← Book details Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 59

Sashe 22

Ameenatou Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sati biyu sukai suka dawo asibitin da ita Rai hannun Allah Kuma sukai babbar sa'ar Dr Jamaal na asibitin Dan haka Shine ma ya amshi matsalarta tareda shiga damuwa sosai sbd ganin Halinda take ciki yafi na Baya muni.

Daqyar suka samu numfashinta ya dawo bayan sunsha wuya sosai Dan haka Kai tsaye ya tattauna da iyayenta sosai ya fahimci tsananin rayiwan da suke ciki da azaban da fadilan Kesha tin tana yarinya har zuwa yanzu datake ganin kaman ta zama musiba ga iyayenta.

Da kansu iyayen suka ringa masa Hawaye suna rokonsa ya fahimtar da ita suna tsananin Sonta ahakan Basu taba gajiyawa da ita ba bare kallanta a matsayin musiba.

Lamarin fadila da iyayenta tsaya masa yayi arai Dan haka Ya karbi file dinta gaba Daya ya mayar da ita patient dinsa da shi kadai ne yake dubata hakama ya dauke musu siyan oxygen nata shine me siya.

Ta Dade sosai wannan Karan kafin aka sallamesu Kuma duk wanna taimakon da dadewan da sukai asibiti Bata taba dagowa ta kallesa ba sedai ta riqe qamshinsa da kaf asibitin Babu me irinsa bayan shi kadai,

Shi kansa Bai taba tsayawa ya kare mata kallo Dan ba dabiansa bane qarewa mace kallo dan haka tsakaninsu gaisuwa da Godia ne kadai Amma umman da baban sun Saba ahankali ahankali Dan sosai Allah ya Saka musu kaunarsa da tsananin ganin girmansa Dan tinda suke wannan dawainiyar ta 'yarsu Babu Wanda ya taba taimaka musu sai shi Dan haka suke tsananin kauna da ganin girmansa.
#MAMUH#
#DR JAMAAL
#AMEENATOU
#HAROON SEELAH
#FADILA
#JEDEENDS
#THE SEELAHS

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
21
Acikin kankanin lokacinda bamai tsayi ba iyayen fadila suka zama tamkar wasu ahalin Daya hada jini dasu Dan kuwa sosai yake taimka musu bayan matsalan ciwon Fadila wadda a yanzu tafara Dan sakewa tana amsar rayuwarta da kaddararta sbd shi din Daya bayyanar mata da wata sabuwar rayuwar hakama tana ganin iyayenta cikin walwala sbd taimako da kulawansa sai kawai ahankali take kallansa da wani irin matsayi me girma.

Shi kansa Dr Jamaal idan akwai abinda Bai taba tinanin zai samu kansa a rayuwarsa kwata kwata ba to son wata 'ya mace ne Amma Kuma ga dibbin mamakinsa sai gashi zuciyarsa Mai tsananin kamewa da kiyaye ko kallan mace ta kamu da wata tsaftatacciyar son fadila Mai tsananin gaske da Bai taba tinanin samun kansa a wannan fannin ba.

Son dayake mata ya ginu ne daga tausayi me tsanani tare Kuma da nutsuwanta da yanda ita gaba Daya Bata taba abokiya ba bare sakewa da mutane sbd tana kallan kanta a matsayin matacciyar data ke yawo da kararrin kwana,

Bata taba sakewa tayi muamala da mutane ba koyaushe a kadaice take sbd halinda rayuwarta ke ciki na koina da oxygen take yawo maqale a hancinta Babu abinda batareda shi oxygen dinnan takeyiba Dan haka rayuwarta take tsit Babu kowa a cikinta face iyayenta,

Hakan ne shikuma yayi masa sbd macen da batada hayaniya ko tashin hankali ko Daya itace macen dayakeda raayi wadda bazasu samu hayaniya ko damuwan zama ba,
fadila ta samu shiga zuciyarsa ne sbd wainnan halayen nata hakama ba qaramin so me girma da tsafta zuciyarsa ta kamu dashi Dan hka Kai tsaye ya sanar da iyayenta da sukaji kaman zasu shide Dan tsaban farin ciki da basa fadilan da dukkanin Saka albarkansu.

