Sashe 3
Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ummi da angonta Yaya Bashir suna cikin (kitchen) suna hadin (burger) da suke so su ci. Da ya fito sashen Mama a bakin kofa suka yi karo da Shu'aib ya tambaye shi kwatancen gidan Yaya Bashir. Ya ce, "Yaya Fa'iz muje mana in raka ka, nan ne Kabala Custain ba nisa". Ya ce, "Amma da kanka za ka dawo? Don ni daga can ba gida zan dawo ba". Shu'aib ya daga mishi kai suka jera suka fito suka shiga motar Baba, Fa'iz ya ja motar a hankali suka fita daga gate din gidan nasu. Ummi ce ta fara hango shi ta tagar (kitchen) din wadda ke santar harabar adana motar su. Tayi ihu harda dan tsalle ta ce. "Ya Fa'iz in town". Suka fito da sauri ita da Bashir suka game dashi a main falonsu. Daga matar har mijin bakin su yaki rufo sai jera masa sannu da zuwa da yaya hanya suke yi yana amsawa da ka, yana dan yatsine fuska. Ya bi daya daga cikin lafiyayyun kujerun falon ya nitse. Takaici ko kishin yadda yaga Ummi da Bashir ne suna rayuwarsu babu abinda ya dame su duk sunyi haske sunyi kiba, koko tunanin tashi 'yar bala'in amaryar ne yasa shi yatsine fuska oho! Da irin tarbar da shi zata masa? Allah kadai Yasan ZUCIYAR MUTUM (sunan wani littafin TAKORI). Suka zauna kusa da shi suna manne da juna. Ya dube su sai ya saki fuska. "Mr. and Mrs.". Suka hada baki wurin cewa, "Allah Ya taimaki angon Fa'izah!". Ummi har da jinjina da hannunta. Bashir dariyar shegantaka yake mishi ganin yadda ya zabge amma ba zai fasa halinsa na rainawa mutane wayau ba da ginshirar babu gaira babu dalili ya ce. "Shin Pilot Giwa yayi ciwo ne?" Ya ce, "Lafiyata kalau, me ka gani?" Tare da cin laya kada su kawo mishi shegantakar da ba zai dauka ba, amma sai da Ummi ta ce. "Kaima dai dear! Fa'izah's calamity mana! 'Yar banza Bakin Bunu Bata Baibaya...". Ji yayi kamar shi ta zaga, kuma dai shi baya son a dinga shigar masa rigimarsa da Fa'izah ko ace tayi ba dai-dai ba, zai fi son ka zauna a gaban sa kayi ta yabonta kana bashi labarin rayuwarta fiye da nuna kana taya shi takaicin abinda take yi akansa. Ya share zancen da cewa. "Shin kuna lafiya? Na same ku lafiya?" Bashir ya ce, "Gani ya kori ji". A yayin da yake tuttula mishi (fresh milk) din Peak cikin tambulan din dake hannun Ummi, ta mika mishi ya daga mata hannu. "Barshi, bana tare da yunwa, Mama ta bani abinci na ci". Ummi cikin rashin jin dadi ta ce, "Amma ta yaya zaka shigo gidanmu ka fita ko ruwa baka kurba ba?" Kamar zata fashe da kuka, sai ya mika hannu ya karba ya shanye ya dire kofin bisa (center table). "Na yaba da tsarin gidanku, Allah Ya ba da zaman lafiya. Ni zan wuce". Ya mike. Dan uwa rabin jiki, Yaya Bashir sai yaji tausayin Fa'iz ya kama shi duk da basu cika shiri ba ya gano damuwar dake tare dashi da halin da ya shiga ganin irin rayuwar da suke yi shi da Ummi suka mike suka fito tare da shi. Bashir ya ce, "Wai ina Fa'izar ne?" Ba tare da ya juyo ba, kamar yadda bai fasa tafiya ba ya ce. "Tana nan". Ummi da Bashir suka hada ido suka yi murmuishi, shi kuma ya sake hade rai da fuska har