← Book details Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 31

Sashe 12

Zumuntar Kenan Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

juna? Meye na tsayawa kusa da shi haka kusa da kusa a bainar jama'a? Da na ce yazo ya tsaya min cewa nayi kuyi hoto? Shi kuma Ya'u da kullum kike bare baki kina hira dashi da izinin uban waye? Ina ruwanki da duk namijin da na kawo na aje cikin gidan nan da har kike dafa musu abinci? Cewa nayi dake bana basu kudin da zasu ci abinci ko me?" Wani matsanancin haushi da takaici suka taru suka rufe ni, naji in ba rushewa nayi da kuka ba bazan huce wannan cin mutuncin da rainin hankalin na Fa'iz ba. Na kasa cewa komai sai ido dana zuba masa cikin matsanancin haushi. "Ina magana kin zuba min wadannan kwala-kwalan idanun naki, ba zaki amsa ba? Na ce shi kuma Ya'u ina ruwanki da shi har yake gaya min kince masa kaza da kaza? Na kirashi na aje domin baiwa tsintsaye abinci hirar da kike yi da shi ta mece ce? In hirar kike so kiyi dani mana? (Am I not applicable to meaningful talks than him?) Ni baki yi hirar dani ba sai da wani gardin kauye can daban. Ba zai yiwu ba to! Daga yau Ya'u ya bar gidan nan. Shima buzun in kika sake kula shi wallahi tafiya zai yi, ki zauna ke kadai ba zaki kasheni da raina ba... Akwai masu bukatar rayuwata ba don ke kadai aka halicceni ba!!!". Bayan takaici da haushi da buyaginshi ya bani, sai ya dawo bani dariya saboda da iyakacin gaskiyarshi yake wannan hargagin, akwai (gesture) a tare dashi mai nuna abinda yake fadin, haka yake har zuciyarsa. Dariya ta cika min ciki ban san sanda nayi murmushi ba irin murmushin nan na tura haushi da maida kai shashasha domin na rantse da fari na firgita, matukar firgita kuwa. Ko da kwartaye biyar aka kamani yanayin da ya zo min dashi sai haka! Ko ni nace a daukemu hoto da wani Surajo oho! Balle kuma bawan Allah Ya'u. Naga idan na kula shi ma (is a waste of time) don haka da sauri nabi ta gefensa zan fice daga (kitchen) din, sai jin hannuna nayi rike cikin nasa, cikin wani irin riko mai tsauri dana kasa fincikewa kamar ba mutum ne ya rike ni ba. "Ina magana kin maidani dan iska?" Yanayin da yayi maganar muryar kamar ba tasa ba kuma cikin wani irin 'tune' da ban taba jin wani mahaluki yayi magana dashi ba. Abubuwa biyu sautin da yayi amfani dashi din ya haifar a gareni. Faduwar gaba da wani irin bugun zuciya, hannun nasa da jikinsa duka rawa suke yi yana wani irin tsuma. Wani matsanancin tsoro ya shigeni. Na daga kai a hankali na dube shi don tantance ko dai wani ne ya rikide yazo min da suffarsa don ya cutar dani. Daga idon dana zo ina dakacensa, domin kamar jira yake na dago idon yayi hanzarin ya sanya bakinsa cikin nawa ya soma 'kissing' ba ji ba gani kamar wani mahaukacin zaki. "Na tuba Fa'izah, na bi Allah na biki. Kiyi min duk abinda kike ganin in kinyi shi zaki huce bacin-ranki, amma ki barni in rayu dake muddin rayuwata...". Kalaman da yake maimaitawa kenan ba adadi, babu 'comma' ba 'full-stop'. Saura al'amuran da yake kokarin bijiro dasu masu nauyin fada ko misaltawa ne, kuma ban shirya karbarsu ba daga nan har gaban abada. Don haka na tattara karfina da Allah Ya hore min a wannan lokacin wanda ya kasance fiye da nashi na angaje shi na taka da gudu nayi dakina na shige na rufe da 'key' ban kuma yarda na zare key din daga jikin kofar ba har safiyar washegari. Kwana nayi jinyar tsallake rijiya da bayan da nayi jiya wanda ko a mafarki ban kawo shi cikin rayuwar dolen da nake yi da Fa'iz ba. Wanda ya hankaltar dani ga cewa in sauya taku. Hanyar dana dauka ta yin sako-sako ga rayuwar da muke yin bisa tilas ba zata bille dani ba, ba kuma mai billewa bace ba. Idan kuma na ci gaba da binta, la-shakka ina cikin hatsarin da bazan iya maganinsa ba idan ya sameni. Nayi kuka har na gode Allah. Daga baya bacci mai nauyi ya dauke ni. Can cikin barci na naji yana buga kofar ba da karfi ba. Na bude ido na ga hasken rana ya ratso ta labulen taga nayi mamaki matuka, sallar asuba ta kufce min cikin shagala! Ina rokon Allah Ya yafe mini. Na fada (toilet) da sauri nayi alwala, saida nayi sallah sannan na koma nayi wanka. Sannan na shiga (kitchen) don kwana nayi da bakar yunwa. Har kicin din ya biyoni ya tsaya daga kofa yana sanye da kayan wanka na 'versace' da alama fitowarshi kenan daga wanka. Daga inda nake ina iya jiyo kamshin 'bathrobb' din da yayi amfani dashi na 'desire dunhill’. "In kin kammala ki shirya muje Jabi, Area One (Zaria) da Giwa kiyi musu sallama don jibi zamu tafi". Na wani irin juyo nayi masa kallon kayi hauka ka