← Book details Zara Yar Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 13

Sashe 3

Zara Yar Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inda suka barta wayam hankalin malan inyai dubu ya tashi wata nurse ya gani xata wuce ya tambayeta ta nuno masa emergency room tana ciki da sauri ya shige gadonta ne na karshe tana kwance sai wani matashin saurayi dabaifi muhammadunsa ba axaune abkujera da'alama bacci yakeji muktar yace baba bara naje gida karsuga ban musu sallama na tafi toshikenan dan albarka nagode yaron da ke xaune ya dago kai yaga yana shafa mt kai kasanta ne baba eh yaro diya tace Allah sarki ya mike daga xaman da yake ga guri xauna yi xamanka.

Anman baba mai yasa ka tafi ka barta wallahi ba tafiya naiba naje nemo kudine gashi duk yadda xanyi nayi bansamuba haka ne karka damu anbiya anman dan Allah baba kadena irin haka gangancine kaxo kabarta ba kowa gwandama ka tsaya inma mutuwa tai ku koma da ita eh hakane duk na gigice ne wallahi ai dakyar muka samu nurse tabar xancen da cewa tai baxata tafi ba sai ka dawo wallahi police xata hadaka yaxaro ido towa ai ansha kanta akiyaye gaba dai insha Allah.

Ya mike baba ni bara naje kar anaiman agida to yaro baka fadan nawa aka kasheba yai murmushi baba kenan karka damu ni dan Allah nai wallahi nagode yaro Allah yasaka yanata saka albarka yaron na amsawa Allah ya kara sauki amin yaro sai dai baka fadan sunanka ba yashafa kai sunana *Zaem* kijerar da ya tashi malan yabi yaxauna tunanin yanayin rayuwar xaran duk sukabi suka cika masa rai yadda aka haifeta yadda take tayuwa duk suka dawo masa baisan sa'adda hawaye suka biyo kuncinsa ba.
**********************
***********

*wace ce Zahara*

Dina haifaffiyar garin kano ce mahaifinta hamshakin dan kasuwane sananne afadin Nigeria su shida iyayansu suka haifa biyu sun rasu tun suna yara sai yayansu mai suna zaem mai bimasa zikir sai ita Dina dan autansu salman kasantuwarta mace daya da suka mallaka yasanya duk san duniya suka dora mata.

Lokacin da dina ta kammala secondary ne yasamu damar tafiya sch of hygiene inda take environmental health.
Ranar da baxata taba mantawa da ita ba itace ranar exam dinsu ta parasitology ta xauna gefen wani saurayi shi dan EVT ne yayin da ita take yar EHT kafin akawo papers har sun saba sunata hira akan nata course din yafi dole ya girmamata shi kuma yana ta zolayarta.

Tundaga sannan suka xama frnds indai ba lecture ce dasuba xaka samu islam cikin mata duk inda kaga dina kaganshi kai ko agidansu dina ansan da xaman abokinta islam.

Ada dina batasan hygiene anman yanxu koda dad yai mata batun yin jamb ai sai cewa tai tafisan kawai tai diploma a health inyaso daga baya tayi degree din aiko ya kyaleta.
Dina batasan tasaba kuma tanasan islam ba sai da sukai hutun semester ending dake shi ba dan kano bane ya hostel ne .

Dina na NDll dad yace aure xai mata da dan abokinsa aiko tahau ta dire ita basansa tana da wanda takeso yace waye ta fadi mai yace shikenan ya aminta anman xai bincike.

Sati biyu da batun yakira kan yanasan ta rabu da yaronnan baida asali tace ina ita haka takesan abunta duk yadda yaso ta rabu dashi taki .

So yagama rufe mt ido dad yace shikenan tayaji xai auranta dashi anman tasani bashi ba ita yayunta sukai sukai taki ita ta yadda haka aka daura auran.

Murna gurin sabbin ma'auratan ai ba mgn idanunsu ya rufe basa tunanin komai haka islam ya dauki matarsa sai bauci gaba daya suka watsar da karatun.

Zuwansu bauci komai dai dai yake tafiya kafin rayuwa tai wuya su kwaso su dawo kaduna anan dimma ba dadi tsi tsi suke in anci na rana ba lallai asamu na dareba haka dai sike hakuri ana haka Dina ta samu ciki gata da dan banxan laulayi duk tabi ta rame komai yai musu xafi.
****************
Cikin ta nada wata bakwai tace xata kano ganin gida yace ina ba inda xata bacin basanta sukeba tace itadai haka xata tafi.

Agajiye ta sauka ga yunwa da takeji yadda mamanta ta ganta yasa dasauri da abinci ta fara taryarta aiko sai loma kamar ba dina mai kincin abincin data sani bace aiko sai hawaye dad yana dawowa yace vaisan xance ba taxo tabar masa gida tana kuka mama nayi yan uwanta na bashi hakuri yai kemai mai haka bata kwanaba ko abincin bata gama ciba ya korata.

Haka ta dawo gida tana kuka maiyasa dad baxai mata uxiriba ta gane kuranta .

Duk yadda dina xatai islam yakaita danginsa yaki yanxima yashiryane dan xuwa xaitawo da kakarsa tai tai xata bishi yace tayi hakuri inta haihu inxasu maida kaka sai su tafi tare ahaka sukai sallama ya tafi.

Kwanansa hudu da tafiya ta haifi diyarta mace dayake yabar komai ranar suna aka yanka rago taci sunanta *zahara*.

