← Book details Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 31

Sashe 16

Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 10 min read

BAYAN TAFIYAR FA'IZ
Wani ikon Allah ko abin mamaki tun tafiyar Fa'iz sai naji sam bana jin dadin gidan. Kewa da kadaici suka yi min sallama. Da yana nan, ko banyi masa magana ba shi zai mani, zanji motsin dan Adam cikin gidan ta hanyar karakainarsa, a falo da (kitchen) da nasa dakin. Amma yanzu gidan ya zame min kamar makabarta ko motsin kyankyaso babu.
Kusan kullum ina baya wajen Dawisu ina jefa musu abinci, har kujera nake kafawa in zauna. Yanzu har sun saba dani har kofar falo suke biyoni in na haura lokacin da nake fitowa basu abinci. Sai suzo kofar falo su tsaya su bude bindinansu abin ban sha'awa suna juya su gabas da yamma, kudu da arewa cikin nuna baiwar kyan da Ubangiji Ya yi musu da bai yiwa wani tsuntsu a duniya ba.
Yaran gidanmu duka an hana su zuwar mana dagani har Ummi. Haka 'yan uwa ba mai zuwa don kamar yadda na fada a baya sunce sai ranar da suka ganni da ciki irin na Ummi ko 'ya'ya irin na Zaneerah. (In fact) ina kewar Fa'iz duk da bana so na yardarwa zuciyata cewa kewar tasa nake yi.
Duk da bamu dade tare ba, sati biyu kacal muka yi tare, abubuwan dake cikin sati biyun masu yawa ne (it seems like a journey of two year full of blissful adventures) da suka kasa goguwa a zuciya da kwakwalwata. Fadansa na bani dariya, haka kishinsa na babu gaira babu dalili.
In ka debe wadannan na fahimci wasu abubuwa wadanda ada ban sani ba, wato Fa'izu Abubakar, mutum ne mai saukin kai, barkwanci, dadin mu'amala da dadin zama amma fa ga wanda yake so kadai, shi yasa iyaye da dangi duka kowa ke sonsa. Idan baya yi da kai ko ya tsaneka zaka dauka ne cewa babu wanda ya kaishi rashin kirki da rashin dadin mu'amala a duniya.
Hakazalika yawan kiran sunana da yake yi cikin gidan Fa'izah-Fa'izah-Fa'izah kai kace shi ya rada min suna Fa'izah ko Aunty Fa'izah.
(I also missed his regular sayings) "O.K?" Wannan ban san me take nufi ba har ya zamanto nima ta zauna min a baki ko magana na yiwa Ya'u na gama sai na ce "o.k?"
A da kam nasan ba haka Fa'iz yake ba sam, magana ma wuya take masa balle mu'amala da mutane, ban san sanda bakinshi ya bude ba domin ada sai ya wuni baiyi magana ba.
Ina kewar Fa'iz ne a bisa dalilai da yawa dani kaina ban san adadinsu ba, ko ba komai ina jin motsinsa cikin gidan da maganganunshi ko a waya ne nasan dai ba ni kadai bace cikin gidan. To amma ya tafi, ya bar min kangon gidan da abin da ke cikinsa, gidan yayi shiru, yayi tsit sam babu dadi kamar babu mahalukin dake rayuwa a cikinsa.
Ina kwance tsakiyar kafet din falona na tada kai da filon kujera kwanaki uku da tafiyar Fa'iz, aka danna kararrawar son shigowa fallon. Daga nan inda nake kwance nake tambaya,
"Waye?"
"Ni ne Shu'aib".
Na bude ina dariya, "Yaya Shu'aib kaida wa?" Shima dariyar yake yi, ya shigo na bashi hanya ya wuce ya zauna a kujera muka soma gaisawa. Sannan ya ce.
"Yaya Fa'iz ya turo ni inzo in karbi ATM dinki in amso miki kudi a bankin UBA ko kina da bukatarsu, in kuma hada miki (tablet) dinki in sanya miki 'Interner data' in dora ki akan 'social networks' akwai 'group' na A.B family a (whatsapp) kowa yana ciki ki dinga hira da 'yan uwa madadin kiyi ta zama shiru".
Ban yi musu ba na mike na dauko masa 'Samsung tablet' din na kawo mishi ko ni zanso hakan. Amma jaganar karbo kudin a UBA na ce.
"Shu'aib bar kudin nan a muhallinsu, me zanyi dasu? Bana bukatar komi sai abinci gashi nan dankare nau'i-nau'i a 'store' da 'freezers, ga Ya'u na kawo katin waya. (I need nothing)".
Ya gyada kai cikin gamsuwa, hannunshi da idanunshi akan tablet din yana ta shiga 'applications' muna ci gaba da hirar mutanen gida da na Giwa.
Na mike na kawo masa lafiyayyen 'yoghurt' din 'L&Z Dairies' dake cike da (fridge) dina da sabon cup-cake din da nayi jiya.
Na ce, "Shu'aib, ina Hajjaty?" Sai bayan da na fada ne kunyar kaina da nadama suka zo suka rufe ni, muryata ma a lokacin tayi kasa sosai.
