← Book details Zara Yar Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 13

Sashe 6

Zara Yar Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inda sabo ta saba in basu da lecture ko suna jiran daya anan suke xama tun insun xauna basa shiga sabgar kowa har yakai suna hira da duk wanda ya xo. Yanayin yadda jafar yake nuna kulawarsa akansu dik abinda ya shige musu duhu yana kokarin fitarsu haske yasa suke kiransa yaya baya nuna banbanci yadda yake wasa da dariya da zahra haka yake da zakiyya da zafira baxaka taba cewa ga wadda yake so cikin su zakiyya yake koyama karatu takai ta kawo invasu da lecture xama suke suji karatun da yake mt dan ba karya ya iya koyarwa. Duk irin gorin shegiya da umma ke mt bata taba yadda ita din shegiyar bace dan kullum baba cikin kareta yake shine babanta bata taba yadda ita din ba diyarsa bace ko fasa auranta da ismail ce mt yai mahaifiyarsa ce bataso dan taima danta mata abu daya tasani tai makanta alkawarin cire duk wani namiji aranta da rayuwarta ko waye kai dik yadda kuke kana kawo mta batun soyayya kun bata. Juyi kawai yake yakasa bacci in ya rufe idansama zahra yake gani tana sakar masa tassausan murmushinta akullun ya tunkareta da batun da ke ransa sai yaga tana ms wani kwarjini kullun ji yake santa na karuwa cikin ransa xumbur ya mike daga kwanciyar da yai dan tunawa da yai da hirarsu da mubarak watakilma kana nan kana haukanka ita tanacan tana da wanda takeso kananan tana faman kiranka yaya waikai awayo xakai winning din love dinta sai dai ka ganta da ibin aurenta ina baxai yuwuba ya dauko wayarsa cike da kwarin gwiwa yau xai fada mt ya wuta ma ransa sunanta ya danna kira yanaji ya fara shiga ya gyara xama gami da kara kankame wayarba kunnensa kai kace in bai haka ba baxai jiyo mai take cewa ba. *************** Har kiran ya katse bata daga ba akaro na biyu ya kara gwadawa sai yaji akace tsaki yaga gami da fadawa gado ya shiga tunani karar wayarsa yaji kwanciyar da yai yaji dadinta dan hk baijin xai wani tashi dauka. Yah jafar jiya ka kirani bana kusa naxo da gudu daukan wayar dai ta fadi nakuma biyo kiran kaki dauka ayimun afuwa yai dariya daman ba'a rikeki ba suka sawo wata firar. Mutuncin su xara da jafar mutunci ne mai karfi wanda duk mai hira dasu yasan da wannan mutunci tuni mutuncin nasu ya shafi muhd da zaem dan sun xama abokai duda jafar da zaem basu taba ganin juna ba hakan bai sa sun kasa gaisawa a waya ba. Balle kuma shi mai uban gayyar babu wanda bai san da xaman yan matanba a gidansu musanman xaran. Yau basu da lecture dan haka ta roki malan tanasan xuwa gidansu xaem dan yi week end malan bai hn taba dan inda sabo tun tn karama take xuwa. Akofar gidan dan sahu ya sauketa malan wato kakan xaem yana kofar gidan kamar koyaushe indai yamma tayi anan xaka ganshi yn jan carbi ya ganinta ya washe baki ita m ta saki fuska ta durkusa ta gaidashi kafin tace dan tsoho ana nan ana kwashe ladan to ya ranki so kike in mace ko dan karki auri tsoho ai kai mutuwa ba ynx ba sai mun mace mun barka gadin duniya yai dariya wani rufan asiri da gadin duniya aikai dinne bakasan mutuwa in ba gadin duniya ba mai xakayi ko istiqfar din dakai m ya isa yai dari ai inxan shekara dubu bai isaba baba kenan waya ganka da shekara dubu tab yankwani tasa dariya bata jira amsarsa ba tai ciki bari naje gun daya tsohuwar karta ce in koma ya bita da kallo yana dariya yarasa mai yasa yakesan yarinyar sun saba sosai tun tana karama yake gojen babanta ya bashi ita yaki anman jinta yake kamar su zaem kodan baida jika mace ne oho. Da sallama ta shiga da ladidi sikai ka cibis bayan sun gaisa take tambayarta ina hajiya tn sama ta kada kai tai xamanta anan dan film din mutamin ta ake wato SRK . Au zahra kece kika xo shine bazaki iya karasawa saman mu gaisa ba aikece mutun ya tsufa anman kullun yana sama gani nai ana wannan film din na xauna kalla ah koda naji aike duk inda indiyawa suke kinanan tai dariya Allah ba hk bane samanne baxan iya hawa ba yimun shiru mutum sai san jikin tsiya in baka motsa jikinka ai cutace xata kamaka hh wace cuta sai dai karame da'ace karame ai gwara ace kayi kiba eyye lallai ni da'ace ba karatun lpy kike ba zahra da anga shirme a hakanma mai makon kidinga abinda xai ciyar da lpyr ki gaba kinbar san jiki xai cuce ki kaga su kaka kenan kikga ni xoki hadan kayannan dasu gobe Alhaji xai tafi shago. Duda Alhaji ya tsufa yayansa sun taso sunai ms komai hakan baisa yakashe xuciyarsa ba kullum yn xuwa shago in xaem nanan su tafi tare dan yace jira sai wani ya baka ko roko shike kawo raini . Tunda zaem yazo hutu kullum yn gidan su zahra suna shan fira duk irin