← Book details Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 31

Sashe 10

Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani gashin kaza yake ci yau da bai taba cin mai dadi da taushinsa ba, koko santin hannun daya sarrafa shi ne, bai sani ba. Kunnensa har motsi yake musamman da abin ya hada da yunwar wuni guda. Tun barowar mu Minna bai ci wani kwakkwaran abinci ba, sai ruwa da lemo yake daddaka. Tunda ya fara bai yi motsin kirki ko magana ba, sai da ya zuge kasusuwan katuwar kazar nan gaba daya.
Da ya kammala kasa jurewa yayi sai da ya dangana da kofar dakina. Ya rausayar da kai yana rike da kofar.
"Aunty Fa'izah, daga yau, a duk inda muke, zaki gasa min kaza da (chips) da wadannan yatsun naki, a kowanne dare matsayin (dinner) dina. Zan samu Fa'izah na?"
Ban amsa ba, sannan ban kalle shi ba, na ci gaba da jera kaya cikin (wardrove) kamar bada ni yake magana ba.
Ya gaji da sauraron amsata, ya aro (extra) hakuri ya kara akan wanda yake da shi, murmushi ya karawa zuciyarsa. Wani bangare na zuciyarsa na cewa, "There's alot of improvement. Is a matter of time!".
Washegari ban tashi da wuri ba sai misalin karfe tara na safe. Badon komai ba sai don sanin babu nauyin sallah akaina. Nayi wanka ba tare da wata kwalliya ta kuzo ku gani ba. Babbar rigar shadda mai aikin surfani na sanya, nayi daurin kai sassauka da kallabinta, na fesa turare 'Escada sentiment' na nufi (kitchen).
Ruwan tea na fara dorawa a (water heater) sannan na debi dankali dai-dai cikin mutum biyu na soma ferewa. A haka ya cimmani cikin madafin. Ya hade cikin bakar shaddar rini mai ratsin ruwan makuba, yayi sharr yayi (fresh) kamar sabon ango sai fesa kamshin '212' yake.
Ya saki murmushi mai kayatarwa cikin fadin, "Good morning Aunty Fa'izah".
Na ci gaba da firar da nake yi, ban kalleshi ba sai ta gefen ido, haka bai samu amsar gaisuwarsa ba. Bana son wannan kulanin da yake yi, na fi son tunda zama tare ya zama dole, to kowa ya ci gashin kansa kamar yadda ya ce a farko kamin in shigo gidan kowa yayi wadda zata fisshe shi, koko rayuwar da yayi amanna da ita.
Ya dauki wata wukar cikin fadin, "Bari in tayaki ba don halinki ba".
Ya fara ferewa da gani bai iya ba, sai zaftare tsokar dankalin yake. A haka aka yi firar aka zo wajen daddatsawa, nan ma ba iyawa yayi ba sai yanka su yake ba fasali, wani kudi wani bashi. Bai ankara ba ya sharce dan alinsa da wukar. Nan da nan jini yayo ambaliya. Ya yi saurin ya da wukar ya tara danyatsan a famfo jinin na bin ruwa.
Sai naji tsigar jikina na tashi ganin yawan jinin dake fita. Kamar yadda ya ce din ne idan babu soyayya akwai kauna ta 'yan uwantaka. Ban san sanda na wuce daki na dauko turaren dana fesa ba na dawo na kashe famfon (sink) din da ya kunna na soma fesa turaren akan yankar. Ban fasa ba sai da gudun jinin ya tsaya. Na gutsiro (tissue) na danne yatsar, duk kokarin da zan iya nayi wurin ganin bamu hada ido ba. Shima bai takura da sai mun hada din ba, kawai cewa yayi.
"Thank you!".
Na bi na tattare fuska na hade wuri guda cikin raina cewa nake, " Ni bana son wani tayin aiki, a barni da likitancin da ban karanta ba". Amma a fili aikina na ci gaba da yi bance komai ba.
Sai ya jingina da kabinet din (kitchen) din yana kallon yadda nake ayyukana cikin nutsuwa da hada hankali guri guda.
Na bude firji na debo kwai ina fasawa sai ya baro jikin (cabinet) din ya iso gareni. Cikin murmushi ya ce.
"Let me help you".
Na ce ciki-ciki, "Barshi nagode".
Bai karbi godewar da nayi ba ya dauki daya, maimakon ya hada shi da uwansa ya fasa ko ya fasashi da wuka, sai ya hada shi da goshina ya juye a fadi ka mutun da nake juyewa. Ya sake daukar daya, ya hada shi da tsinin karan hancina shima ya juye ya yar da bawon a (dusbin).
Nan da nan ya fashe su duka guda takwas din a goshi da hanci na, ko a ina ya koyo wannan fashin kwan oho! Nan take na soye shi tas na gama duk abinda nake yi yana tayani. Amma cikin raina bana godewa, a kyaleni yafi mun.
Karar kararrawar shigowa tasa na samu yadda nake so, wato ya fita ya barni. Can na jiyo tashin sautin su shi da Surajo ne.
"Na dauka tuni ka kama hanya?" Cewar Fa'iz.
"Ni na isa in tafi, ban zo naga dakin Madam rikici na sayi baki ba?"
Tare suka zauna kujerun falon rike da hannun juna.
Kai sai yaushe zaka wuce? Ko kazo kenan".
Ya ce, "Two weeks off gareni, yau kuma kwana na hudu, saura kwana goma inaga".
"Tare zaku wuce amma?" Surajo ya tambaya.
"Don Allah ka rufa min asiri kada ka ballo min liki irin wanda ka saba ballowa, na samu an daina yi min hayagaga ko ba'a bini ba na gode".
[1/4, 12:23 am] Takori: Abin ya baiwa Surajo dariya, in wani ne ya bashi labarin Abubakar Mukhtar (sunan da suke kiranshi) zai koma haka akan mace karyatawa zai yi. Soyayya ba karya bace, a yau ya kara yarda da hakan. Ya shiga girgida kai kamar kadangare.
"Tana ina ne? Ban ji motsinta ba. Ga hotunan (cocktail) din ku fa na wanko".
Ya amsa ya aje gefe ba tare da ya bude ba yayi mai nuni da (kitchen) da girar shi.
Dariya Surajo yayi, "Kace har girki ake mana!".
Shima dariyar yayi, "Mai dadi kuwa".
Suka yi ta dariya kamar wasu shashashan madina, sai da suka yi mai isarsu tukunna.
Surajo ya ce, "To yanzu yaya za'ayi batun tafiya UK?"
"Sai yanda ta yiwu Surajo, bani da sauran dabara, duk abinda zan iya nayi, na bada hakuri, nayi fada, nayi wa'azi, nayi nasiha. Zan iya cewa (there are lots of improvements) sai dai bata yi min magana, sannan in nayi bata amsa min da baki, sai dai tayi a aikace. Kuma ba musu, ba rashin kunya, duk abinda nasa ta daga jiya zuwa yau tana yi".
Surajo ya ce, "To Alhamdulillahi, hakuri (still) ba abinda baya bayarwa. Kuma ina ganin inta bar kasar zuwa inda bata da kowa komai zai tafi (normal)".
Ya ce, "Nima tunanin da nake kenan, amma Surajo (how easy is that)?"
Dai-dai lokacin da na fito daga (kitchen) dauke da fadi ka mutu ina jerawa akan (dining). Duk suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su. Jikina ya bani zancena suke yi. Zan koma (kitchen) Suraj yayi gyaran murya.
"Madam ba gaisuwa yau ma?"
Ina tafiya ban tsaya ba na ce, "Ina kwana?"
Ya ce, "Lafiya lau, sannu da aiki".
Na ce, "Yauwa".
Na shigo don dauko filas din ruwan zafi. Suka dubi juna suka yi murmushi.
Tare suka karya kumallon shi da Surajo yana tambayarsa abinda yaji masa ciwo. Ga ammakin Fa'iz sai ya kasa gaya masa kada yayi masa dariya don a hakan ma bai daina mamakin canzawarsa da rauninsa ba, gani yake yayi min sako-sako da yawa. To abin ne shima yazo amsa 'beyond comment' (sunan wani ganyen shayi), idan yana gaban Fa'izah manta kansa yake da (identity) dinsa.
Cewa yayi yankewa yayi da reza ya ce.
"Kai me ya hadaka da reza kamar wani wanzami?"
Ya ce, "Don Allah ka kyaleni haka Surajo, kwakkwafin ka ya isheni".
Wata irin dariya Surajo yayi wadda ke nuna ko dai bai gano ba to ya kusa ganowar. Ni kyale su nayi na koma daki na kwanta don rama bacci.

