← Book details Zara Yar Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 13

Sashe 13

Zara Yar Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ya fara bada labarin inna ke kuka sai asannan ta kalli yan matan da suka shigo tare ina jikan tawa sai asannan taga zahra ta mike daniyar zuwa gun zahran itama ta taso suka rungume juna suna kuka ashe jinin muce shiyasa muke santa ashe jinin diyarmu ce tilo da muke so sauran yan uwa duk duk sun iso suna masu farin cikin ganin jinin dina saidai suna masu alhinin rashin yar uwarsu.
Cikin kuka zahra ke nemawa ummanta gafara sukace ai tuni suka yafe mata rashin ganin hotunanta hakan ya farune sakamakon in malan ya gani saidai yaita kuka yana damuwa ganin haka yasa aka boye su dan rage masa damuwa.

Nasir na zaune yana jiran fitowar zahra ta fito sanye da doguwar riga Golding ta nada mayafin rigar duda ba wata kwalliya tai va tai kyau sosai inbanda baka ce da sai ace bala rabiyya ce musanman a idanun masoyinta sallama yakeson suyi da yake kakanninta sunce su anan zata zauba bikinma anan za'ayi tunda ta fito yake kallonta sai taji duk kunya ta rufeta tunda ta gaisheshi ta kasa cewa komi jitake kamar ta koma ciki.
Zahra yace yadda ya ambaci sunan yasata saurin dagowa sukai sa'ar hada ido yasakar mata murmushin dake narkar mata da zuciya murmushin dake kara mata sansa na fuskanci ni kadai nake budirina kan soyayyar mu kodai fasa auran xa'ai tai saurin dagowa me kace nasan kinji sabida me kace haka sabida na fuskanci da cutar wa kullum saina rokeki kice kina sona anman koda wasa kinkasa ko sau daya fadamin yai dariya ai kaidinne ba sanka nake ba kai kuma ka kasa fuskantar haka jira nake kace zahra kice kina kaunata sai ince Dr. Na ina sanka ina kaunarka zan kaunace har bayan rai Dr. Na kasa aranka zahra me kaunarka ce zahra taka ce tace baka jiba ya dago ina kaunarka tai ciki da gudu ya rungume hannunsa ak'irginsa dadi na ratsashi yai murmushi ahankula yace zahra nima ina kaunarki jiyake kamar ya jawo auransu adaura yanxu zahra kenan sarkin kunya zanso ganin ranar da zakice kina sona ba hanyar guduwa inga yaxakiyi da kunya.
Yau su nasir sukaxo dan zuwa gidan baban zahra me rasuwa yau cikin farin ciki take dan tana dokin ganin su duda tana tunawa da maganganun umma zahra ki daure ki mance damu sai dai batajin zata iya mantawa da iyalin babanta wanda yasota alokacin da kowa ya kita taya zata mance da ahlinsa kosu sun k'ita sunyi sa'a duk suna gida dan ummance ba lpy duda halin datake ciki besa ta gane zahran ba zahra naganin halin datake ciki hankalinta ya tashi sai fada take me yasa vasu kaita asibiti nan ta kamata sai asibiti.....

*Zahra Yar'amana*
*145-150*
*Na F.A.Ya'u*

_Wannan paging nakine_ *Rasheedat Isa Mrs Idris* kinfi _kowa san Zahra yar'amana ina alfahari dake cikin Fans dina_

Koda umma ta warke kuka ta dinga yi kan tayi hakuri ta auri muhd kan zahra tace wani abu nasir ya rigata ai nine mijinta sati me kamawa za'a daura auranmu umma tasake fashewa da kuka ada ta hana zahra aure dan karta je inda zata huta sai gashi tasamu fiye da wadancan inkyaune akwaishi in kudine yanadashi in illimine yanadashi ahankula tace wannan izinace babu wanda ya isa ya hana abinda Allah ya baka.

