← Book details Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 31

Sashe 24

Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gaya miki da kansa ba sai su Walida?" Nasa hannu na kautar da zirin gashina dake disar da ruwa a jikina, na ce a hankali. "Ya yo waya ina bacci, ya sake yowa ina cin abinci, daga nan bai sake yowa ba. Kuma laifin Walida ne da bata bani wayar ba, sai ta ce wai ina bacci, ko ta ce abinci nake ci don shirme irin nata". Mama ta ce, "Ai shi kenan. DOn Allah kiyi amfani da kayan lefenki kinji Fa'izah! Ya gaya min baki taba amfani da duk abinda ya dauka ya baki ba. Sakon da Shu'aib ya kawo kuwa kada kiyi wasa da yadda na ce a cikin takarda kinji Fa'izah na?" Tausayin Mama da wani bala'in son danta ya kara kamani, na kara kwantar da kai a cinyoyina na kasa magana. SHin ita din wacce irin UWA ce mai maida nata ba nata bane? Ta ce, "Ba abinda kike bukata ta fannin kayan girki?" Na ce, "Ba abinda Shu'aib bai kawo min ba Mama, har da wanda bana bukata duka ya kawo". "Yayi kyau". Inji Mama. Muka yi sallama cikin girmama juna. Ni na fara aiwatar da umarninta. Wata irin kwalliya na soma da Voyal din Hilton pitch and maroun, kasancewata wankan tarwada sai kalar ta wani irin kwanta ta bi fatar jikina. Na dauki voyel din ne cikin kayan da Mama ta kira da lefe na a dinkensa na ganshi, dinki mai kayatarwa da daukar ido na doguwar riga budaddiya, sai dai daga sama ta kama jikin tsam. Na nada dankwalin a kaina ya kwanta lambam. (Make up) dina bai yi yawa ba, (very cool and sexy). Don karawa aya zaki na dauko takalmi cikin kayan, (flat) ne pitch dan Italy na zura siraran kafafuna. Turaruka kala-kala nayi amfani da su, duk dakin ya dumame da kanshi mai sanyi da sanyaya zuciya. Na karashe shanye romon kazar Mama, na shiga (toilet) nayi (brush) na fito na dawo falo na kishingide cikin (three seater) ina kallon tashar ALJEZEERAH. Dai dai lokacin da agogon bangon dake 'main palour' yua buga karfe hudu da minti talatin. A lokaci daya na murdo radio daga I-pad dina ina sauraron sashen Hausa na BBC, ni kaina ban san wanne nake sauraro ba tsakanin Radio da talbijin. Sai dai babu wanda hankalina ke kansa cikinsu, hankalina ya karkasu ne. Wani ya tafi ga tunanin wace irin tarba zan yiwa Fa'izun in ya shigo? Sannu da zuwa ko sannu da hanya? Sannu da hanya ko ina wuni? Ni kaina ban sani ba. Wata mutum ce ni din a yau dake ninkaya cikin maliyar SO, take neman a karbeta ko yaya ne a zuciyar da bata da tabbaci a kanta. Daya kashin kuma ya lula ne cikin tunanin tarbar da shi zai yi min. 'Will I be accepted? Appreciated? Trusted? Believed? Ignored or abandoned??? Karfe biyar ta buga na soma waiwaye ina duban kofa, haka duk motsin da masu karanta labaran Aljezeera da na BBC suka yi tsammani nake shigowar mota ne, ko kararrawar shigowa falo. Biyar da rabi... shida na yamma babu Fa'eez babu mai kama da shi. Bakwai na dare ta shude babu labarin Fa'eez Bamalli balle sallamarsa. Na soma karaya, kwalliyar ta soma gushewa da kanta, Gwiwata ta soma sagewa da kagara da zakuwa. Mutumin da akace zai zo biyar na yamma, shi ne har karfe takwas na dare, babu shi babu alamarsa. Da kyar na iya mikewa