← Book details Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 31

Sashe 23

Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*** Muna (kitchen), abinda zamu karya kumallo dashi muka fara hadawa, sai dai nasan ko naman Dawisu na ne na gidan nan yau aka soya, aka farfesa min ba zan iya ci ba, farin cikin da nake ciki, doki da kuzarin da har yayi min yawa ba zasu barni in iya kai komai baki na ba, bayan ruwan lipton, shima don ya warware min hanji, ba don ina da 'appetite' akanshi ba. Kausar dake firar dankali ta ce, "UHm! Yaya Fa'izah in miki wani tsegumi mana?" Walida ta sanya bawon kwai da ta fasa cikin 'dustbin' ta ce. "Uwar tsegumi, yau kuma gulmar wa za'ayi?" Kausar tayi dariya, "Ba na kowa bane, naki ne. Don ni bana gulmar mutum sai dai in fadi akan idonshi don nasan illar yi da mutum". Cikin matsanancin nishadi nake wanda har baya kwatantuwa, don haka dariya suka bani. "Ina jinki Kausar, me ya faru?" Ta dubi Walida tana dariya alamar akanta zata yi maganar kuma Walidar bata sonta. Ta ce, "Kwanaki ko? Na ji Baban Kaduna yana gayawa Baban ABU a dakin Hajjah, an yiwa Yaya Walida miji". Duka Walida ta kai mata nayi hanzarin boyeta na riketa. "Wallahi ba zaki dake ta ba, ai ba ke take baiwa labarin ba ni take baiwa. In ba zaki iya ji ba ga hanya ki fita. Ina jinki Kausar, wane ne mijin?" Kausar dake tuntsira dariya ta ce, "Ki canka". "In canka Kausar?" "Eh, ki canka". "A cikin A.B ne?" "Eh mana". "Mus'ab?" "Gaba dai". "Abba?" "Can gaba dai". "Sani?" Ta ce, "Saura kiris". Na ce, "Shu'aib?" Tayi dariya, "Wannan ya mata nisa, yafi karfinta". Na harareta na ce, "Badar?" Tayi dariya, "Lallai kin manta magajin Ya Fa'iz wajen ginshira irin na 'ya'yan A.B". Ta fara kular dani, na ce, Ke na baki gari wane ne?" "A nawa zan fada miki?" "Au, sai mun tsadance?" "Eh Mana!". Na ce, "To #500 zan baki cash ba cheque ba". Ta mere baki, "Allah Wallahi yayi kdan". Da yake a zake nake da son jin abinda zata gaya min, na ce. "To #1,000". Murmushi tayi, "Shi kenan sai mun gama aiki". Walida dai na jinmu bata kara tofawa ba sai anan ne tayi tsaki, muka ci gaba da aiki duk na kosa a gama ta gaya min don Kausar miskilar yarinya ce, na san ko na ci gaba da na ci ba gaya min zata yi ba sai sanda ta ga dama". Muka kammala muka baje a kasa kan ledar cin abinci muka fara karyawa, ko ince suka fara don ni abinda na ci din ba wani na azo a gani bane. Ganin Kausar bata da niyyar gaya min har suka gama na kwada mata duka a baya, na ce. "Ke don Allah ki gaya min mana, ko so kike sai jini na ya hau?" Ta tintsire da dariya, ta kai kofi mug bakinta mai cike da kunun farar shinkafa ta kurba ta hadiye, ta ce. "Gaskiya sai naci na koshi Ya Fa'izah". Don haka nayi zuciya na kyaleta. Amma da suka gama ta shiga wata sabgar haushi ya kume ni, na ce (kamar zanyi kuka). "Uhm! Ke nake sauraro fa Kausar". Ta ce, "Kai don Allah Ya Fa'izah, kya bari abincin da naci ya tsirga mini mana". Ta sha toka abinta muna haka wayata tayi kabbara (call tune) din kenan. Na mika hannu zan dau wayar ina fadin. "Ke don Allah kada ki fada min in kina kaunar