← Book details Zara Yar Amana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 13

Sashe 1

Zara Yar Amana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zahra yar'amana.
1-20
Written by
F.A.Ya'u

I am forever grateful to Allah(S.W.A)

In Dedication to my Parents.

My appreciation goes to
Salma Ali Wada
Zakiyya Aminu Ibrahim
Hawwa Usman Ya'u
Rasheeda Isah (Mrs Idris)
For their helpful support.

One love to Readers no word to express by thanks.

Banhakuri
Ina mai kara bawa makaranta hakuri kan sauyin suna na wannan littafi daga yar'amana xuwa Zahra yar'amana hakan yasanya nayi kokarin hade muku shi a page daya nagode.

  Bismillahirrahmanirrahim

Kuka kawai take kai kace an aiko mata da sakom mutuwa wai badake nakeba wallahi kika sake na dauko hijabina baki shigoba saina kure miki gudu na kamaki nakuma dakekin mara mutunci kawai ahankula take bin bangon kai kace wata wahainiya ce saida taxo daf da ita ta xuro hannu xata cafketa tai wani tsalle ta koma baya lallai ma yarinyar nan nikikai ma haka ko jibi yadda kika sanya na kurje hannu na tai ciki a fusace.

Dasauri ta bi bayanta tana kuka dan Allah umma kiyi hakuri baxan kuma ba xan wanke karma ki wanke sai afkin ki cuci mutum kixo kina bashi hakuri shegiyar yarinya mara tarbiya tako hauta da duka kai kace tasamu jaka saida tai mata lilis sannan ta saketa dauran inkin gama kukan ki fice inkin dawo na dada miki munafika ta shige daki.

    Au baxaki tashi kimin abunda nasakiba ko dukanne be ishekiba yar marasa mutunci to inma malan kike jira ya dawo ki hadani dashi ba yanxu xai dawoba sauran ya dawo naji lbr gobe kici na jaki .
  Zara yau bazaki makarantar bane xani yaya so nake na gama wannan wanke wanken to kiyi sauri karki makara dakinshirya ai damun tafi tare lah yaya kai tafiyarka karka rasa exam din to sai kin tawo to yaya Allah ya bada sa'a amin ya leka daki umma na tafi to dan albarka sai ka dawo yana fita umma ta leko ke wai yaushe xance miki kidaina kula yaronnan umma dan Allah kiyi hakuri wallahi baxan kuma ba ta dungure mata kai kima kuma.

   Umma na tafi ke zonan ina xaki umma makaranta mn eyye wato makaranta mn ko kin gama aikin dana sanyaki eh umma to sai kindawo tamurmusa gami dayin zauro ke sunan datake kiranta kenan zonan tazo ta durkusa ba wata nakaranta da zaki kinma daina zuwa tasa kuka umma dan Allah kiyi hakuri nace kinmun lefine .

  Kuka kawai take tana rokon umma kan tabarta ta tafi makaranta itako tai mata banxa tuwonta ma take ci tana sautaron waka ta cillo mata kwanon data gama ci maxa jeki ki wanken daga nan ki wuce dakinki in inada bukatarki xan nemeki sun sun ta mike tai gun wanke wanken bayan takai kwanon madafa tai xaure dan nanne dakinta yake indai malan benan ko yai tafiya ke ta juyo kikace kin gama komai eh umma kya iya tafiya anman inna fito naga wani aikin wallahi kika dawo saina dakeki jitai kamar ta daka tsalle dan murna saidai ba dama aduniya tatsani abinda xaisa yau ace baxata makaranta ba dan bata da inda take jin sukuni kamar nan din duda goma saura haka ta daure tai makarantar dan ta fiye mata gidannasu sau dubin bubata.

   Tai sa'a ba'akoma break ba dan haka ta saje da sauran yara daketa wasa kamar ba'a lokacin taxo ba.

*******************

Zarah!!! Na'am yaya ganinan ta fito rike da hijabinta kinshirya ne a'a yaya wai mai tasa kwanakinnan bakyasan mutafi tarene ko kekenne bakyasan hawa tai dariya lah wallahi yaya ba haka bane ban karya bane katafi karka makara to aishikenan kiyifa sauri karki makara kinji ko to yaya se kadawo.

 Muhammad kenan dan kimanin shekara goma sha shida xuwa sha bakwai sanye yake da uniform dinsa na Rumfa college inda yake ss3 yayin da zara ke primary 4 anan Kwalli special primary sch.

    Furai yarinyar nan kuwa ta dawo eh tana daki kasanta bata san zaman waje kodai kika hanataba kajika kaima dai malan inna hanata maye ribata kinga ba musu nace muyi ba maza kiramin ita mezata maka yau naji ikon Allah shikenan mutun da diyarsa baxai kirataba sai ace danmai yi hakuri mai ya maxa ni kiramin ita tamike tai ribabben dakin da shine na xaran tun rasuwar ummanta.

  Ke kixo inji ubanki kuma sauran inya tambayeki kinci abinci kice a'a saina karya miki kafa inya fita gobe ta juyo dan komawa inda malan din yake asanyaye ta mike sabida wata irin yunwa takeji ga wani irin ciwo da kanta yake har wani jiri ke dibarta rabonta da abinci tin jiya tunjiya da safe shima dan da sch ne tasamu kawarta taxo da abinci suka ci yau ba mkranta gashi yini tai tanai ma umma aiki ko kanxo ta hanata yaya muhd mai sai mata kosai shima tunjiya baya gida.