na bada faralin magariba da isha. Takwas da rabi na samu wayar Mama, ina dagawa ta dora da tamabayar da ta girgiza ni ko ince ta firgita ni. "Fa'eez Malali ya soma isowa kenan? Ni ina nan ina ta zuba ido shiru, to kice da shi in ya huta Babanku na son ganinsa da safe kafin yaje ko'ina...". Ban san sanda hawaye ya barke min ba, na soma shasshekkar kuka da ma kiris nake jira. Hankalin Mama ya tashi. "Ke lafiya? Babu lafiya yazo ko kuwa?" Cikin kuka na ce, "Bai fa dawo ba kwata-kwata, kuma babu wayarshi babu ta Yaya Bashir. Nayi (trying) ta Yaya Bashir din a rufe take. Shi kuma wadda ya kira da ita dazu da na duba sai naga ashe anyi (hidden No.) din". Mama tayi dan jim! Kafin ta ce, "Ya isa! Nan da karfe tara in bai iso ba zan turo Malam Isa ya dauke ki, Babanku sai ya bi sawun su Kanon shi da Shu'aib, idan yayi tafiya irin wannan ba inda yake fara sauka sai nan Jabi Road, daina kukan hakanan, watakila suna Kanon". Nayi shiru ina goge hawayena tana bani hakuri, da cewa kukana yana tayar mata da hankali. Jikina a matukar sanyaye na aje wayar gefe, lokaci guda hankalina ya kai ga abinda ake fade a tashar ALJEZEERAH, tare da wanda BBC ke fadi duk a lokaci daya, wato; "JIRGIN BRITISH DA YA TASO DAGA HAVERFORDWEST AIRPORT DA KARFE GOMA NA SAFE, YA FADI A SYCHELLS ISLAND TSAUNIN DAKE HADAKAR KASAR SINGAPORE DA...... Ihu da kururuwa na saka, wanda ya tafi tare da yin fatali da I-pad din da kafata ta kwankwatse a kasa, na mike tsaye ina ta kururuwa hade da INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'OUN. Na dora hannuna duka biyar a kaina, wani irin azababben kuka na saka dake ketowa tun daga cikin hanji da koda ta, cewa nake. "Noooooo!". Na yunkura na doshi kofa hannuwana aka, juwa ta kwasheni ta kayar. Ban daddara ba na sake yunkurawa, burina in bar gidan zuwa inda za'a ce min ba dai dai naji ba, ko kuskuren hanyoyin sadarwa ne. Juwar ma bata yi kasa a gwiwa ba wajen sake kayar dani. Sai na soma rarrafe akan gwiwoyina dai-dai lokacin da wayar da ta fashe a kasa ke nata kuwwar duk da tsagewarta. Da rarrafen na isa gareta na sata a 'handsfree' dukkan hannuwana da jikina baki daya rawa suke da karkarwa. Tun kamin inyi magana naji muryar Surajo cikin karaji da kuwwa yana tambayata. "Fa'izahhh! Fa'eez ya sauka karfe hudu na yamma?" Na kara rikicewa da kuka, cikin in'in'ina..., "Naji...naji...nima...nima Suraj...jir...jirginsu ya fadi ko?" Surajo ya ce, "Hasbunallahu wani'imal wakeel! Ni'imal maula wa ni'imal naseer!!! Gani nan zuwa yanzun, nima bisa hanya nake". Na durkushe anan na cigaba da kuka ba kakkautawa, hawaye na hade da majina. Dai dai lokacin da ALJAZEERAH suka shiga hasko jirgin a tsaunin daya fadi, ban san sanda na kwarara ihu da dukkan muryata ba. Abinki da unguwa irin GRA Malali, ba ruwan kowa da kowa balle wani yasan halin da nake ciki ya kawo min dauki, buzu yayi nisa domin na tabbata akwai tazara tsakanin bakin gate da cikin gidan wadda mota ma sai tayi tafiya zata iso. Ya'u kuwa tin dazun yayi min sallama da cewa ya tafi gida. Haka nan yanayin gininmu mawuyaci ne ko zubar ruwan sama aji balle a jiyoni, daga ni sai Ubangiji na muka san halin da nake ciki. A