← Book details Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 59

Sashe 43

Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai guraren 11:20 suka baro Kai tsaye daga Nan office din airport suka nufa suna Isa suka ajiye motar anan airport suka shige jirgi sbd sunma iso kusan late.

A cikin jirgin yayi breakfast dinsa hankinsa kwance da nutsuwa sabanin siddeeq Daya kasa samun nutsuwa ko Kwanciyar hankalin sbd abinda zai iya faruwa idan aka samu matsalan Dad suka gane.

Suna sauka Lagos drivern Dad dinne yazo airport daukansu sbd shi Jamaal din da kansa Daya turawa Dad text din azo a daukesa daga airport Nan da awanni.

Da farko kaman Bai gane ba Saida ya sake karantawa ya tabbatarda Haroon dinne yayi masa sakon A tura driver ya daukosa daga airport.

Numfashi ya sauke ahankali Yana jinjina lallai Haroon din yafara samun karfin zuciya tinda ya iya masa sakon Kai tsayen Nan Mai kama Dana Bada order.

Driver na Isa airport Kai tsaye siddeeq ne ya budewa Jamaal kofa ya shige bayan kafin Shima ya zagayo ya shiga gaban motar driver Dake Satan kallan Jamaal din ta mirror cikin girmamawa yace

"Barka da dawowa Sir Haroon"

Gyada masa Kai kawai Jamaal yayi sbd hankalinsa na kan sakwannin asibitin Haroon da aka turo na can Poland Yana karantawa.

Suna isowa mansion din Jamaal ya hadiye wani abu Daya danne maqoshinsa Yana kashe wayarsa gaba idanuwansa na Neman sauyawa Amma ya Hana hakan sbd dawowa ko shigowa mansion din seelahs wani abune dabai taba tinanin zai sake ba har abada idan ba yanzu da Dan uwansa Dake tsananin buqatansa ba.

Sedai abinda Basu saniba shine kaman yanda yayi alkawarin duk ranar Daya Sako kafarsa ya dawo musu Saiya tabbatarda sun rasa komai to tabbas tinda ya Sako kafarsa ayau din ya dawo Saiya gyara musu komai sbd Haroon kafin suna kallo ya rabasu da komai daga ranar Daya tabbatarda Haroon ya mallaki macen dayake so fiyeda komai ayanzu.

Kai tsaye bangaren Haroon ya nufa Yana amsa sannu da zuwan da securities din gidan ke masa cikin tsananin girmamawa da mamaki me girma na sauyin Haroon din.

Yana shiga palon Haroon Kai tsaye bedroom dinsa ya wuce ya shige toilet alwala yayi ya fito yayi Sallah Yana idarwa wayar Dad na shigowa wayar Dake gefensa.

Kallan wayar yayi tareda dagawa cikin nutsuwa yayiwa Dad din gaisuwan Data Saka kirjinsa mummunan bugawa Saida yayi shiru ya sake sauraron muryan da kyau yaji sai yaji Yana Neman rudewa sai kawai yayi Watsi da abinda yaji Kai tsaye ya Bude Baki yace

"Ka sameni yanzu a office din cikin mansion din."

"Ok" kadai Jamaal yace tareda rigan Dad kashe wayan Wanda ya sake Saka Dad din mamakin halayen da Haroon ya fara sauyawa.

Saida yaci abincin da siddeeq yayi masa ordernsa daga tsadaddiyar restaurant ya koshi kafin ya shirya ya fito tareda siddeeq Wanda shine yake nuna masa hanyar da office din yake tinda Bai saniba.