Tun abin bai damun dina har tafara damuwa dan yau watan islam uku bako labari bashi ba kakartasa har bauci taje sukace baixoba daman ai daga Niger yaxo canma vasu da tabbacin inda yake koma dan canne aiko tai kuka mai isarta ita bama kanta takemaba sai yarta itace abin tausayi.

Watanta tara da haihuwa ta kuma gwada xuwa gida aka kuma kwatawa bama su tsaya suji bayanintaba ko ganin abinda ta haifa suka korota ta dawo kaduna.

Tun dawowarta daga kano jiki yaki dadi ciwuka kala kala ga ba dangi kusa sai wata makociya dake kula da ita.
Shekaran zara biyu tana gudunta ko ina harda dan gwarancinta yarinyace mai shiga rai tashaku da makociyarsu ita take mt komai wani sa'inma agunta take kwana itama ta yayeta.
*****************
Zahra yar'amana

20-60

Na F.A.Ya'u

Yaukam jikin dina yaki dadi hajiya barira keta bata baki kan ta rage damuwa sai tai murmushi umma kenan nidai ko bayan raina kitaimakeni ki riken xara koda babanta xai dawo kibashi diyarsa haba kekuwa cuta ba mutuwa bace sai kikaga kinga girmanta ni ban ganiba.

Zara xaune keta faman bugun uwar da gwarancinta ki tashi ta mike ta dauko takalmi yadda taga tanayi kamar xata daketa ganin bata kulata ba sai kuka umma barira ta shigo haba dina yaxaki bar yarinya na kuka aiko yadda ta ganta ya kidima ta subhanallahi ta dauki xara aiko babu uwar ta mace.

Tun rasuwar xarah babu wanda yaxo gurinta dan naiman xara haka take ta kula da ita itama fa sai kansar mama dan haka kaninta sunaiman dake kano yaxo ya tafi da ita da yar amarta.

Tun zuwansu gidan matar malan furai tabi ta tsani yarinyar dan kawayenta sunce watakil yar malan dince yayarsa ta rufa masa asiri ta rike yarinyar ko lekowa batai dan in ba haka ba kuwa taci na jaki.

********************

Yayan malan biyar hudu mata daya namiji duk sunyi aure muhd ne kawai agida Allah ya hada jininsa da xara duk yadda umma taso rabasu ta kasa hakan yasa take cewa xaran mayya ce.
Muktasira itace babba zulfa mai bi mata sai bilkisu mansura itace karama

Muktasira da bilkisu kamar uwarsu sike sun tsani xara vabu irin hantarar da basa mata indai sunxo gidan.
Mansurace dai ba sawa ba fitarwa bata shiga sabgarta yayinda zulfa ke tausayin yarinyar ko kwancen kayan yayanta ita take kawowa har saboma tana kawo mata halin malan gaba daya ta deve su.

Ko bayan rasuwar umman xaran zulfa tace xata dauki xaran umma tace indai ta dauka sai ta tsine mata lokacin xara na primary 3 aiko axaba kala kala dan daman idan umma nasa wa arage mata.

Makarantarma sai ta gadama take barinta duka ba kama hannun yaro abinci ba koyausheba duk wai tanasan ta mutu.

Maganar xara da yaji ya katse ms tunanin da yake tace baba kuka kake yace a'a gumi ne ta yun kura xata mike bari naima fifita sai ta kasa wash kafata sannu xara kiyi hakuri asannu xaki warke to baba.

Wajan hudu zaem da kakarsa suka xo dan tun da yakoma yabata lbri tace xata xo koda malan yagansu yaji dadi duda bai sansuba sai yaji ya yarda dasu ya barmusu xara yace xaije gida ya dawo .

Koda malan ya koma gida baibi takan furairaba wanka yashiga sannan yaxo dan yin sallah itako koda taga yadawo shidaya batare da gawa ba sai takaici duk ya rufeta dan taso ace ta mutu duda tana tsoron kar axargeta.
Sai bayan yama idar da sallane ya tuna baiko ci abinci ba tun karin safe tana kallonsa ya gama komai xai fice bata tambaye shi mai jiki ba malan baxaka ci abin ci bane yako watsa mt wani kallo gami da tsaki ya fice.

Saida ya tsaya ya sayi biredi duda bashi ya dauka sannan ya wuce asibiti sunanai sai dai xaran na bacci zaem ya fice inna nabgefe a xaune suka kara gaisawa da da malan sannan take kara tambayarsa mai yasamu xahran yake fadi mt ai gini ne ya fado mata ta nuna tausaya warta sosai kafin su tafi harda ajiye masa kudi gashi koxa'a naima yaiko ta godiya.
*******************
Satinsu biyu a asibiti aka sallamosu ta warke sosai saidai karayar dataine sai ahankali.
Duk xaman dasukai a asibiti umma furai bata taba koda dawasa tace ma malan yamai jiki ba balle tai gigin cewa xataxo dubata a asibiti balle kuma sauran yayanta inka dauke mansura da taxo sau daya sai xulfa da kullum sai taxo muhd kuwa shi yaxama mai jinya harsun saba da xaem kai kace sun shekara danshima kullum yana tafe shida kakarsa.
Makotansu xaran kuwa kullun sai an samu mai xuwa.

Koda suka koma gida ma kullun gidan akwai masu xuwa kaxalika da abinda xasu kawowa xaran ko an baima umma cewa take bataso duda kuwa ranta naso.

Ko agidanma umma bata kalletaba balle tamata sannu kallon kirki bata isheta ba dan tafuskanci malan babu abinda xaiyi sai muxurai duda kuwa randa xasu dawo yaja mata kunne kan xaran takuwa ji dan saidai hararar ba damar duka.
Chapter 3 · 0% Book details