wannan halin Isa direba ya cimmani har cikin falon, ko yayi sallama ko bai yi ba ni ban sani ba, na dai ganshi tsaye a kaina, shi kanshi yayi wujiga-wujiga, idanunshi sun firfito sunyi jawur. "Mama ta ce inzo in tafi dake...". Ko tunanin rufe gidan banyi ba balle yafa mayafi na bi bayan Isa, sai shi ne ya dawo ya rufe kofofin. Tunda muka hau titi nake rasgar kuka, babu abinda nake tunawa illa musgunawa da kaskanci gami da rashin albarka, dana shekara yiwa mijina Abubakar Fa'iz tun ranar da aka daura mana aure. Muka kuma rabu, ba tare da na nemi cikakkiyar gafararsa ba, ashe Allah Ya rubuta iya tafiyar kenan, iyakacin sallamar kenan, iyakacin zaman kenan SAI A DARUS-SALAAM....! Na tuna yadda naci burin sauya akalar rayuwarmu, (from negative to positive). (So, kauna da mutunta juna. Ashe Allah Ya riga ya kaddara cikin kundin rayuwata BAZAN TABA CIN WANI BURI A RAYUWATA IN SAMU BA... BA ZAN TABA SON WANI ABU KO WANI MUTUM A DUNIYA IN SAMESHI BA!!! Inama ban zo duniya ba... YA LAITANI KUNTU TURABA...!!! Idan kuma zuwan duniyar kaddarata ce, inama ban kawo wannan lokacin ba, ina ma ban kawo wannan ranar ba, inama na rungumi KADDARA TA ta auren Abubakar ZABIN IYAYENA kowanne irin hali gareshi na yiwa iyayena biyayya kamar yadda Ummi ta ce! Kamar yadda Ummi tayi, kamar yadda Zaneerah tayi... gasu nan da manyan rabo tun a duniya kafin aje Lahira, da tabbataccen farin ciki da kwanciyar hankali wanda na tabbata ni har tawa mutuwar ta riskeni ba zan same su ba...!!! Inama mun rabu ne bayan na bashi jikin da yake rokon na bashi ya dauki budurcina da nake tattalawa shekaru ishirin da uku yana mai sa min ALBARKA??? Inama ban taba yin ramuwar gayya a rayuwata ba? Inama ban taba nunawa Fa'iz kiyayya ba... Inama mun rabu lafiya... da ko ba komai na tsira da wannan koda ban haifi kyakkyawan Da irin Fa'iz ba... inama...inama...inama... Inaman tana da yawa!!! A halin yanzu bani da abinda zan fuskanci Ubangijina dashi, ranar da tawa mutuwar ta riskeni. Banyi biyayya ga mahaifina da iyayensa ba tun farko, na sanya shi cikin bakin ciki da bacin rai maras misali. Na bashi kunya... na ba mahaifiyar shi da 'yan uwanshi... wadda ta sadaukar da kacokan rayuwarta da inganta rayuwarmu kuma komi tayi tayi ne 'for our own betterment' bata da ribar da zata tsinta a ciki, ta riga ta gama rayuwarta, ta gama cin ribarta ta Allah kawai take jira Hajjaty... bata cancanci abinda nayi mata ba ko sakayyar dana yi mata. Har kaurace mata nayi, don ta bani abinda tafi so a rayuwarta. Babu wanda ta yiwa zabi irin wanda tayi min, tabbacin ni din ma tana so na! Shin ni FA'IZAH cikin butulallun 'yan Adam wace iri ce??? Anya ba ni ce SHUGABAR su ba??? A yau FA'EEZ din ya bar min duniyar baki daya, in ci ta yadda nake sonta, da tsinke koda cokali, koma da cokalin kaya (fork). Banga amfanin sauran rayuwata ba, rayuwar da babu FA'EEZ a cikinta. Wanda suna ma daya aka sa mana, kamar yadda kamanninmu suke daya, duk da zuciyoyinmu basu samu daidaito ba tun muna kanana. Na tabbata na kuma yi amanna da cewa baki daya zuri'ar A.B ni zasu zarga da gushewar Fa'eez a doron kasa, tunda na sha faden ina addu'ar
Chapter 24 · 0% Book details