da tsuke baki kada su kara tambayarsa game da Fa'izah, kowa yayi (minding business) dinsa. Ita kuma Ummi bata fahimci hakan ba, sai ta ce. "Don Allah ka kawo min ita mu wuni yaya Fa'iz, na matsu in ganta, nayi-nayi tayi hakuri ta ki saurarona...". Sai kawai ya samu bakinsa da furta, "Me kika yi mata?" Alhali bai yi niyyar yin furucin ba. Ummi ta ce, "Matsalar mu ce, amma ka tambaye ta mana, ai kunfi kusa". Sai yaji kamar shaguben da yake gudu suka yi masa. Ita kuwa Ummi tsakaninta da Allah ta fada, ta kara da cewa. "Sai yaushe za ku tare mu zo rakiya?" Ji yayi kamar Ummi ta zage shi, ya ce. "Ummi, ina wasa dake? To babu rana babu wata!". Dai-dai sanda suka kawo inda ya yi (parking), Shu'aib na zaune bencin megadi suna hira yana jiransa. Ya bude boot din motar yasa Shu'aib ya fitar musu da tsarabar da ya kawo musu. Electronics ne na amfanin (kitchen) cikin kwalayen su guda biyar samfurin 'Binatone' microwave, juicer, mixer da 'rice boiler' sai 'blander masu karshen (quality). Shu'aib ya shigar musu da su gida ya dawo suka shiga motar suka tafi, Ummi da Bashir na godiya suna daga musu hannu har suka fice daga harabar gidansu suka hau titi. Yana tukin ya dan juyo ya dubi Shu'aib ya ce. "Yo kai in haka ne ai zaka yi min amfani wajen sauke kaya, shige muje Zaria kawai". [1/4, 12:22 am] Takori: *** Ban tashi kaduwa da al'amarin Fa'iz ba sai da na ganni cikin jihar Niger (Minna). Ya samu gefen wani titi yayi (parking) ya doshi wasu masu kirar wukake da ludaya na garin Minna ya yi cinikin wata sharbebiyar wuka gayawa jini na wuce, irin ta yankan shanu, suka yi 'yar magana da makerin, sai naga an fara rubutu a jikin wukar. Ya kunso wukarshi cikin takarda ya biya kudi ya shigo ya ajeta a gefenshi ya kunna mota. A raina na ce. "Eh, gara kayi min yankan rago ya fiye mini da hada rayuwa da kai. Mugu, azzalumi, munafiki, mara imani. Ko kuma kayi min yankan kifi gunduwa-gunduwa zai fiye min kwanciyar hankali fiye da in karashe rayuwata matsayin matar Fa'iz Bamalli Giwa. Uhh! Daga wurin masu wuka kun san ina Fa'iz ya dosa? Fa'iz shahararren kogin Nigeria da nake ji cikin tarihi da 'Geography' sanda nake sakandire, wato 'RIVER NIGER' ya nufa damu wanda an tabbatar yanki ne daga kogin Nilu (Nile). Can ya dosa damu gadan-gadan ya zagaye masu kamun kifi zuwa can inda babu mutane ko daya. Ya danna wani madanni jikin motar glassai bakake suka maye gurbin farare (tinc) suka rufemu ruf. Ya kwantar da kujerarshi baya sosai ya bita ya kwanta yayi matashi da hannayensa ya yi 'facing' dina (fuskantata) sai kuma ya yunkuro ya taso ya dauko wukar nan ya cireta daga cikin takardarta tana walwali da walkiya. Duk da abinda na ce a baya na gara min ya kashe nin, yayi min yankan rago ko na kifi gunduwa-gunduwa amma a wannan lokacin da matuwar ta iso muraran sai na samu kaina da matsawa gefe na soma marmasa kalmar shahada tare da duk irin addu'ar da tazo bakina. Walwali take da walkiya inba za'a ce idona bane yake min gizo da sai ince har huci wukar take yi. Sunan Allah nake kira a halshena