***
Ban jima da kwanciya ba bacci ya dauke ni, ba ni na farka ba sai azahar. Nayi wanka nayi (brush) ba don banyi na safe ba sai don inji dadin cin wani abu. Domin da mahaukaciyar yunwa na tashi. Na fito falo na duba (dining) na tarar da (plate) daya da basu taba ba, na hada 'tea' mai kauri na fara warware hanji na dashi sannan na zauna na soma ci. Na kammala na kwashe komi na hada da wadanda nayi amfani dasu a (kitchen) na wanke. Na adana komi wurinsa.
Dana kammala sai kadaicin ya isheni, na kasa zama wuri daya. Tunanina ya bani in zagaye gidan cikinsa da wajensa in gani, sai na sanya mayafi da (slippers) na fito harabar gidan na zagaya baya.
Dawisu ne guda biyar (peacock) mata da maza, wasu a kasa, wasu akan katanga sun bude kyawawan jelunansu abin gwanin ban sha'awa. Sai na gane sune ake maganar su jiya sun kwanta da wuri. Na debi dawar da na gani cikin buhu a kofi ina cilla musu da dai-daya. Sai ga wani saurayi ya bullo yayi min sallama, na amsa muka gaisa. Jiya ban kalle shi ba balle in san kamanninsa, da yayi magana ne na gane shi.
"Kai ne Ya'u?"
"Eh, ni ne Madam. Wannan aikina ne, don Allah ki bari zanyi, basu dade da cin abinci ba".
Nayi murmushi na ce, "Ka dinga share kashinsu daga yau kawai Ya'u. Ina so na karbi ragamar ciyar dasu da hannuna, ina son Dawisu Ya'u".
Sai yayi dariya ya ce, "Hakan ba zai zama matsala gareni ba wurin Yallabai?"
Nayi murmushi nima, "Ba zai ji ba insha Allahu".
Ya ce, "To Allah Ya ba da lada Aunty".
Na amsa, "Amin Ya'u".
Ya wuce ya barmu, na ci gaba da jefa musu dawa duk suka yo gabana suna dauka da bakunansu masu kyau suna kara baza bindi.
Chapter 10 · 0% Book details