warke, na juya na ci gaba da aikina. Ya girgiza kai ya juya ya kyaleni. Duk yunwar da nake ji sai naji ba zan iya cin abincin ba ma saboda tashin hankali. Amma sai wata zuciyar ta ce bishi kawai kuje wajen Maman, wannan ce kawai mafitarki sai kiyi amfani da damar ta inda bai zata ba. Sai kawai na aje komi na fito na sauya kaya, kwalliya sosai nayi da 'pitch swiss-lace’ mai ratsin baki, na yafa bakin gyale na rufo dakina. A falo na cimmasa yayi nasa shirin cikin riga da wandon shadda getzner dark-green dinkin tazarce kanshi ba hula. Sai 212 ke tashi a falon. Ya hadu ya cakude da 'escada sentiment' da nayi amfani dashi wani sanyin ni'ima ya baibaye dukkanin mu, da ganinmu kasan ango da amarya ne ba karya. Ko kallona baiyi ba yayi waje, na bishi a baya naki rufo falon na shige mota. Ina kallon yadda yayi kwafa, ya fito ya rufe ya dawo, sannan ya tada motar muka fita harabar gidan buzu na daga mana hannu muka nufi gidan Baban Kaduna. Su Yahya dake ball a harabar gidan babu wanda ya taremu da murna ko tsalle kamar yadda suke yi da, tabbacin haushin yayan nasu da abinda yayi musu bai sake su ba. Sun dai yi mana sannu da zuwa suka ci gaba da 'ball' dinsu. Ya kalle su ya gyada kai yayi murmushi bai ce dasu komai ba, muka wuce kai tsaye falon Mama. Mama waya take sanda muka shiga kafarta daya kan daya a hamshakin falonta. Ta daga ido ta dube mu muna shigowa, fara'arta ta karu, ta ce. "Kinga 'yan halak, gasu nan sun zo". Ta miko min wayar tana fadin, "Rabi ce daga Kano". Na karba sannan na zauna a kusa da ita daga gefe na kara a kunena na ce. "Hello Ya Rabi". Kafin in karasa ta fasa min guda aka mai barazanar tarwatsa min dodon kunne. Da sauri na dubi Mama da danta don tsammani nake suma sun jiyo mahaukaciyar gudarta Ya Rabi, sai naga hankalinsu baya kaina sam, gaisawa suke. Yaya Rabi ta ce, "Diyata 'yar albarka, ya aka kare da BOXING? WHO IS THE WINNER?" Nayi tsaki, "Tsiyarki kenan Ya Rabi, ba a maganar arziki dake". [1/4, 12:23 am] Takori: Tayi dariya sosai, "Ni kuwa ake maganar arziki dani, ‘yar Abubakar uwar Abubakar da Fa'izah, uwa ga Zanira uwa ga Ummi, sha lelen Muftahu autar Hajjah. Kirarina kenan, na zama duwawu dole a zauna dani. Tafiya ta tashi ko? Birtaniya ko Murtaniya? Na so ace nazo rakiya Allah bai yi ba, naji tafiyar taku ne ba shiri, a tabbatar in za a dawo da baby aka taho min sai inzo in zauna zaman dabaro mai dalili...". Nayi tsaki na katse wayar don nasan in ta Ya Rabi ne sai mu kwana muna yi bata gaji ba. Ga haushin da take kara kuma mini ta barni inji da wanda nake fama dashi. Mama ta dubemu duka tana murmushi bayan ta karbi wayarta. "Komai lafiya ko?" Tana duban Fa'iz. Ya hade gira ya ce, "Tambayeta mana Mama!". Mama ta ce, "Fa'izah ta ina Fa'iz ya kuskuro ki ko ince yake bata miki?" Na girgiza kai kaina a sunkuye. "Babu Mama". Ta dube shi, "Fa'iz Giwa fa?" Ya ce, "Mama ba sharri ba, tunda dai gatanan a zaune a gabanta zan fada. Da abinda take yi min na kisan mummuke gara min ta bude baki tayi ta zagina kamar da, ko ta ware hannu tayi ta dukana kamar yadda ta faro. Bata yi min magana, bata shiga sabgata, ba ruwanta dani ko rayuwar da nake yi cikin gidan. Bata yi min biyayya sam, ta maida kanta kurma domina". Na dago idanuna da suka yi jawur na ce. "Wallahi Mama ina iyaka yina, ina masa girki duk abinda ya ce dani bana musawa nake masa, to ban san kuma wace irin biyayya yake nufi ba...". Ya katse ni tare fidda ido, "Girkin banza! Mama baya ga girki me take yi min na hakkin maza akan matansu? Fa'izah bata kula ni, bata taba zuwa shimfidata ba, bata gaida ni, ga tsaki da harara kamar wani sa'an wasanta". Maganar ta dan girme mu ni da Mama, amma dukkanin mu sai muka yi kamar bamu ji ta ba. Na kawo wata daban. "Saboda Allah Mama ya yake so nayi? Ya zo ya sani gaba da bala'in wai don me zanke kula Ya'u leburanshi? Bayan a karkashinmu yake, dole ne ko gaisuwa ta hada mu, wai kuma don me zan ke basu abinci bayan ciyarda barori wani abu ne da muka taso muka tarar a gidanmu a matsayin kyakkyawan koyi koda ana basu albashi. Ban kula shi ba sai ya koma wai don me nayi hoto da Surajo ranar Cocktail? Bayan bani na gayyato shi ba, ban kuma je fatin nan don kowa ba sai don kaina ko ku baku san zan je ba. Ban san ma sanda aka dauki hoton ba da abinshi ya zo. Sannan kannena suka zo min zumunci ya kore su, yanzu duk haushina suke ji kamar yadda suka kullaci Ummi. Sannan ya kawo wata magana wai wani tafiya, ko ina oho! Ni kam kiyi masa magana ya fita harkata, babu inda zani gaskiya in har ba so
Chapter 12 · 0% Book details