Dariya yayi, "Hajjah tana nan lafiya ko jiya na je Giwa sun tafi Umrah ita da Baba Na'ibi".
Ya cigaba da shan L&Z Dairy yana lumshe ido saboda gardin madarar ya aje gorar, ya ce.
"Wai kuwa don Allah Aunty Fa'iza yaya kike yi Yaya Fa'iz yayi miki magana?"
Shu'aib kusan sa'a na ne domin bai fi shekaru biyu ya bani ba, tsakaninsa da Fa'iz kuwa shekaru bakwai ne , mukan tattauna matsalolinmu da junanmu tun sanda muka fara hankali.
Nayi murmushi na ce, "Kamar Yaya Shu'aib?"
Ya ce, "Yo mutum ba fara'a kullum fuska kamar bindinga, babu alamar rahama sai muzurai. Duk inda yara suke ya tashe su. Shi ne nake mamakin yadda zai zauna da iyali yayi mu'amala ta dadin rai dasu. Don na tabbata in ba mace mai tsantsar hakuri ba, babu wadda zata iya daukar ginshirar Yaya Fa'iz ...".
Dariya nayi, "Baka da dama Shu'aib! Ni dai toh!! Ba zan ce baya magana ba, amma yafi yi a waya da abokansa!!!:.
Na jawo wata hirar don hirar Fa'iz da yake sani ya na sanyani cikin wani hali, da ni kaina ban san shi ba. Ban san irin shi ba, mai wuyar fassarawa ne.
Har la'asar muna tare da Shu'aib bayan ya hada min 'Whatsapp, wattpad, Facebook, Twitter da Instagram. Sannan ya zuba min duka numbobin 'yan uwa, muka yi sallama na juye duka 'cup cake' dinnan nace ya kaiwa Mama. A ranar na soma (chatting) dasu Ummi nima da (family group) dinmu ta watsapp.
Sati biyu bayan nan Mama ta sake aiko Yahya ya kawo min wasu jarkoki cike da magani mai zaki wai Mama ta ce in sanya a (fridge) in maida su ruwa sha na (tsumi). Da zuma iri-iri 'yan asali da abubuwa dai daban-daban wani ta ce asha da nono,. wani da peak-milk. Zuciyata tayi ta raya min meye nufin Mama na bani wadannan magunguna? Amma da nayi tunani mai zurfi Mama dai uwata ce wadda ba aurena da Fa'iz ne ya hadamu ba.
Mama uwata ce ta tun fil'azal ba zata bani abinda zai cutar dani ba, sai na dukufa shansu dare da rana yadda tayi 'prescribing' kowanne a rubuce a 'yar takarda har suka kare.
Satin ya kare ta sake aiko da wasu, haka muka yi tayi har watanni biyu.
Rannan a (chatting) nake tambayar Ummi ko tasan magungunan mene ne mama ke dirka min? Ta ce in fasalta mata su. Na fasalta har 'prescription' dinsu. Tayi alamar dariya ta hanyar turo 'emotions' na dariya ta ce.
"Mama nayi mana gatan da Hajjah, Aunty Hawwa da MOmin ABU suke kunyar yi amna. Ke dai kiyi ta sha Fa'izah ba zai cuce ki ba. Nima nan haka take aiko min dasu jarka-jarka kulli-kulli. Kiyi godiya kawai ga Allah da yayi mana baiwar uwar mazaje tagari mai kaunarmu tsakani da Allah.
Daga nan Mama ta koma aiko turaruku iri-iri 'yan Borno. Ni kam karba kawai nake ina faman turara daki. Amma sai Mama tayo waya ta ce.
"Fa'izah! Turarukan dana aiko miki fa ba na turara daki bane, jikinki zaki ke turarawa, kullum da yamma bayan kin fito wanka. Akwai abin turaren wuta na lantarki (burner) cikin lokas din (kitchen) dinki ki dauka kiyi amfani da ita, nasan hankalin ki bai kai wurin ba".
Na ce, "Akwai wata dana samu ne a falo da ita nake amfani, insha-Allah zanyi yadda kika ce. Mama Allah Ya kara girma".
Murmushi tayi ta aje wayar.
Tunda nayi nisa a sha da amfani da magungunan da Mama ke aikowa, sai na soma samun wani irin sauyi a jiki da zuciyata. Na nemi kiyayyar da nake yiwa Fa'iz na rasa tana (decreasing gradually) a kullum. Sai wani irin bege da son ganinsa. Da tsananin son kebewa dashi da son jin koda muryarsa ne amma babu. Tunda ya tafi ko sau daya bai kira ni ba har na soma zargin anya ba asiri Mama ke yi min ba, inso danta in kaunace shi? Nayi saurin kawar da wannan tunanin tare da yin istigfari a zuciyata.
[1/4, 12:23 am] Takori: ***
Na wayi gari ne yau cikin matsanancin nishadi, irin wanda ban taba tsintar kaina a ciki ba. Don haka na share ko'ina na goge lungu-lungu da sako-sako na gidan ya zama tas, sai sheki yake kamar lomarka zata fadi ka sanya baki ka side, duk da gidan ba wani datti yayi ba, don akai-akai nake kula da tsaftarsa. Na samu kaina da son shiga dakin Fa'iz, ko na rage kewar sa data addabe ni. A hankali na murda kofar na shiga dakin ga mamakina a bude ya barshi, sallama dauke a baki na.
