Sashe 28
Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
da Allah baki shiga dakina ba?" "Na shiga mana, amma ban bincika komai ba wallahi, gyarawa kawai nayi". Ya miko min hannun shi na dama na alamar karbar abu. "Bani DIARY dina!'. Na kai tafukana na rufe fuskata cikin matsananciyar kunya. "Koda na gani, ba lallai ne ya zamo na karanta ba. Kuma ma ai duk rabi Larabci ne ba iyawa nayi ba". Ya girgiza kai, "Fa'eezah! Kin dauka ban san cewa tun kina 'yar ficikar ki kike yara Larabci ba? Kin zaci ban san cewa (B.A Arabic) kike karantawa a BUK ba???" Baki na saki galala! Ina kallonsa. "Rufe bakin kada kuda ya fada". Dariya nayi na juya masa keya. "Duk wani motsi na rayuwarki nasan dashi, haka duk wani abu da kike aiwatarwa a kan wadannan fitinannun idanun ne, ko ba haka kuke cewa ba keda 'yan uwanki Ummi da Zaneerah?" "To mai yasa kake sa min idon? Ko kasan sa min idon da kake yana daga cikin abubuwan da suka sa na ki jininka a lokacin? Ina ganin kana sa min ido ne domin ka kuntaci rayuwata". "Kina so ki ji dalili?" "Eh". "To amsa min tambayata, ta shin kin karanta min DIARY bada izinina ba ko?" "Eh, na karanta, shi kenan? Amma wallahi ba bincike nayi don na samo shi ba, tuntube nayi dashi a dokin kofa". Murmushi yayi, "...Fa'izah matar Fa'iz! Insha Allahu jirgi ba zai zamo ajalina ba sai SON FA'IZAH!". Na dago cikin (slow) na dube shi, kwayan idanunmu suka hadu, suka sarke da juna. Babu komai cikin kwayar idanunshi sai 'gesture' wato motsi mai nuna zahirin abinda ke zuciya. Tsigar jikina ya tashi yarrr! Jikina yayi bala'in sanyi, ban san yaushe kalaman ke fitowa a hankali daga baki na ba. "Balle ma in Allah Ya yarda tare zamu mutu, tare za'a binnemu, kuma ba ta hadarin jirgi ba. Tukin-jirgi, hanyar abincin mu kenan ba hanyar ajalinmu ba, yanzu muka fara tukashi muna saukewa daga kuruciya har tsufa, ranar da ba zamu iya ba 'ya'yanmu su karba, haka har jikoki". Ni kadai nasan abinda naji... da na tsammaci mutuwarka! Da ka mutu a wannan lokacin Yaya Fa'iz I'll no longer be in existence. Na tabbata in 'so' bai kasheni ba kewa da 'kauna' za su kasheni...' Wata irin runguma Fa'eez yayi min da saida kasusuwana suka amsa. Hawayen dake makale tun dazu suka balle mini suka shiga shan sharafinsu a kundukukina zuwa gadon bayan sa. Ya kai hannu ya shafo hawayen, "Daina zubar dasu haka nan Fa'izah. Na tabbata ba ni ne baki so ba HALINA NE. Wanda a zahiri ba halina bane KISHI NE. Ba ke nake sanyawa ido ba, SOYAYYAR DA KIKE YIWA YAYA ALIYU NE! Ina kishin Aliyu Fa'izah, yadda bakya zato, har gobe ba zan daina ba. Domin wani mutum ne shi da kika so da zuciya daya saboda HALINSA! Na yarda na amince halin mutum jarinsa ne daga yau nima na zama dan kirki, dama ke kadai nakewa rashin kirkin, kema kuma don kina son ALI NA'IBI ne! Tunda kin maido son gareni na miki alkawarin zama mai kirki fiye da Yayanki ALIYU HAIDAR NA'IB A.B GIWA!" Na dago kaina ido sharkaf da hawaye. "Ko baka canza ba INA SON KA HAKA! I go along with the people I love da halinsu...". Dariya yayi, "Da can dinma bakya ki na, bacin ranki kike expressing' na bakanta miki da nayi. Da kina ki na da kinbi shawarar dana baki