abinda umma ke mai bai kulawa. Yauma kan hanyarsu ne na xuwa makaranta dan yace yau xafira ta huta shi xai kaisimu xai kuma xo ya tafi dasu hirarsu suke gwanin sha'awa zahra ce agaba xafira da xakiyya abaya tun kunnowarsu area din akan idan jafar karaf ya dora idanunsa kan xarah dake dariya hankalinsa inyai dubu ya tashi wani kishi ya cika masa rai.. Saida suka dan jima a motar kamar bazasu fitoba sannan zafira da xakiyya suka fito suna dariya ita kuwa zara fafur taki fitowa wai ita ba'anan zafira ke sauketa ba shi kuma yace wlh ba inda xai kara jin ya rantse su xakiyya suka fito fitowa yai yaxago barin da take ya bude gami da dan durkusawa haba kanwis pls ki futo kinga na rantse ta juyar dakai gami da makeshi alamar a'a ya kaikaici idonta yai mt gwalo karaf a idanta aiko tace vaxata fitoba yai saurin durkushewa ya km kunnensa pls kinga na rantse tai dariya daga yau saika daina saurin rantsuwa jafar yana daga nesa vaijin avinda suke fade saidai idanunsa na hango ms drama dun da suke idanunsa suka kada sukai jajur lallai yarinyar nan ta rainashi wato bama ta taba xata santa yake ba kenan ita tanacan da wani yi hakuri yar kanwata ki sauko xan saya miki ice cream da chocolate promise yace promise ta fito tana dariya yai saurin rufe motarsa da karki fito mn can ta hango jafar xai juya da sauri tai gunsa yah jafar ta kwala ms kira kamar karya tsaya xuciyarsa tace xamto jarumi mn ta karaso dan Allah kaxo ku gaisa dawa inkaje ka gani to baxani ba wallahi sai kaje me duda sun saba wasa yau sai yaji yarinyar ta bashi haushi tama raina ms hankali wato hartana da kwarin guwar nuna ms masoyinta ni na jama kaina ya fada dakaimai bansan mgnr ta fitoba dan haka ya maxe ban saniba bata cika jan xance va ita sai ta basar nadai fuskanci yah jafar bakasan kugaisa da yah xaem sai yaji duk kunya ta rufeshi mai ys yacika garaje yai dariya haba ni ba isa suka yo gurin kafin su karaso zaem yaxo ya mika ms hannu jafar ko eh ai na ganeka yai dariya mai yasa kannen nw sunce kai farine yah mubarak baki kaga in akace xa'a hadamu xan gano tunda kune kawai frnd nasu na kusa yai dariya ina mubarak din shi ance bakine kamar yar dunarmu xahra tasan da ita yake tace dadinta mai fadinma dunanne oho dai nafi wasu ko ba hk ba jafar sukai dariya baki daya. Abu kamar wasa zahra tarasa mai yasa take jin zafin mata inta gansu da jafar koda kuwa ada tana ganinsu tare koya batasan ace baya kusa da ita suna hira to wai mai hakan ke nufi ta tambayi kanta sansa kike kishinsa kike xuciyarta ta bata amsa iba baxai yuwuba ta fada a fili. ********************* Haba malan karka bada maxa mn karasa waxakai shakko koma ince tsoro sai mace kasan Allah danine da tuni anrufe wannan babin dan wallahi da tuni na fada mt uhum mubarak kenan ai garani na na iya fada mk kaida ka kasa fadawa kowa kabarshi yn nukurkusarka kai kuma ka vada wa kenan kaga malan bansan sharrifa ai shiyasa naga san na ramar dakai hhhh to wace sharrin naka ya hango oho pls kafadan sai dai inka yadda na fadi ba dai dai ba xaka fadan ko wace eh naji wace inbanda zakiyya hhhh jafar yaushe ka fara duba yai dariya aiko karamin yaro xai fiskance ku gaba daya kunasan juna kun kasa showing kai kake ganin haka mata sunada wuyar fahinta kuna mutunci kana cewa kanasanta sai wulacin kaga ni shine banso hhhh to basan gaske kake ba aishi so bakaji ana cewa rigar wahala ba to dole kasata kafin ka warke. Tun jafar da mubarak na boye boye harsuka hakura suka bayyana abinda ke ransu soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu yayin da zafira da zaem tuni sukai nisa asan junansu. Jafar ya takurawa zara kan yanasan aturo dan hk tasamu muhd ta fada ms dan bata da kamarsa shine yasamu malan y fada ms yaiko farin ciki sosai dan burinsa ya aurar da zara'unsa . manya sun shiga mgnar tun sa'adda umma taga irin kufin da ake kawowa na nagani inaso kawai hankalinta ya tashi sosai hankalinta bai kara tashiba saida taji sunan mahaifin jafar hankalinta ya tashi sosai dan haka ta tashi tsaye sosai. Abu kamar wasa asirin da umma take ya fara daukan jafar dan insuna tare da xara sai yadinga jin haushinta zahra ta kasa gane kansa dan kullum ynx sai sunyi fada yaita mt fada. Takanas umma taje gidansu jafar ta fadawa umman jafar aikuwa tahau ta xauna fada kamar mai taima umma godiya. Abu kamar wasa sai gashi yaxama gaske dan mahaifiyar jafar tace ita bata yadda adaura auran ba ta inda tashiga batanan tashiga ba mahaifin jafar bai dauki abin da mahimmanci ba ganin ya dau abin dawasa dan hk taje tasanar da innarsa taxo tai ta bala'inta indai yasake aka daura bashi ba ita yai ta
Chapter 6 · 0% Book details