Fa'eez ya kawata dakin baccinshi da duk wani nau'in kayan jin dadin rayuwa. Duk da A/c a kashe yake, amma dakin da sanyinsa, wanda ya hadu ya cakude da sassanyan kamshin '212'n da Fa'eez ke amfani dashi (on a regular basis). Babu komi dake cikin dakin da aka saye shi cikin Kadunan, bayan gidan Fa'iz kadai abin kallo ne, wanda bai cika girma ba. Banda katifar ruwa data mamaye gadon shi, karamin 'frame' din dake aje dai-dai santar inda yake sanya kanshi guda biyu kanana su suka dauki hankali na.
Sannu a hankali nake takawa zuwa garesu, yayin da kafata ke nitsewa cikin (center-carpet) mai tsananin taushi dake gaban gadonsa. Wanda ya sha bamban da sauran carpet din dake cikin gidan baki daya.
A hankali na russuna na dauki 'frame' din. Wani dadadden hoto na ne mai rungume da (teddy bear) wanda da alama ya kaiwa gwanaye ne sun wanke shi sun adana a cikin 'frame' din ya zama kamar daukar jiya-jiya. A kusa dashi wani hoton nawa ne cikin (swiss-lace) da goggoro, wato ranar partyn 'Indoor-sport hall' na nan Kaduna. Na tsuke giran sama da ta kasa wanda hakan ba karamin kyau ya kara min ba tamkar anyi shi ne 'in-style' ba bacin rai ba.
Na tambayi kaina wannan shi ne 'SO' kenan? Wanda ni bana jin shi? Don ko cikin wayata ba zan iya ajiye hoton Fa'iz ba balle a dakin barci na, inda nake ta da kai da mayarwa, a yayin kwanciya da tashi daga barci.
To me ya hana inso Fa'eez? Babu! Illa shi SO din abu ne wanda ke yin kansa, ko ince yin Allah ne, ko kuma wani hali na mutum ko wasu (personal-attributes) kan zamo sila na samuwarsa, and Fa'iz 'lack any loving attribute to be loved upon'. Wato bashi da wani hali da za'a so shi don su, sai wani sashe na zuciyata ya ce dani.
"A bisa rashin saninki kenan a da, banda yanzu, da kika fara lakantar ainihin waye FA'EEZ BAMALLI?" (And I came to the conclusion that) ba wani abu ne ya hana ni son Fa'iz ba illa tunanin baya... Inada RIKO, bani da mantuwa, sannan inada gudun wulakanci. Ina son momi na, Ina ganin muddin na sake da Fa'iz nan gaba zai koma min Fa'izun Hajja, wato Fa'izunsa na baya, zai sake sanya ni cikin 'problem' sannan zai sake tsanata...
Na cigaba da kallon dakin tare da komi dake cikinsa ba tare da na bude kowacce ma'adanar kaya ba (locker).
Ba don komi ba sai don nasha jin Hajjah na fadin, "Yiwa miji bincike ba ta'ada ce mai kyau ba, duk mai yiwa mijinta bincike wata rana sai ta binciko abinda zai daga mata hankali, ya hana ta bacci, ya sanyata bakin ciki wanda bata da maganinsa. Watarana sai ta binciko abinda ba alkhairi ba!".
Duk da baya dakin amma kamshinsa 'permanent' ne. Turaren '212' tamkar shi kadai aka yiwa. Komi na Fa'iz kamshinsa ne a jiki hatta takardunsa, bedsheet da labulayen dakin nasa. Na kasa fita a dakin Fa'iz, sakamakon wani shauki (emotion) dake dibana, zan so ace a lokacin yana cikin dakin ne ko yana falo yana kwala min kira in kawo masa kaza da 'chips' dinsa.
Shaukin dake dibana ne ya debe ni ya kwantar a gadon Fa'iz, ya janyo tattausan bargonsa ya lullube ni dashi. Da filon shi na tada kai na lumshe ido ina cigaba da shakar daddadan kamshin na '212' (men). Na soma zargin kaina da son Fa'iz a karo na farko. Wadannan (emotions) din (are for real!) YAA SATTAR!!! Ya Sattaru, idan mafarki nake ina rokon ka da ka farkar dani. Na bude dukkan idanuna dake lumshe, da karfi nayi wurgi da filon na zauna dabas a tsakiyar gadon ina wurga ido kamar mara gaskiya.
Eh, mara gaskiya ce (in fact!) Domin son karyata 'emotions' din nawa nake da gangan suna fin karfina. Na sakko daga gadon cikin barin-jiki, amma ga mamakina na kasa fita a dakin Fa'iz! Ina son dakin!! Ina son nayi bacci a dakin ko na samu nutsuwa.
Na koma na kwanta cikin mutuwar jiki da zuciya, naja bargo na rufe har kaina. Bacci mai karfi ya fisgeni.
Chapter 16 · 0% Book details