← Book details Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 31

Sashe 14

Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a tare dani. Nayi murmushin da na tabbatar zai kwantar da hankalinta, gaba daya jikina yayi sanyi kalau. "Ba gidan nan zan dawo ba. Tunda muka tafi ma ai ba a gidan Baban Kaduna muke ba, Walida bata gaya muku ba? Muna gidanshi ne a Malali GRA". Ta dan zuba min ido kamar bata yarda da abinda na ce ba. Na ce, "Wallahi Momi da gaske nake, kuma ki tambayi Mama. Ko ya tafi a can zanyi zamana nayi miki alkawari, in kin ganni gidan nan ko gidan Baban Kaduna ko Giwa ko Kano wajen Ya Rabi gaishe ku nazo yi". Anan ne ta saki fuska ta ce, "Shi kenan. Su Walidar basu dawo bane, daga can suka wuce Lagos wajen su Zanirah". Dai dai lokacin da muka ji sallamar shi a dakin, abin mamaki ya saki ba kamar yadda muka zo ba. Ya ce, "Momi zamu wuce, ni kuma gobe zan wuce Wales din kasar England, na samu aiki da 'British-Airline' zan jima ban zo ba sai na samu (break) mai dan tsaho". Momi ta sanya albarka tayi addu'a da Allah Yasa matakin arziki ne, Ya kara rufa asiri, Ya kiyaye sharrin karfe da na iska, Ya cire haramun daga cikin abinda za'a samu alfarmar Manzo (S.A.W). Ya fadada murmushinsa cikin jin dadin addu'arta yana fadin. "Amin Ya Rabbi Maman Walida". Na mike, ta dubeni ba yabo ba fallasa. "Akwai garin semo da bushasshiyar kubewa da bushasshen kifi in kuna bukata". Na ce, "A'ah Momi, ba yanzu ba dai, zan aiko in ina bukata". Ta ce, "Ke kika sani". Da muka shigo Kaduna ya tsaya wani babban 'Shopping Mall' bai yi min ko tayin shiga ba shi kadai ya shiga abinsa. Ya jima sosai kafin naga yaran kantin sun biyo shi da manyan ledoji, suka zuba a bayan motar, sai katon-katon na abin sha (ruwa da lemo) kala daban-daban. Akan hanyarmu ta shigowa Malali ya tsaya ya tsayi gashasshen nama muka karaso gida duk jikina a sanyaye yake. Muna shiga Ya'u ya taremu, sai na samu kaina da kara jan lullubina na rufe har rabin fuskata ban san dalili ba ko don ya nuna baya so din ne da gaske? Bazan so ya zamo nayi sanadin hanyar abincin wannan bawan Allah ba, wanda ga dukkan alamu ita ce madogararsa kadai. Ya kwashe komai daga bayan motar ya shigar (kitchen). Yayi mana sallama ya fita. Ya maida kofar falon ya rufe da (key) ya dawo ya zauna bisa (carpet) ya kunna t.v tashar CNN yana rike da (remote) ya dawo ya zauna, ya janyo ledar namansa yasa a gaba yana ci yana sauraron labaran, bai kara kallo na ba kamar yadda bai nemi 'chips & chicken' ba. Na mike ba don an sani ba na shiga (kitchen) na soma sarrafa su kamar yadda na saba, amma na yau (with additional aroma and taste) saboda kamar ina neman hanyar shiri ne ko yaya ne dai na kasa gane kaina. Wata zuciyar ta ce tunda ni nayi nasara nawa ra'ayin aka yi masa fin karfi aka bi, bari in dan kyautata. Dana kammala na aje a (dining) kamar yadda na saba, na ce. "Ga (dinner) din". Kamar ba da shi nake ba kallon t.v kawai yake duk da na tabbatar ya ji ni saboda ba wai yasa muryar t.v din da yawa bane, a'a dai-dai jinsa, raina