da zuciyata, idanuna sun kankance sunyi wuri-wuri, amma babu hawaye a cikinsu sai firgita da razana. Na tabbata yanzu Fa'iz ya fini hauka, na dubi rubutun da aka yiwa wukar a sace, "FA'EEZAH". Na fiddo ido kuru-kuru na sake makurewa jikin kofa. Fa'iz ya cillo mini wuka akan cinyata ya tube riga baki daya, har singiletin jikinsa itama ya cire yayi kira da kakkausar murya. "Fa'izah!". Subhanallahi-subhanallahi, Hasbunallahu wani'imal wakeel kawai na shiga furtawa, na runtse idanuna. Ban taba ganin namiji a tube ba balle kato mai girma irin Fa'iz, yayinda haiba da kwarjini na Fa'iz Giwa yayi min lullubi, ya kara fuskantata ya ce. "Dauki wukar nan ki caka mini ko ki yanka ni karewar kiyayya kenan, ko kya huce bakin cikin zamowa na miji a gareki, ko kya yafe laifin da kike ikirarin na miki, wanda kika kasa yafewa! Kika kuma ki saurarona inyi miki bayaninsa. Idan kika yi hakan na tabbata zaki huce ba karya...". Nayi salati na dire ba tare da na kai karshen sa ba na dauko sabo. Na ture wukar daga cinyata ta fadi kasan kujera, na soma murda murfin motar ko na samu ya bude in san inda dare yayi min amma ko gezau kofa bata yi ba, yasa (lock) ya kulle ta gaba daya. Cikin dakiya da tsare gida ya ce. "Haba Fa'izah, (be brave) mana! Babu wanda zai sani, babu wanda zai ganki. Na tabbata in kin yankani zaki huce kiyi rayuwa mai dadi da nagarta. Ki samu rangwamen kullaci na dake zuciyarki na zagin Momi, mugunta da azabar dana kwashe shekaru ina yi miki, takardar saki dana hanaki, tare da huta auren direban tasha tunda ni dai hannuna ba zai iya rubuta saki ga Fa'izah ba ko da ace na iya rubutu!!!". Idona rufe na ce, "Fa'iz ka bude min kofa in fita, naga alama ka haukace. Wallahi ba don komai na yarda na sanyo kafata a motar ka ba sai don furucin Babana, na yafeni da ya ce zai yi". Na fashe da kuka. Ya sake matsowa ya dauki wukar dana yasar, ya ce cikin taushin murya. "Fa'izah, ki kwantar da hankalinki ki yanka ni, kinga in ba hakan kika yi ba baki huce haushi na ba, baki kuma ci nasarar kiyayyarki ba. Kamar yadda bakin cikina ba zai kyale zuciyarki ta samu sassauci ba don kuwa ni ba sakinki zanyi ba...". A yayin da ya zura min kotar wukar cikin hannuna, nayi maza na yi baya da hannuna na kwalla kara tun karfina. Ihun da ake kira kunu a makota babu wanda yasan ina yi. Ihu nake ina karawa ko Allah Zai kawo wani giftawa yaji ya kawo min dauki. Sai dai ga dukkan alamu ihu na ya tsaya ne cikin motar kadai ko ta taga baya fita. Ya ce (in subdued) wato cikin raunin murya. "Ki yiwa Allah ki aikata abinda na umarce ki, sai ki jani ki tura cikin kogin nan. Babu wanda zai ganki, wukar ma ki jefata cikin ruwan. In yaso ki samu wani ki roke shi ga kudi zan bar miki ya tuka ki zuwa Kaduna ko Giwa tunda baban ABU yasan tare muka fita...". Na girgiza kai da sauri, "Ko da nake kinka babu yadda za'ayi in kashe ka da hannuna tunda ba ni nayi maka ran ba. Sai dai na kasance cikin addu'ar Allah Ya kashe ka in huta wannan bala'i". Wannan karon murmushi ya yi, sannan ya cira ido a hankali ya