Suna kaiwa kofar office din siddeeq ya tsaya daga waje Jamaal Kuma Kai tsaye ya Bude kofar a natse zai shiga sako ya shigo wayar Haroon Dake hannunsa Kuma Kai tsaye yasan Haroon dinne Dan haka ya dakata tareda duba sakon Daya bayyana akan screen din wayar inda ya rubutu masa tini tareda rokonsa akan yayi masa alkawarin ganin aurensa da Ameenatou ya tabbata kaman yanda tin farko yayi masa wannan alkawarin zai tabbatarda shi din Bai rasa macen da itace farin cikinsa ba kaman yanda shi Bai samu tasa farin cikin ba.
Lumshe fararen idanuwansa yayi da suka fara sauyawa Yana sake Tina alkawarin da yayiwa Haroon din zai tabbatarda su Dad da hannunsu sun aura masa Ameenatou kafin yabar kasar idan har auren Bai tabbataba to Allah ne yayi su din ba ma'auratan bane Kokuma Idan dayansu Baya raye wannan shine abinda mum dinsu ta roka daga Jamaal din sbd bazata so Shima Haroon dinta ya dandani irin radadin da Jamaal ke cikinsa haryanxu ba na Rasa Macen da ita kadai ya bawa zuciyarsa.

Numfashi me sanyi ya sauke ahankali mara sauti kafin Kai tsaye ya shiga batareda knocking ba kaman yanda Haroon yakeyi kafin shigan.

Yana shigowa Dad Lameenu dayake facing kofar ne ya zuba masa idanuwansa Yana kallo cikin Dan mamaki kafin Shima Dad din ya dago Yana kallansa Dan dukkanin idanuwansa mamakinsa a bayyane,

Dad Lameenu Daya rasa abin fada cikin yar rikicewa yace

"Da Jamaal Yana kasar Nan da babu abinda zai hanani tinanin shine a gabanmu,
Haroon hankalinka kuwa kake mayarwa akan aikin gabanka kokuwa gyaran fata ka mayarda hankali Akai sbd mace??

Dad da har lokacin idanuwansa na kan Jamaal din Yana Jin zuciyarsa na kokarin dawo masa da kewan Jamaal da tsananin buqatansa dayakeyi Kuma sai zuciyar ke Jin kaman ta samu Jamaal a gabansa Amma Kuma yasan abune da bazai taba yiyuwaba Dan Koda Jamaal Yana Nigeria ya shigo bazai taba Sako kafarsa SEELAHs ba Dan haka duk yanda idanuwansa ke nuna masa kaman Jamaal ne gabansa bazai yiyuba Dan haka ya dauke idanuwansa daga Jamaal din Yana sauke numfashi ahankali Shima Jamaal din sai alokacin ya ya dago ya zuba musu idanuwansa da suka sauya sosai sedai Bai furta komai ba Dan maganarsa a lokacin zata bayyanarda radadin ganinsu kawai Dake cin zuciyarsa Dan haka ya zabi yin shiru kaman yanda Haroon keyi a gabansu.
#MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
43
A cikin murya me nutsuwa Kai tsaye ya gaidasu Dad din acikin jam'i batareda ya Bada amsar maganarda Dad Lameenu ya jefesa da ita ba ta farko.

Dayake dukkaninsu kowa da abinda yake bakinsa na maganar Dake cinsu Basu tantance sauyin muryanba Wanda Daman Shima Haroon idan jikinsa na Sanyaye muryansa a natse da sanyi take fita Dan haka Babu Wanda ya tsaya amsa gaisuwan bare tambayar ya jikinsa Kai tsaye Dad dayaji Baya iya kallansa Dan yau din cika masa ido Haroon keyi sbd kamanninsa da Jamaal sun tsananta ayau dayake ganinsa kaman Jamaal Dan haka batareda y kallesa ba murya a daure da bacin ran abinda yayi yace

"Ko zaka bani dalilanka Daya Saka bawa project dinmu da ma'aikatan aikinsa Hutu harna kwana uku batareda sanar damu meyake faruwa ba??

Numfashi me sanyi ya sauke Yana dauke idanuwansa daga kallansu kafin ya Tako ahankali dukkaninsu sukai saurin kallansa ganin ya tinkarosu Yana kallansu Dad Lameenu ne yayi saurin cewa

"Amsar abinda yake faruwa muke buqatan Dani sbd Haroon Banga alamar zaka cika alkawarin daka dauka ba na sakamu alfahari dakai,
Aikin Nan fa duka duka sauran sati uku ne a time dinsa ya cika,.