ya dan baci na wuce na shige daki na sayo kofa amma ban sa mukulli ba. Can naji motsin kwanuka a (kitchen_, na daga labule ta taga ta wadda kana hango duk abinda ke faruwa a (kitchen) sai na hango shi ya dora 'yar tukunya akan (cooker) ya saka indomie guda biyu bai ko cire ledar maggi da chili din dake ciki ba ya kawo ruwan zafi wajen kofi uku wanda ya sha kan indomin har baka hango ta ya zuba, ya rufe. Ya fita daga kicin din ya koma ya ci gaba da sauraron labaransa. Kamar inje in duba wannan lamari wata zuciyar ta kwabeni abinda ba ruwan ka ance dadin kallo gare shi, na koma nayi kwanciyata. Anfi minti talatin kafin inji shi ya koma (kitchen) din, ban san abinda ya faru kuma ba bayan nan. Bayan kamar minti biyar naji fitarsa a mota, tsegumi har tsunkuli na yake nayi (kitchen). Na bude tukunyar daya dora a wuta. Indomin ta hadu ta dame ta zama kunu zance ko koko ko tuwo, gatan nan dai ba suna ba fasali. Na tabbata ba zai iya ko tabawa ba balle ya sanya a bakinsa shi ne ya fita yaje ya sayo. A raina na ce, "Ashe dai girkin banza na da amfani tunda sai da shi ake rayuwa". Na kara duban dabgen da yayi nayi dariya na mayar na rufe na koma daki. Nayi zaton zan kuma jin duriyarshi kafin nayi barci, amma har garin Allah ya waye banji ba. Haka dana tashi yin sallar asubahi na fita falon ko zan ganshi sai abincina na daren jiya (chips and chicken) kadai na tarar akan (dining table) inda na ajiye shi ko matsar da shi ba'ayi ba. Daga nan nayi brush na koma daki, ban tashi ba sai karfe tara na safe. Da hanzari na nufi (kitchen) na soma aikin hada masa karin kumallo, amma na yau 'is special' kamar na daren jiya duk da raina ya sosu da rashin cin da bai yi ba. Cikin dan lokaci na kammala 'scottish egg, plantain with syrup, bread with jubnah' da ruwan na'a-na'a. Cikin dan lokaci kalilan na kwashe na jiya na shirya su a inda ya saba karyawa a kwanaki goma sha ukun da muka yi tare. Na koma daki nayi wanka nayi shiri cikin atamfa sufa ja mai ratsin kore da baki wanda dinkin ya zauna a jikina sosai, zanin ya bude daga kasa. Na fesa turare 'escada sentiment' na kalmasa dauri sassauka, na dubi kaina a mudubin dogon yaro na yi wani irin 'fresh' (looking takeaway) ko ni kaina na baiwa kaina sha'awa. Sai na samu kaina da tambayar kaina kwalliyar ta mece ce? Mene ne dalilinta? [1/4, 12:23 am] Takori: Dana gaza samarwa kaina wadannan amsoshin guda biyu, sai kawai na fita, ina juyowa muka hada ido yana kokarin fitowa daga nashi dakin janye da (travelling bag) mai matsakaicin girma 'troller' ruwan zuma. Dammm! Naji kirjina ya buga, bugawar da ba'a kirjin kadai ta tsaya ba ta hudo ne har cikin zuciyata. Sanye yake da riga fara anyi rubutu da shudin zare 'TOMMY HILFIGER' da shudin wandon (jeans) turrare, sumar nan ta kwanta tayi luf a saman kansa sai sheki take, inda duk ya motsa sassanyan kamshin '212' ke tashi.. Ya saya kwayar idanunshi cikin gilashi 'porsche' mai duhu ainun, don haka kai tsaye ba zan iya cewa ga halin da kwayar idanunshi ke ciki ba. Ya ajiye jakar a kusa dashi ya zauna a