Fadilan da farko duk da sanin nesa nesa sosai yayi mata zarra yafi karfin ajinta dari bisa dari Amma kasa amincewa tayi da Hakan sbd tasan tausayi ne yake mata tsagwaronsa Amma ahankali ahankali tsarinsa da kalan tasa kulawan ya Sakata mutuwa gabaki Daya akansa batareda tasan da Hakan ba sai jinta tayi cikin sonsa sosai fiyeda yanda ma shi ya samu kansa.

*********
Haroon ne Kai tsaye Wanda yasan JEEY din yasamu irin macen dayake so duk da yayi tsananin mamaki me girman gaske dayaga fadilan black beauty da ita me tsari da nutsuwa Amma Kuma a yanda yasan JEEY yasan tsari da rayuwarsa ba lallai fadilan itace macen da raayi da rayuwarsa ke buqata ba sbd fadilan tayi sanyi da nutsuwa da yawa Wanda shi Kuma nasa nutsuwan da rayuwar rashin son hayaniya yafi na fadilan Dan haka rayuwarsu taruwa zatai ta mutu ba dadi ko annashuwa acikinta Dan haka yakega kaman rayuwar JEEY da mace me yar hayaniya da son Nishadi ya kamata sbd ta kawo annashuwa rayuwarsa.
Amma tinda Dr Jamaal Seelah guda ya Riga ya bawa fadila zuciyarsa babu abinda zaiyi bayan Shima ya kaunace sosai tareda girmama raayi da zabin Rabin jikinsa.

Alaqar Dr Jamaal da fadila yayi nisa sosai Wanda ahankali ahankali ya dawo da ita mace Mai farin ciki da annashuwa da walwala ba kaman yanda rayuwanta yake a Bayaba a tauye cikin qunci,
Shi kansa yana mamakin yanda yake tsananin son fadila wadda ta wani bangaren sai kawai Sonta ya fara sauyashi zuwa ga Maison qara zurfafa iliminsa na Addini Dan babanta malamin Addini ne Dan haka sai kawai ya sake zama busy Sam baida time na zaman gida ko zaman Shan iska da fita dasu Dad kaman yanda suka Saba duk weekend shi da Dad dinsa da Dad Lameenu da Haroon harma da matan family din wasu lokutan.

Idan yaje office da safe duk abinda yake gabansa ajesa yakeyi idan 2 tayi ya baro ya dawo gida ya shirya ya wuce karatun dasuke dauka shi da baban fadilan a wani course dayayi musu Register Mai tsada na karatun Addinin basa fitowa sai gap da magrib suna fitowa abinci da wanka kawai yakeyi ya wuce asibiti ya kwana acan wani lokacin Kuma ya dawo gida.

Baban fadilan ayanzu ya zama kaman mahaifinsa sosai suka samu shaquwa hakama ummanta wadda itace mace ta farko data samu matsayin uwa a gurinsa bayan Mum dinsa.

Ahankali ahankali harkokinsu Dad suka fara tabuwa da wannan sauyin da aka samu daga JAMAAL din Dan kuwa aikin site ma tini ya fara kokarin damqawa Haroon komai sai gashi baaje koina ba suka fara samun matsaloli abubuwa na tabuwa.

Babban abinda yake Kara dagawa su Dad hankali da sauyin shine faduwan dasuka farayi hakama yanda Jamaal din ke sake zurfafa a harkar Addini sai sukejin tsoron tayaya zai fara dasu idan yaji rai ta Dan Adam su baa bakin komai take a hannunsu ba
take sukaji kwata kwata aurensa dama yarinyar da iyayenta Bai kwanta musu ba musamman Dad Jin yayi yayiwa yarinyar da mahaifinta mummunan tsana hardai yanda yake bayyane so Mai tsananin gaske yakeyiwa yarinyar.

