Sashe 25
Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ALLAH YA KASHE FA'EEZ BAMALLI IN HUTA. Duk da cewa tsakanina da Ubangijinnawa ban taba yi ba sam. Kuma ban taba fadin hakan daga karkashin zuciyata ba, sai, dai a fatar baki. Banga amfanin sauran rayuwata ba! Idan nayi la'akari da manya-manyan kura-kuran da na tafka ban yi 'repenting' dinsu ba. Wadanda nake ikirarin LOKACI zai bani damar goge su, gaskiya ne babu wanda yake sama da KUSKURE sai dai lokacin da nake ikirarin zai canza komai... bai bani wannan damar ba...!!! Kuka da gunjin da nake gunzawa da shekawa a fili da zuci, yasa ban san tuni munzo gidan Baban Kaduna ba sai da naji Isa na kira. "Munzo fa Hajiya...". Na sunce kullin kaina na zagayo dashi wuyana don sai a lokacin na lura ko mayafi ban dauko ba. Na rarrafa na fito daga motar. Bana ko ganin abinda yake gabana. Banyi mamakin rashin haduwa da kowa a harabar gidan zuwa ciki ba, bana ganin hanya, illa kafata da tuni ta riga ta gane kowanne sako da kowanne lungu na gidan Baba Mukhtar A.B Giwa. Gaba dayansu suna tattare a babban falon gidan inda na sanya kafata, manyan gidan da yaransu, babu wanda baya kuka na fitar rai a falon cikin matukar kidima na doshi Mama Asma'u, wadda idanunta suka yi luhu-luhu don kukan da harshe ba zai iya bayyanawa ba... Nayi zaton ma zan tadda FA'EEZ a falon. In hadiye bakin cikina. Amma yanzu na tabbata FA'EEZ YA RASU A HADARIN JIRGIN SAMA!!! Na kama Mama cikin gigicewa ina wani irin kuka hawaye na min lugulgude da ambaliya a fuska... "Mama da gaske Fa'eez ya mutu??? Da gaske bazan ci ribar wannan SON ba ma a wannan karon???" Mama kuka kawai take, ko amsa daya cikin tarin tambayoyina ta kasa bani, Ta kankameni a kirjinta kawai amma ta kasa magana. Baban Kaduna ne ya shigo yana dafe fa kansa, yana fadin. "INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN... da gaske jirgin ya fadi, daga Kanon muke, Bashir din ma ya kamo hanya ne don ya gaya mana yayi (accident) yana asibitin koyarwa na Zaria babu yadda yake... Bamu san wa yaje ya gayawa Hajjah ba ta fadi! Barin jikinta ya jikkata. Allah daga gareka muke kuma gareka zamu koma... Ba Ka daurawa rai abinda ba zata iya ba, amma wannan jarrabawoyi da kayi a garemu masu tsauri ne... muna rokon sassaucinka da afuwarka idan mun kasance ne masu saba maka a kan sani ko bisa rashin sani. Hakika Kai Kaine Sarkin da bashi da mahadi, muna rokonka kudurah da iradarka akan wadannan jarrabawoyi namu zuciyoyinmu sun gaza dauka, kwakwalen mu sunyi rauni ga rungumarsu... Yaa ASSAMADU, KADIRAN ALAA MAN YA SHAA'U muna rokon sassaucin ka....!!!" Wani rugugi da hargagi naji a cikin kaina. Na tabbatar dai yanzu FA'EEZ YA RASU!!! Bayan wannan ban sake sanin me ke faruwa a duniyar ba... Ban sake sanin inda kaina yake ba...!