kujera sosai ya zage zip dinta, ya ciro katin ATM ya dago ido ya dubeni ina tsaye a inda nake ban ko motsa ba. "Ko zaki iya zama?" Abinda ya ce dani kenan. Tamkar wata rakuma da akala na bi umarnin furucin nasa, na zauna a kujerar dake fuskantarsa. ATM card din ya aje mani gabana, ya yagi takarda yayi rubutu itama ya turo mini. "Ga PIN dinsa nan na rubuta a jikin takardar na bankin UBA ne, in kina da bukatarsu sai ki kira Shu'aib a waya ki turashi ya debo miki adadin da kike bukata. Anjima Surajo zai kawo miki waya ni na tafi ban san kuma ranar da zan dawo ba. In kina da matsala ki kira Mama ki gaya mata, Ya'u zai ke kawo miki (recharge-card) duk sati, ban yarda da fita ko bakin (gate) ba in ba lalura ta rashin lafiya ba tunda rayuwar da kika zaba kenan". Ya mike yana zuge jakarsa. Idona ya cicciko da kwallah. Ba zan ce bai yi min dai-dai ba, kuma bazance yayi min dai-dai ba. Na san akwai hakkokin shi da yawa akaina, wadanda na sanya kafa na shure na take akan sanina, wadanda hujjojina babu ruwan Allah dasu. Auren Fa'iz dake kaina kadai ya sani dole in bude baki yau inyi magana saboda halin rai, yau yake da tabbatas gobe babu shi. Sannan sha'ani na tafiya wanda bana fatan hakan. Muryata na rawa na ce, "Ga abincinka fa ka karya mana sai ka tafi". Ya dubemu duka ni da abincin ya hararemu duk da ance aikin banza wai harara cikin duhu don kuwa bakin gilashi ne a idonsa, ya ce. "Ki rike kayanki, na gode. Akanshi dai kike yi min tsaki in na saki, to insha-Allahu ba zan sake cewa ki dafa min wani abu ba, sai kin ganni ma balle ince ki bani abincin. Zan tafi inda ba sai nace a bani za'a bani ba, balle aje ga goranta min ko yi min tsaki". "Kayi hakuri don Allah...". Na fadi cikin kuka. Ya dubeni cikin mamaki, nasan bai zata ba. Ni kuma harga Allah banyi hakan ko fadi hakan don wata manufa ba, sai don kar ya tafi da fushina in kasance cikin fushin Ubangiji da tsinuwar Mala'iku har yaje ya dawo, wanda ban san ranar dawowar tasa ba. Ya koma ya zauna, sannu a hankali yake zare gilashin idonshi, ni kuma ina ta sharbe. Ya kirani da wata irin kankanuwar murya. "Fa'izah!". Na cira jajayen idanuna na dube shi, ban amsa ba amma idanuna sun nuna ina sauraron sa ne. "Komi ya wuce?" Ya tambaya. Na sunkuyar da kai ina jan zaren carpet bance komai ba, amma na daina kukan sai ajiyar zuciya. Ya baro kujerar shi ya iso gabana yayi zaman dirshan, ya kamo hannuna na dama ya sarke cikin nashi. Na dago kai na dubeshi kana nayi sauri na maryar na sunkuyar. Ko da can bama iya hada ido da wadannan 'sexy' idanun balle yanzu? Da aka samu karin ilhamomi masu yawa a cikinsu? Ya sumbaci goshina, idanuna, karan hanci da bakin da yakan ce rashin mutuncin dake cikinshi ya fishi girma, mun dade cikin wannan halin, da dukkannin mu bamu taba tsintar kanmu cikinsa ba, zuciyoyi da ruhinmu sun hade sun cure wuri guda, muka samu kanmu cikin mantawa da duk abubuwan da suka faru cikin rayuwarmu. Dai dai lokacin da kararrawar shigowa falon ta soma kara. Mikewa nayi cikin sanyin jiki,
Chapter 14 · 0% Book details