   A hankula ta xauna baba sannu da xuwa yawwa zara kinko ci abinci tai saurin kallon umman dake gefenta tako gallo mata harara eh baba naci anya kuwa kin koshi eh nakoshi anya kuwa ni banga alamar koshi atattare dakeba ya miko mata na gabansa da umma ta ijiye ungo ci wannan umma tai saurin mikewa wa wallahi baza ta ciba aiba ubanta ya sayoba ke Fure mene haka bansan wulakanci aikaji mainace wallahi baxata ciba tabari in ubanta ya sayo sai taci aike naki uban ya sayo ko kai malan karka xageni kan shegiyar yarnan taka yanzu diyar tawa ce shegiya to karya nai wallahi ki kiyayeni nine ubanta karki kara sheganta min diya hhhhh lallai eh kaine ubanta seka fadan sanda ka auri uwarta abincine dai ko ki cinye abinci yai tsaki yai waje.

    To mayya aisaiki koma dakinki ko kin wani xuban ido kamar xaki cinyeni ta mike tai dakinta ke xonan dan wallahi ban yarda dakeba sai kin fadan inda kike cin abinci sai kin fadan dan iskan dake baki abinci tsananin ciwon da kanta keyi da yadda cikinta ke murdawa yasanya maganar umman ma taji kamar tana kwara mt ruwan xabi aka kawai saita juya danyin dakinta aiko umma ta kufa ta fincikota lallai yarinyar nan wato ga yar iska na mgn shine xaki wuce dakinki ko tako jawota kofar sakin muhd ta ciro wayar cajar fitilarta ta hau duka ko ihu bata iyawa se hawaye kawai dake bin kunxinta kan umma ta ankara sai ganin yarinya tai asandare na shiga uku karfa yarinyar nan ta mutu ga dan rigimar nan na gari wato malan aiko sallamarsa dataji ta kara daga mata hankali.

     Salati ya saki furai karfa kiyi kisan kai kasantuwarta jaruma mai taurin rai in nakasheta ma ai na rage mata takaici ta murguda baki gami da yin dakinta ganin da ranta ya debo ruwa ya shafa mata a fuska sa'annan ta farfado shayin da yasayo mata ya bata kasantuwar cikinta ya nade tana gama sha tayo amansa subhanallahi ya fada gami da daukanta yasanyata bayan mashin dinsa sai asibinta Wata tazo dake nan bayansu saida suka saka mata ruwa koda ya kare suka rubuta mata dan mgni sai isha'i suka baro asibitin.

Wai yau malan baxaka fita ba dake kike sawa na fita a'a gani nai shuru har tara baka fita ba shine nace bari na leko ko lpy to banga dama ba ko xaki fito dani ne tai tsaki dan Allah ka shekara adakin ta kade labile gami dayin dakinta.

    Shima tsaki yai gami da mikewa yai madafa kofi ya dauko yai waje koko mai xafi ya sayona xara ya amso kosan da tun daxu yabada kudin saida ya biya kanti ya sayo madara yar ashirin da biyar ya dawo gida.

   Tana kwance adaki ya shiga dakin yai kaca kaca duk tarkacen umma ne yace zara ya jikin ina kwana baba lpy kalau yar albarka taso ki karya saida ya tabbatar ta koshi sa'annan ya bata magani ta sha yadan gyara mata dakin kafin ya fito.

      Saida yai wanka ya shirya tsaf da niyar fita sannan ya leka dakin Furai Furai ni xan fita sauran indawo intarar kin bugarmin diya ko kin hanata abinci kibari randa kika fara ciyar damu saiki fara hanata tai dariya to inna hanata mai xaka mun sakinki xanyi wallahi akan yata tas xamu rabu ta rike hanci tana buda sai mai to akaina aka fara rabuwar aure balle irin auranka auran kaddara auran jidali eh duk naji anman wallahi kitsaya kiji rufe ido xanyi na manta da yayan dake tsakaninmu in hadaki da police kinsan inada shaidu duk unguwar nan duk wanda na kira sheda ne abinka da mutumin kauye da tsoron yan sanda banda abinka malan mai kuma yakawo maganar wadannan masu bakar xuciyar nidai na fada miki wallahi ko yau na dawo na taras kin mata abinda bai gamshenma kisan makomarki.
*****************

Tun daga wannan lokacin xara ta samu saukin duka da horon yunwa saidai faduk wani aikin wahala ya koma kanta bata da takaimai mai lokacin kanta kafin ta tafi sch aikine inta dawo ma aikine ta rage hanata abinci duda bawani isarta yake ba yafidai babu.

   Yar albarka kina inane ta fito da sauri gani baba kinje makarantar kuwa eh naje daxunma na dawo to yayi kyai xoki gwada kayannan muga koxasu miki ta karba tana dariya jeki ki gwado muga kai anman sun miki kyau kamar mai saidawar yasanki saida nace baxasu mikiba yacw mai xai hana tai dariya nagode baba Allah yasa da alkairi amin zara'una.

   Nifa malan ban gane mai kake nufiba dan maine xaka dinga sayawa wannan yarinyar kaya alhalin ni ba isata yai ba to banda abinki har yaushe na siyo miki ina dawo wata wancan watan kena siyowa to naji anman ai wannan nuna banbanci ne in gaskiyane ai muhd ma na bugata eh nayi rashin adalcin komai xaki ce sai dai kice ba xan siya masa ba to karka siya dadinta bani Allah xai kona ba sau ki godema Allah tunda ba kabarinmu daya ba yai tsaki gami da shigewa dakinsa.
Chapter 1 · 0% Book details