Annabi, ko ba dade-ko ba jima zanji ne ai". Kamin in dauka Walida dayake tafi kusa da wayar ta daga, ta ce. "Hello Yaya!.." "Eh ta tashi, abinci muke ci ma yanzun". "O.k toh". Ta kashe. Cikin zabura nake tambayarta, "Wane ne?" "Yaya Fa'iz ne. Ya ce in kin gama cin abincin ya sake kira". Kamar in maketa don takaici, muryata kamar ta wadda ta sha duka. "Amma ai kina ganin mun gama ko? Tun dazu muka gama ci fa!". Na karasa cikin karkarwar murya kukan takaicin Walida na neman kubce min ba da niyya ba. Ga idona ya ciko da kwalla. 'Yan banzan yaran nan sai suka kyalkyale da dariya. Karfe goma sha biyu da rabi na rana sai ga Shu'aib, Ya'u ya biyo bayansa niki-niki da kaya, jakunkuna saiti biyu samfurin (Argos). Na mike ina yiwa Shu'aib sannu da zuwa, Ya'u na shigo da jakunkunan falo. Ya zauna yana satar kallon Walida, ita kuma yana shigowa sai naga ta bar falon bata gaishe shi ba kamar yadda Kausar tayi, sai yasa murya yana kiranta amma bata dawo ba. "Ke 'yar kauyen ABU... Ina Yaya Sa'id Na'ibi A.B Giwa?" Cikin mamaki na ce, "Au, dama Yaya Sa'id ne mijin da Kausar ke fadi tun safe take ja min rai ta ki gaya min?" Yayi dariya, "Nima haka naji ana fada, ni na ce a bani an hana ni wai tunda ni na furta ba za'a bani ba. Yaya Sa'idu za'a baiwa, amma ai munga wanda ya furta aka bashi ba tare da an tuna cewa shi ne ya furta din ba, saboda mu ne ba'a so kawai sai Yaya Fa'iz". Murmushi nayi ya kuma matukar bani dariya da maganarsa. Ashe dai ba ni kadai nasan Hajjah tafi son Fa'iz akan kowa ba kowa ma ya ganeta ayi magana ta ce shima yafi kowa sonta, mu bama mata sai dai ta mana, Hafizinta fa? Komai nashi nata ne, komai ya samo ita yake fara tunowa kafin iyayen da suka haife shi. Ban kai karshen zancen-zucin nawa ba Shu'aib na tsinkaya yana fadin. "Ga kayan mijinki nan sun riga shi isowa, yanzu haka daga Airport din Malam Aminu nake, shi sai yamma zai iso wai sai biyar jirginsu zai sauka. Yaya Bashir zai je ya taho dashi ni yanzu haka Giwa zan wuce". "Allah Ya kiyaye hanya Yaya Shu'aibu". Na fada ina shiga (kitchen) don kawo mishi abinda zai ci a hanya ko da ba abinci bane ya samu na motsawa a baki. Ya'u ya shigo da kayyakin cefane har da buhunhunan kayan abinci ya shiga (store) dasu wanda hade yake da (kitchen), sai nama nau'i-nau'i, nasa Kausar ta adana kowanne daban a (freezer). Shu'aib ya mike zai tafi yana godiyar 'snacks' da dambun naman da na zuba masa a leda, ya ce. "Af! KInga ko na manta da sakon Mama a mota, bari inje in dauko". Ya koma ya dauko ya dawo ya miko min. "Ta ce kowanne akwai takarda a cikinsa, yana dauke da yadda za'ayi amfani da shi". Na amsa da hannu bibbiyu ina zabga godiya kamar shi ne Maman. Na ce, "Ka turo min Malam Isah (direban gidan Baban Kaduna) ko ta waya ne zai maida su Walida Zaria anjima". Murmushi Shu'aib yayi, "Ai yayarmu, haka za'a kora su 'so early' don maigidan ya dawo har an gama cin amfaninsu za'ayi (dumping) dinsu?" Na harare shi cikin wasa, "NI ban kore su ba, su suka kori kansu. Tun safe suka hada kaya za su tafi da kyar na samu suka kai yanzu". Shi dai ya fice yana min