a RIVER NIGER". Na dunkule hannu na bugi kirjinshi da shi. "Kai ne baka iya kishin ba ai, kishi na mugunta?" Na sake bugunshi, "Ba'a nuna KISHI da KIYAYYAH... Ga wanda aka yimawa KIYAYYAH NE. Ka daina kishi da Yaya Aliyu don Allah, dan uwanka ne, kuma surukinka. Na so yaya Aliyu, kasancewar shi wani mutum da ya wahalta mini, da gangar jikinsa, da zuciyarsa, da aljihunsa da lokacin shi a kaina. Ya shiga kunci a lokacin da ya rasa ni. Kai da ka samu bai yi kishinka ba ya bada kyakkyawar gudunmawa wurin ganin na hakura na rungumi aurenka Yaya Fa'iz. Aliyu ne ya sani yin zuciyar da na tsaya nayi karatu na shiga sahun dalibai nagartattu a lokacin da nake cikin shagaltattu. Don me ba zan so shi ba a wancan lokacin tunda an halicci zuciya ne da soyayyar mai kyautata mata? Ina son shi ne a lokacin, amma wani irin so irin wanda nake yiwa BABA NA ban taba kimsawa zuciyata sha'awar tarayya a tare dashi ba sai so na 'KAUNA' da mutuntawa hadi da ganin kimar juna. Amma wannan son da nake ji a yanzu akan Hafizin Hajjah? Wani iri ne da harshe ba zai iya bayyanawa ba, kwakwalwa ba zata iya fassarawa ba, da ya gagari fahimtar mutum sai dai zuciya ta jishi amma ba zata iya bayyanawa ba. Haka nan zuciya da kwakwalwa basa iya daukar shi ba tare da sun nuna gazawa ba saboda GIRMANSA! Daban yake dana YAYA ALIYU kazalika NAZIR SANI GALADANCI. A kansu duka, banji irin wannan lullubabben son da nake yiwa FA'EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA BA!!!". "Barni haka... kada ki kasheni da raina". "Ya fadi ne a galabaice, cikin tsananta rungumar da yayi min. "Allah Ya bani tsawon ran da zan ninka farantawar da Aliyu yayi miki, Allah Ya bani tsawon ran da zan nuna miki bakiyi asarar Yaya Aliyu ba! Nayi alkawari Fa'izah zan nuna miki so da kulawa fiye dana Yaya Aliyu. Ko da can din ban samu dama bane, babu kuma hanyar da zan samu damar. Sai dai kisa a ranki, na rantse ALIYU BAI FINI SONKI BA... DAMA YA FINI SAMU!" Ni kadai nasan halin rudun da na shiga a lokacin da kike neman hallaka kanki don kiyayyata, sai ko abokina Maajid. Kada ki kara sawa a ranki wai bana son ki. Kisa a ranki Fa'eez naki ne KE KADAI". Shudewar mintuna masu tsayi cikin wasu al'amura masu tsayawa a rai, da zuciyar wanda ake mawa. Na nemi ji na da ganina na wucin gadi na rasa. Fa'eez ya daukeni ya kai wata duniya ta daban irin ta Adamu da Hauwa'u da ma'aurata kadai ke zuwa kwatankwacinta. Ya manta da yunwar cikinsa na manta da tawa, da kyar muka rarrafa zuwa cikin gidanmu muka dangana ga dakin baccinmu. A can komai ya kwance, al'amuran suka sauya taku, baga Fa'iz ba, ba ga Fa'izar ba, kowanne so yake ya nunawa dan uwansa ya fishi so da kaunar kansa. Ina rokon Allah Ya tsawaita rayuwarmu, Ya kara soyayyar junanmu cikin zukatanmu, ya bamu 'ya'ya masu albarka da biyayya ga iyaye. Bana burin in haifi da mai irin halina na kafiya, riko da taurin zuciya. Addu'a nake, Allah Ya bani Da ko 'YA mai hali irin na Ubansa/ubanta, mai yakanah irin ta Ubana da Baban Kaduna, mai son zumunci da kyautatashi irin HAJJAH. Mai tsaftattar zuciya irin ta MOMI na ma'abociyar rungumar kaddarorin UBANGIJI. (Ku ce Ameen, makarantan TAKORI).