Dad kallansa ya sake yi Yana Jin zuciyarsa na son shiga tinani daban daban Amma ya watsar Yana cewa

"Karka manta nutsuwanka akan aikin Nan shine tabbatan aurenka Dan Neman aure ba shine aurenba Karka manta da Hakan Dan nakai maquran rashin nutsuwan Nan taka,

A Hakan kake Neman mutuwa sbd mace kanason kayi aure batareda kasan ciwon kanka ba bare tinanin tsayuwa ka zama abin alfahari ga iyayenka ba tayaya zaka tsayu ka zama abinda matarka ko yayanka zasuyi alfahi dashi....

Dakatawa Jamaal yayi daga inda yake tsaye tareda dago idanuwansa da sukai ja ya Kalli Dad din dashi ma shi ya Dan kalla Yana cewa

"Yes, Haroon haryanxu ka kasa sakani farin cikin Da kowannen Uba yake shiga akan yayansa da alfahari dasu,
Alkawari nayi Maka akan idan kasakani farin ciki akan wannan aikin zan nema Maka auren da kakeso Amma......

Katsesa Jamaal yayi Dan bazai iya tsayawa sauraron wainnan maganganun akan Dan uwansa ba komai zai iya faruwa Dan zai iya bayyanarda kansa Dan haka wayarsa ya daga ya kira siddeeq take siddeeq ya shigo da takardun komai dasuka gama a yau din ya karba daga hannun siddeeq ya ajiye gaban Dad din Yana kallansa yace

"Gashinan Alkawarin zan cika Maka acikin kwanakin da bazasu kai na cikan kwanakin ba Amma Kuma a ranar da komai ya tabbata a yanda kakesonsa a ranar nakeson a daura mun auren da yarinyar....."

Daga dad har Dad Lameenu sakin Baki suke kokarin yi gurin kallansa da mamaki hankalinsu na rabuwa biyu daga abinda ya fada da Kuma karanta takardun Daya zuba a gabansu suna karantawa cikin tsananin mamakin sabuwar project din data dawo musu Da cikakkiyar damansu a hannunsu.

Dad Lameenu Daya kasa Kai karshen takardan cikin farin cikinsa Daya mantar dashi mamakin dasuka shiga yace

"Nayi Maka alkawarin daura Maka auren Ameenatou a washe garin ranar da Akai bikin Budewa duniya wannan aikin project dinnan Haroon idan abinda nake Gani da suna SEELAHs a jikin takardan Nan ya bayyana.

Dad ma mamakin ne yayi mugun kashesa kafin idanuwansa su sauka kan signature din jamaal Dake karshe wayarsa tayi ringing daga turawansu na Abujan ne Yana dauke idonsa Akai siddeeq ya matso Yana rufe file din tareda amsar masa cikin girmamawa Dan basa Daman amsa wayan wadda ta Saka Dad Lameenu washe dukkanin bakinsa cikin tsananin farin ciki Yana sake tabbatarwa da Haroon zuwa wani sati zai tabbatarda Abdul yayo parking da familynsa sun iso Lagos din gaba Daya.

Wayar da Dad keyi ta sakashi Shima dukkanin farin cikinsa bayyana Yana washe Baki Yana wayar cikin turanci Dan nutsuwa Yana Kuma Basu tabbacin wannan Karan Inshallah komai zai tafi daidai Nan da 3 zuwa 4 weeks komai ya zama cikin Shirin bikin qaddamarwa.

Dad na gama wayar Haroon din ya kalla cikeda farin ciki yace

"For the first time da yau nake alfahari dakai Son"

Kalman zafafa zuciyar JAMAAL tayi Dan haka baice komaiba sai sake fuska da yayi ya amshi zancen Dan kawai da zargi.

Buga kofar Akai kafin aka Bude tareda shigowa
BB ne Wanda duk kwakwalwansa take Neman Juyewa sbd ba dare ba Rana a bincike da yawon garuruwa suke da kauyuka gurin Neman da haryanxu Babu me baccin arziki akansa tsakanin shi dasu Mam din.
Chapter 43 · 0% Book details