dariya, ya barni da guntuwar kunyata a katara. Cewa yake. "'Yau Mama zata sha labari idan na dawo daga Giwa, zata yi murna da farin ciki kwatan-kwacin na a zuba ruwa a kasa a sha. Fa'izah, ta sauke tata GINSHIRAR ta Bamalli, saura Pilot Fa'eez Giwa". Na ce, "Lala! Shu'aib ba ma haka da kai kada mu soma, kada kayi min sharri. Su Walida su suka nemi tafiya ni ban kore su ba". Ya ja motarshi kowannenmu cikin matsanancin nishadi marar misali. Ni da Walida muka share ko'ina na gidan nan kal-kal, muka goge, muka kade, musamman (side) din Fa'eez, da kaina na wanke (toilet) din shi na kawata da (toiletries) da turaren bandaki ko ina sai tashin kamshi da (atmosphere) mai dadi. Na canza (bedsheet) din dakin da wani (light-blue) mai hade da (duvet) da Baban Kaduna ya bamu tsarabar Umrah ni, Ummi da Zanirah. Na feshe (bedroom) din da (room-freshner) na 'HARAMAIN'. Na kunna na'urar sanyaya daki duk da sanyin da garin ke dashi, nasan daga 'Europe' zai fito, don haka zai bukaci sanyin. Sannan muka yi sallar azahar muka fada (kitchen). Da taimakon su Walida komai ya tafi dai-dai cikin dan lokaci, munyi faten acca da bushasshen kifi, baked moi-moi, tuwon shinkafa da miyar yakuwa da alayyahu da kabewa da tantakwashi zallah. Sai gashin 'Turkey' wato tolo-tolo. A fannin abin sha munyi coconut and milk shake, carrot drink, sai zobo mai abarba da pinaplple flavour. Dukkansu fresh da na sarrafa da kaina. Na ce a raina, "Yau babu 'chips', babu 'chicken', 'you need change HAFIZIN HAJJAH, as everything around us would completely change. Babu abinda LOKACI baya canzawa. 'With TIME change is possible in everything we do". (Lokaci yana canza komai). Sannan na koma 'snacks', ba tun yau ba, ba tun jiya ba na sha jin Hajjah na ba da umarnin a yiwa Fa'iz (samosa) 'best snacks' dinshi kenan. Don haka shi kadai muka yi, muka adana komai inda ya dace. Walida da Kausar suka gyara min komai suka goge min (kitchen) tas suka wanke duk kayan da muka bata, sannan suka shiga wanka. Karfe hudu Isa direba yazo suka tafi muna cike da kewar juna, sai da Walida tayi hawaye. [1/4, 12:25 am] Takori: Wankan da nake ninkaya ina yi cikin kwami yau (unexpressable) ne. Wani irin wanka (slow-slow) da ban taba yin irinsa a rayuwata ba. Fatar jikina ta wanku har santsi take da silki tamkar mai canza launin fata... "Kazo ga jikin nan FA'EEZ, zan baka abinka, ba na yawon dandi bane naka ne, mallakinka ne, a yau sai yadda kayi dashi... Nayi kuskure Yaya Fa'iz, kuskuren da nayi farin cikin amsar shi tun a duniya na kuma yi dammarar gyara shi tun a duniya kafin Mahalicci ya tambaye ni shi". Karar wayata ne ya katse min sambatun da nake yi, na mika hannu na daga. Mama ce. "Yaya magungunan da na aiko miki dasu dazun Fa'izah? Kin shanye ko?" Cikin jin kunya irin wanda bai taba faruwa tsakaninmu ba, na ce. "A'ah!". "Dalili?" Ta tambaya. "Aiki nake tun safe Mama, su Walida sunce yau Yaya zai dawo". Wata matsananciyar kunya tazo ta lullube ni, na kuma kasa fadin wane yayan? Tunda yayun namu yawa gare su. Tayi murmushi na manyance, "Shi bai
Chapter 23 · 0% Book details