Tun zuwansu zahra gidansu muhd Fadima da muhd suka kulla soyayya tun tana zuzzukewa harta ware kankace me mgn taje gun manya.

Zahra ta ziyarci kawayenta su zafira ansha hira kuwa sunyi murna sosai anan ta basu katin dan su gayyato former mate dinsu ba buk nan Zakiyya ke fada mt itamafa sauran wata daya bikinta ita da muktar zafira tai shiru eyye wato harmun fara surukutar haba yarinya kema kinsan inzanji kunyar kowa vanda taki suka sa dariya ai dannaga sai kifini sanin komi tai dariya zafiran uncle zaem kenan.
Iya kyau kam amarya da ango sunyi kyau faden kyansu ma bata lokacine da yake andaura aure wanda dubban jama'a suka shaida hakan yavasu damar ruko hannun juna ranar families day sunyi kyau ba karya yan bikin kansu sunyi kyau.
Saida aka kwana biyar ana shagali kafin akai amarya gidan ta na wucin gadi kafin su wuce german.
Rayuwa me dadi suka tsarama kansu momi yadda sukeso yake tafiya akullum kara kaunar junansu suke basasan abinda zai raba su aikima adole nasir ke futa.
Wata daya da bikinsu akaina zakiyya da muktar zafira da zaem muhd da fadma shima nasu bikin kam ya kayatar .
Ana gama biki suka tafi german inda Nasir zai karo karatu acan zahra itama tai karatunta fanni noma wato agronomy shekararsu biyu acan ta haifi yayanta maza duk biyun sukaci sunan babanta me rasuwa wato baban muhd dayan kuma baban nasir alokacin data haihu take ganin kamar nasir zai sauya saitaga shi kamar ma alokacin aka bude masa babin kaunarta .
Shekararsu hudu da aure yayan zahra biyar sun saba da uban dan ita kullun tana sch be kuma yadda da daukan nany ba dan tunda ya gama nasa yakoma dan raino ko makaranta baya bari ta tafi dasu suna gunsa .
Zahra na gama karatunta suka dawo gida Nigeria sunyi kyau sosai da yaransu kaikace turawane inba mgn sukai ba dan sun dage yaran sun iya hausa dan basa son yaran su taso bada yarensu ba koda suka dawo nasir be shawara da itaba ba ya sayi fili ya gina mata tamfatsetsen kanfani na sarrafa kayan noma sai budewa akaje yi da ita tai murna sosai ta gode masa kan kace me kanfanin ya shahara ba iya Nigeria ba harda sauran kasashe makofta.
Yadda taga umma hankalinta ya tashi bata da lpy sosai muhd baya gari tunda yasamu lecturing a ABU yakoma kaduna sai lokaci lokaci yakanxo matan duk suna gidajensu basu san jikin yai tsanani haka ba hankalinta atashe takaita Aminu kano nan sukace saidai india zahra tai komi kan futar umma waje .
Zahra har niger naje ta dauko kakarta kawun babanta ya lalace ya zama abun tausayi shima ta tawo dashi dakyar tasamu ta shiryasu da babanta ta bashi jari.
Har gida taje ta duba jafar suka yafi juna anan suka kulla xumunci har bikinsa taje ummansa tai ta neman gafararta tace ai vakomi.
Koda umma ta dawo ta warke simul tai takuka tana kara neman afuwa ayau ta kuma yadda da karin maganar bahaushe dana kowane kahaifa bakasan me moraba gashi ita anhar mata zahra uwatta tarasu ita tana mora.
Zahra zaune tana bin yaranta da kallo yan biyu na game mansur na rubutun haddarsa smally ta fado kanta tana dariya yayin da hafix ya biyo ta mamanmu kinganshi ko ta tareshi haba yarona nasanka da hakuri kaifa babbane mai tamaka itace ina wasa da tsuntsuna ta sakeshi ya gudu wallahi mamarmu bansaniba ya gudu to kaji bata sani ba ayi hakuri zan siyo ma wani yasa ihuuu yawwa mamana shiyasa nake sanki waima mamanka mamanmu dai ke kuma wayasa dake mamanmu kinga yanaimun rashin kunya ko kul yayarka ce vata hakuri sorry sis ya wuce tace mamanmu bakice sagira ta ban hakuri ba bashi hakuri ta turo baki sorry bro yai dariya its a bygone issue ya wuce Nasir ya shigo rige da jaka ta mike ta katbo jakar ta cire ms takalmi da rigar sama tai ciki da lemo ta fto yakarba yana kara wash tace ansha aiki kedai vari wanka ko ci duk wanda kika ce girmanki ne ai to shikenan wankan ai saimuje ko ta dangabe kai baka ganin da yara ya kwaikwayi maganarta to ainima yaron ne kayi hakuri kaje pls kiyi hakuri mu tafi tare pls tasan halinsa dan haka ta dago shi muje ko sukai dakinsa tana shiga ta fito da gudu tana dariya ya kada kai shima yana dariyar yai bayi.

