Sashe 26
Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read
***
Sanyin ruwan da ya ratsa kwanyar kaina, ya dangana da hakarkarina, ya zagayo zuwa wuyana da kirjina, shi ne ya maido ni hayyacina. A hankali nake bude idanuna ina lumshe su da son tantance halin da nake ciki? A ina nake? Me ya same ni? Cikin mafarki nake, ko kuwa idona biyu?
Cikin 'yan sakanni na fahimci a gadon asibiti nake, akan cinyar mutum mai taushi, fanka na wulwulawa, A.C na burari. A hankali kwakwalwata ta soma tariyo abinda ya faru, da kuma musabbabin abinda ya kawoni gadon asibiti, wanda ba zan gushe cikin addu'a da fatan Allah Yasa mafarki nake ba!
Nayi salati cikin wara idanuna sosai da jin muryoyi mabambanta na tashi cikin kunnuwana, daga mutanen dake zagaye dani. A lokacin memory dina (is back on network) duk abinda ya faru, ya kuma yi musabbabin zuwan nawa gadon asibitin ya dawo 'fresh' a kwakwalwata.
Na yunkura zan mike zaune cikin fashewa da sabon kuka, sai naji an kamani an maidani kwancen.
"Koma ki kwanta, 'relax Fa'iza, relax... 'Main Hoon Naa... (I'm here now)! And I will be here for ever, I'll not die and leave you... We are meant for each other!!!"
Wata tattausar murya ke fadi, cikin turanci mai gardi da taushin amo. Sai kuma dariyar Mama akunnena da muryar Momina na fadin.
"Ta gama suman, ta koma iya shegenta. Da dai ba ita din ce ba...".
Muryar Walida, "Kai Momi! 'She's no longer the FA'EEZAH YOU KNOW... Na rantse tana son mijinta".
Muryar Shu'aib, "Kaji Momi da wani zance mara dadi, ai mijinka-mijinka ne, kana son shi ko baka sonshi".
Na daga kai a sukwane, na dubi wanda ke rike dani, kuma wanda nake kwance akan cinyoyinsa, wanda ke shafa min ruwan a fuska, wuya zuwa kirjina... FA'IZ (ABUBAKAR), FA'IZ BAMALLI NE, FA'IZU MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA...!
Mijina abin sona, sanyin idaniyata, cikon farin cikina... 'The one that is always hunting my dream!!!
Makiyina, abokin fadana ada can, masoyin da babu kamarsa a yanzu...Wanda zaton guhewar sa a doron kasa kadai ke neman aikawa dani nima.
Mikewa tsaye nayi cikin wani irin zafin nama na rungume shi. Wata irin runguma kakkarfa, mai tafiya bisa umarnin zuciya da jagorancin gangar jiki, cikin kuka mai yawa wanda ya kasa tsayuwa daga idanu da zuciyata, amma wannan karon NA GODIYA GA UBANGIJI NE da ya kaddara zan sake ganin Fa'iz kafin Allah Ya dau raina. Zan rungume shi cikin jiki na kafin saduwata da Ubangiji na!
Sosai yayi min masauki a katafaren kirjinsa, ya rufe ni ruf da gaba dayan gangar jikinsa ya zagayeni da hannayensa, ba tare da la'akari da iyayenmu da kannemu dake zagaye damu ba, su din dariya suke suna karawa, har da masu yin tafi, cikin nasu farin cikin, da godiyar Ubangiji.
Na dago kaina na dube shi ina kuka, na shiga bugun kirjinsa da hannayena biyu.
"Don me kayi mana haka yaya Fa'iz? Don me? Me yasa ka tsoratani ka tayar min da hankali irin wanda zai iya sawa zuciya ta buga! Kasan baka cikin jirgin kace kana ciki kawai don ka tayar da hankalinmu? Eye Yaya Fa'iz me yasa? Me yasa?? Me yasa???"
