datake Sha da lafiyayyar abinci me gyara jiki take ci.

Har lokacin Bai dawo ba Haroon din Yana Nasarawa n Abuja aikinsu gap yake da kammaluwa Wanda yake Jin kaman Yana Neman rasa kansa kafin gama aikin ya koma Lagos din.

******Su Dad so biyu suna turawa Omar jeden gayyatarsa a matsayin Wanda zai karbanwa Haroon din auren Amma Yana toshe buqatansu ta Hakan sai gashi hankalinsu Yana Neman tashi da Hakan Dan haka Kai tsaye Mam yayi masa maganar Amma still dai ayyukan gabansa bazasu basa Daman zuwan ba ya sake Bada uzurinsa sbd Koda suke maganar ba Baya Nan Yana Japan Dan haka Kai tsaye ya Saka Ahmed ya tura musu zunzurutun kudi a matsayin gudunmawarsa data Saka su Dad din shiga mamaki da baqin gaske me tsanani.

Tsaban kudin suka kalla suna sake shiga qyashin gaske da bakin cikin irin yanda ya debo kudi irin wannan me yawa ya Basu kusan 500m as gudunmawarsa.

Shiru Dad Lameenu yayi lokacinda suke cikin tinanin abinyi gameda baqin cikin da Omar yake Neman sakasu Dan kuwa idan har zaayi auren Nan Bai tahoba tabbas Babu amfanin yin auren babba a garesu Dan duka kudi da dukiya me yawan da aketa zubarwa ana Shirin auren da akeson duniya ta sheda auren SEELAHs duk Dan sbd Omar din yazo ne Amma Kuma komai Yana Neman lalacewa a daidai lokacinda Babu time na Neman mafita ko gyara.

Mam da hankalinsa ya rabu biyu a yanzu akan yanda komai na ayyukansu ke tafiya daidai da Kuma sauyin Haroon Daya fara Sakasa Jin so da kaunan Dan nasa me tsanani na cikeda sedai Kuma Yana shakkar Shima yazo yayi auren mace ta sauya masa shi yazo Kuma baida abinda zaiyi masa barazana dashi Dan tankwarasa Dan haka gaskia gwara ya kama dukiyan dayake son kamawa Koda yayansa sun juya masa Baya yanada abinda bazai taba Jin zafi ba.

Lameenu wani numfashi ya sake Yana dagowa ya Kalli Mam da Shima yake Nisa cikin nasa tinanin ya sauke numfashi Yana ajiye wayar hannunsa daya gama da BB akan a Turo Yan jarida gidan Babbah zasu tafi Kai masa ziyara Yana son a yada abinda ya hadasu din sbd Omar yaga abinda sukeson ya Gani.

Mam da Baisan me Lameenu ke nufi ba yace

"Kayi duk yanda zakayi Omar yazo kasar nikuma wanna Karan nayi alkawarin cike aikin komai da hannuna batareda matsala ko dayaba wannan alkawarina ne."

Murmushin Daya tsaya iya fuska lameenu ya sake Yana Jin dadin Hakan Dan yasan aikin da Mam yasaka hannunsa da kansa aciki kaman cikan alkwarine Da Baya tashi cikar wannan aikin Dan haka ya sake murmusawa Dan shi a nasa bangaren ya gama yadda da indai akwai abinda Babbah ya sani gameda Omar da abinda ya Haifa to tabbas Omar Saiya taho wannan auren idan yaga Babbah a tareda su din.

****Da yamma a gidan Babbah Dad Lameenu yayi Sallah tareda su a masallaci bayan sun Dade suna tattauna maganar daurin auren ya bawa Ameenatou kyautan motan da ita aka taho gidan wadda ta tareda katin gayyatan da aka bugo na musamman me tsadan gaske.

Yan jaridan da BB ya turo sun dauko bayanan da yiwa motar hotuna da Kuma yiwa Babbah da Alh Lameenu din hotunan da suka fito da kyau.

Babbah Bai karbi motan ba ya Saka aka mayar akan bayan auren idan Ameenatou ta dawo hannunsu an Bata acan.

Dayake ba damuwa Daman sukai da lamarin ba Yana dawowa da ita aka ajiye kawai sedai a Daren aka hada labarin dasukeson a hada dauke da hoton Babbah Dana Dad Lameenu suna dariya cikin farin ciki dayake nuna shakuwansu da kusanci sosai.