Wai in tambayeki yn cin abincin yn mgn mai kika zubama abincinnan naji yana zaki zaki aff mantawa kai daci daci yake ohh haka nefa me kika xuba masa maganin mallaka inaso kaxama mijin tace yai dariya yarinya kin makaro aini kan tace ne Allah ko kina mamaki ne ya kurbi lemon lalala yanaji zafi kamanta tafasa yake suka saka dariya baki daya.
Yana zaune yana kallonta tana shafa mai ya mike yana tayata shafawa sukajiyo kukan sagira ya lakace mata man a hanci ya fice yana fita ta fada jikinsa tana kuka dakyar yasamu tai shiru mene ba yaya ce ta dokeni ba to muje haba yaya me ya hadaku ba itace na aiketa taki xuwaba haba sagira kidena kiwa ke kuma banda duka ya kwantar da ita kan gadonta yaja musu vargo ya musu addu'a yawwa yan yarana sai da safe zahra ta turo eyye yaranka ma ko to sarkin kishi yaranmu.

Dakin yan mazan suka wuce sagir na game sulaiman yai bacci hafix rubutu nasir ya kwace rumote din game din zahra ta rufe littafin naxa akwanta dare yayi suka lullubesu suka rufo musu kofa sikai waje.

Rayuwa kenan wataran tasaka dariya wataran tasaka kuka wai yauni zahra nake dariya nakejin dadi nakeda miji da yarana masu sona masu burin faranta mun Allah kabarni da iyalina ta vaya taji ya rungumota Amin maman sagir tana dariya ta daga kai ta kalleshi yadaga mata gira batasan afili take mgn ba ahankula ta kuma cewa Alhamdulillah.
Nima anan nake cewa Tammat billah daya bani ikon kammala wannan labari lpy.
*Godiya*
Gaduk wani ko wata da yabada time dinsa ya karanta wannan labari fatan duk kuskuren dake ciki za'amin afuwa dan adan ajixine nayi labarinne dan ilmantarwa nishadan tarwa bawai dan cin zarafin kowa ba wanda yaga wani abu da yashafeshi akasine bawai danshi naima kirkirarrene ba labarin wata ko wani bane.
*Abin lura*

_Komi na duniya dan hakuri ne ba'a taba dawwama cikin yanayi daya_
_Dana kowane kishi kan yaya ba namu bane mata dan bake kika haifa ba bai kamata ki dinga azabtarwa ba bakisan wane anfani zai miki agaba_
_Abin da Allah ya baka ba wanda ya isa ya kwace koda zai hado duk duniya_

*Taki Dabance*
*Salma Ali Wada*
_Loves u fans badan kuba da tuni nadena rubutu karfamin guwa dakuke kullum yasa nake kara dagewa dan kara saku cikin farin ciki_
For comment,correction or advice u can contact me bear.
Http://fayau26wordpress.com
09028287218
F.A.Ya'u facebook page

*Nagode*
Chapter 13 · 0% Book details