← Book details Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 31

Sashe 6

Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 1 min read

yadda nake wannan mutumin zaiyi saurin cin galabata dole in kara jajircewa. Wanda ba komi bane illa kokarin ganin ban yarda mun sake kadaicewa ba. Domin nima din 'adolscent' ce mai bukatar mahadin rayuwa, don dai auren ya zo ba a yadda na so ya kasance bane. Ya kasance ya zo min tareda wani mutum da ba abinda zai yi ya burgeni a rayuwata, ko ya wanke dattinsa dake raina. Ya yi murmushin da yafi kama da takaici ya tada motar. Bai sake magana ba har muka fita garin Minna. Yayin da ni kuma na tsayar da idanuna gefen da bishiyoyi suke zuciyata cike da farin cikin ko yaya ne dai kalamaina sunyi tasiri.
Chapter 6 · 0% Book details