Dad Lameenu yafi Dad daga hankalinsa Dan kuwa bincike ya tabbata musu da mahaifin yarinyar yagama mallake zuciyar JAMAAL Dan haka komai lalace musu ma zeyi Idan Jamaal ya auri yarinyar,
Gata ba lafiyayya ba.

Duk yanda suka daga hankalinsu a boye da tsanar auren dayake son aje a nema masa baisani ba Dan Basu taba nuna masa shiyasa haka yakejin ma auren yake buqatan ayi kawai dan fadila ta dawo cikakkiya a rayuwarsa da kulawansa Dan ganin yakeyi koyaushe zaa iya samun matsalan oxygen nata wani abu ya sameta idan Bata tareda dashi.

Sosai yake sake samun sabbin akidu da ilimin Addini sosai Dan haka duk da Baya samun time na aikin dukiyarsu sosai Amma dai yanzu Yana tsananta taka tsantsan da bincike Dan Hana Haram shigowa cikin tsaftacciyar dukiyarsu.

Baban fadilan da kansa yake Kara masa karfin gwiwan tsananta bincike Dan kaucewa Haram.

Wannan shine babban kuskuren dayayi batareda yasaniba shi baban fadilan Dan kuwa shigar da zargi da tsananta binciken dayake Saka Jamaal yi tsakaninsa da iyayensa Dan dukiyarsu tini yakai maqura gurin tsananta batawa su Dad Rai.

Dan haka Kai tsaye Dad yace Jamaal bazai auri fadila ba Bai amince ba kwata kwata.

Mamaki ne ya kama Jamaal sbd baiga illan fadila Dan haka Shima yace baiga matan da a duniyar Nan zai iya nawa matsayin matarsa ba idan fadila.

Kafewa Dad yayi Shima akan wallahi tallahi Jamaal bazai auri fadilan ba.

Tin lamarin na kaman wasa sai gashi ya zama babba Dan kuwa maganar fasuwan auren Neman tabbata yakeyi Dan Mam Kai tsaye ya kira Dr Aleena Dan yasan ita kadaice duniya zata iya Hana Jamaal auren yarinyar ya hanu.

Dr Aleena kwata kwata batason Jamaal din Yana samun yawan sabani da Dad dinsa kaman Baya shiyasa ma Daya matsa ita ta hakura tabar Jamaal din ya dawo gurinsa Dan gudun abinda zaije ya dawo Dan idan Mam ya rasa abu yafison kowa ya rasa Dan haka ita tsananin son datake wa danta ta hakura ta gansa daga nesa yafi mata ace Baya duniyar gabaki Daya.

Maganar aurenma Yana gama magana da ita ta kira Jamaal din ta rarrashesa akan ya janye daga maganar fadilan ya sauya wata idan tausayinta yakeyi kobai aureba zai taimakawa rayuwarta.

Shiru yayi Bayan ya gama sauraron bayanan Mum din ya sauke numfashi mata sauti Dan yanajin fadan ya rabu da fadila wani abu ne har abada bazai iya ba,
Su tinaninsu tausayinta kadai yakeyi?
Basusan wane irin karfin son dayake mata da zai iya rabuwa da Dad ya aure su koma gurin mum dinsa suyi rayuwa acan.

Maganarta ta Saka hankalin mum din tashi Dan kuwa tasan fitina ce kwance zaiyi da Dad dinsa akan auren Duk da tana son fadilan itama sosai da 'dan nata sbd ganin irin zurfi da kakkaifan son dayake mata da batama dauka Jamaal Seelah zai taba son mace a kusa ba harma Mai karfi irin Hakan.

Koda ta sanar da Dad din Jamaal ya dage kan yanason yarinyar ransa mummunan sake Baci yayi Dan haka ya fuskacesa da kansa yayi masa fada sosai
Shi kansa Dad Lameenu Kai tsaye yace Bai aminta da aurenba.

Haroon da mum Atee ne suka ringa son lallabata Jamaal su fahimtar dashi ya hakura tinda mahaifinsa Baya son yarinyar
ga tarin mamakinsu daga karshe Jamaal zabar komawa yayi gurin mum dinsa.
Chapter 22 · 0% Book details