Na koma na rukunkume shi da karfin gaske na cigaba da kuka kamar mai tsoron kada ya sake tafiya ya barni, ko wani al'amari makamancin wannan ya sake rabamu.
Baice komai ba, idanunshi ya rufe bai bude ba, ina iya jiyo bugun zuciyarsa mai bugawa da sauri-da-sauri. Wannan wata rana ce mafi soyuwa cikin ranakun rayuwarsa da ba zai iya fassarata ba, ranar da yake tsammanin har ya koma ga mahaliccinsa ba zata taba zuwa ba!
Ya rasa abinda zai yi ko zai ce da zai nuna dumbin farin cikin da yake ciki. Yau Fa'izah ce rungume da shi gaban BABA da MAMA, BABAN A.B.U da MOMIN A.B.U... Wata rana cikin ranakun rayuwarsa mai dumbin tarihi in ka cire ranar da ya karbi aninin zama cikakken matukin jirgin sama, da ranar daurin aurenshi da FA'IZAH A.A GIWA.
Duk dakin asibitin ya dauki tsit, bayan shasshekar kukana dake tashi a hankali a dakin da bugun zuciyar Fa'iz Abubakar. Abinda ya iya cewa a wannan lokacin cikin sassaucin murya, inka cire ni Fa'izar dake rungume dashi, babu wanda ya iya yaji a dakin, ni din ma don na kasance cikin masu karfin ji ne.
"FA'IZAH, ashe kina sona kike wahalar dani?"
Ya fadi tare da kai hannu ya dago habata, ya dubeni cikin ido. A hankali Baba Muntari ya zame ya fice daga dakin, Baban A.B.U yabi bayansa, Momi da Mama suma ficewar suka yi, Shu'aib da Yahya suma suka fice. Amma Walida da su Junior suna tsaye kyarr idanunsu na kallon soyayya mai dumbin tarihi cikin zuri'arsu. Kallo daya Yayan yayi musu, suka fice cikin murmushi da susar keya (It's a show that they don’t want to miss). TAKORI.
Muka yiwa juna kirr da ido, kamar kowanne so yake ya karanto adadin kaunarsa cikin idanun dan uwansa. Abubuwa da yawa sun faru cikin rayuwarmu wadanda duka marasa dadi ne, kowanne kuma yana 'blaming' dan uwansa da shi ne SANADI. Amma a yau mun yarda mun amince haka rayuwarmu ta zo a rubuce babu wanda shi ne SANADI. Mu din da rayuwarmu gaba daya kamar wani rubutaccen KUNDI ne wato LITTAFI mai dadin karantawa da koyarda darussa da dama. MUhimmi shi ne na 'YAN ADAM MU DAUKI RAYUWA DA SAUKI BAMU SAN INDA KADDARA ZATA KAIMU BA. ZA KA KI ABU, BAYAN WATA KILA ABIN NAN ALKHAIRI NE A GAREKA, ZAKA JARABTU DA SON ABU, ALHALIN SHARRI NE A GAREKA. DON HAKA NE IN ZAMU YI SO KO KI MU YI SU SAISA-SAISA. MAFI A'ALA SHI NE MU BAIWA UBANGIJINMU ZHABI A DUKKAN AL'AMURANMU NA DUNIYA BA WANDA MUKE SO KO MUKA JARABTU DA KIN SA BA!!!
Ubangijin da ya halicce mu shi ya halicci SO ya kuma halicci ki ya sanya su a zukatan bayinsa. Kamar yadda ya halicci komai mace da namiji (feminine and masculine) ya kuma ya halicci komai da kishiyarsa (opposite) dukkansu kuma halittar Allah ne da babu dan Adam da ya isa yayi yadda yaga dama dasu face UBANGIJIN da ya halicce su.
Mu karbi rayuwa a duk yadda ta zo, mu kasance cikin GODIYAR UBANGIJI.