Washe gari bayan Dad Lameenu din ya gama karantawa kallan fuskanta Babbah yayi wadda ta fito da kyau akan

"mahaifin Sirikitar Seelahs Mal Nuhu babbah ya nuna farin cikinsa da Jin dadinsa ga kyautan motar da sirikansa da kansu suka kawiwa yarsa har gida amatsayin tukuicin auren dansu"

Kai tsaye tareda invitation dinsu na musamman na auren da hoton dayake dauke da wainnan bayanan ya Saka aka yada kafin kace me labarin ya fara yaduwa har inda basa zato.

********
_Greece_

Dattijo ne Dan zaka zama confused akan shekarunsa and Hutu da wayayyar ilimin data gama ratsa rayuwansa Tako wanne Sako ya koma half bature kwatakwata.

Zaune yake a cikin lafiyayyar balcony din gidansa Mai tsananin yalwa da tsari irin na masu kudin gaske dayake Shan iska Yana sanye da farin glass Daya qarawa farar fuskansa kyau sosai da qara fitarda sirrin kyau da Kwanciyar hankalin da Allah ya wadacesa dashi yana karanta mahimman bayanai a Apple iPad datake hannunsa kafarsa Daya na kan Daya hakama gabansa table ne da laptop take Akai a Bude da alama itama wani sakon ya karanta kafin daga gefe qaramin tea cup ne Daya Sha coffee yabari a gurin.

Ahmed ne da Shima ya sauya sosai kaman wani lafiyayyan dattijon bakin bature Shima Hutu da kudi sun ratsashi ya iso gurinsa Kai tsaye da tasa iPad Shima a hannunsa.

Yana isowa kafin yace komai iPad din ya jiye a gaban Omar jeden Kai tsaye Yana cewa

"Ya kamata kaga abinda yake faruwa" ya nuna masa screen din iPad din.

Idanuwa Omar ya juya akan iPad din yana zare farin Glass din idanuwansa idonsa Kai tsaye akan fuskan Babbah da suketa azaban nema ya sauka a tareda Lameenu a gefensa suna dariya cikin farin ciki da shaquwa.

Hannuwansa Dake rawa ahankali yakai ya dauki iPad din a hannunsa Yana kafe hoton da ido kafin idanuwansa suka gangara akan abinda yake rubuce Wanda shine yake Saka Ahmed zufa da motsawan zuciya cikin tashin hankalin da Bai taba tinanin samun kansa ba.

Alh Omar Dayake Neman kasa gane komai saurin miqa hannu yayi Yana Neman ruwan Sha sbd yawunsa da suka qafe take.

****
SEELAHs sun shiga satin farin cikinsu Dan aikin project ya kammala an kaddamar
Fadan farin cikinsu Baya yiyuwa musamman Dad Lameenu dayake ganin sun tsallake rijiya da Baya Dan haka sune cikin farin ciki sosai.

Haroon sosai ya samu lambar yabo da karramawa tareda burge abokan huldodinsu da yawa ciki hadda turawa da yawa da suka yaba da aikin Dan haka take SEELAHs suka ringa samun manyan proposals masu zafin gaske Daya Saka su Jin duniya ta sake dawowa hannunsu Kuma a cikin satin suka samu sabuwar babbar Hulda daga Ashalawa wadda ta sake Saka kan Lameenu gigicewa shi Kuwa Mam a yanzu alfaharin gaske yakeyi da Haroon Wanda yake cikin farin ciki Shima sosai ya ringa Jin kaunar Dan uwansa na sake kere dukkanin abinda yakeso a rayuwarsa.

Dan haka a Lagos aka shirya hadaddiyar lafiyayyar dinner da aka barar da mahaukatan kudin gaske ta kammaluwan aikin.

Kusan duk wani babba dayaci ya tayar da Kai dayake mu'amalantar seelah ko sanatayya ya halarci dinner din wadda aka sakawa matakan tsaro da securities sosai.
Karfe goma Sha biyu da kusan Rabi aka gama dinner din wadda tsarinta yake na asalin Yan boko da masu kudin da muqami sai business tycoons kowa ya watse.

A daidai wannan lokacin da aka gama dinner din seelahs a wannan lokacin ne jirgin Omar jeden ya sauka a Abuja Nigeria.
#MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
47
Sabon drivern da suke tareda shi tin Baya Wanda dashi kadai Ahmed ya yadda yayi contacting Tin kafin zuwansu ayau din aka tanadi lafiyayyar motan da zata daukosu daga airport har Mansion dinsa Dayake jere Dana Yan uwan nasa.
Chapter 47 · 0% Book details