← Book details Zaman Hostel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 43

Sashe 36

Zaman Hostel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sunanta yakira
Nabeela
Kallonshi tai batare data amsa ba cigaba da magana yai dole a zubar da cikinan banason tara yara gaskiya kinga na manyanta na tabbata bazaso girma tare daniba kuzan bari da wahala idan na mutu, idan kika lura ko maimuna yaran'mu hudu tonda ta haife na hudu nace zan kaita a juya mata mahaifa amma taqi yarda, kwanakin bayan tayi BARI ai nine nabata magani zubar da ciki saboda nafada mata yaran sun isa haka kuma a shirye nake da rabuwa daita har idan bata amince ba.

Babu yanda tai haka ta amince bayan sati daya dayin miscarriage dinta shine na kaita aka juya mata mahaifa.

Dan haka kema dole a zubar da cikin nan har idan kinaso kwanciyan hankali

Nabeela tarasa abinda zatace saboda tsabagen mamaki da tashin hankali dafe kanta tayi hade da zama a kujera

keep following me i need more and more comments read and share😘😘😘
💖💖💖💖💖💖

*ZAMAN HOSTEL💞*

💖💖💖💖💖

STORY
AND
WRITTEN BY

RAHEEMA🔥

DEVOTED TO👇🏻
(YUSUF)💋

DEDICATED TO👇🏻

_Itz Mman 2wins😇🥳_

🅿69-70

Koda tazauna a kujera wasu hawayene suka zubo a idonta batare data kalla Alhaji shehu ba tafurta to a gaskiya nidai bazan iya zubar da ciki ba koda kowa hakan zai zama sanadin rabuwana dakai.

Kwafa yayi kana yace haka kikace
Daga kai tayi hade daciwa "Eh
Tsaki yai sanan yanufi kofar fita yana fadin tonda haka kika zaba mu zuba.

A bangaran Muneera kowa abunta kullum kara gaba yakeyi mansur yafara gajiya da halinta ton yana hakuri yanzu hakurin'shi yasuma karewa, a yanzu Muneera bata aikin komai saidai tai wankan jikinta kawai bata gyaran gida, bata girki daka makaranta take siyo abincin daza taci ga yawan bacci da takeyi.

Kwance take akan resting chair dake dakinta farar vest ce a jikinta wace ta rufe rabin cinyarta, mansur na zaune gefen gado yana aiki a system dinshi.

Rufe system din yayi sanan yace Muneera
Kusa dashi ta dawu tazauna tana fadin naam herty

Hannunta ya rige cikin nashi sanan yace meke damunki?
Bata fuska tayi sanan tace ba abinda ke damuna herty
A'a fadamin gaskiya gaba daya kin canza Muneera bakya girki, bakya gyaran gida, ba wanan ya dameniba hanane hakkina da kikeyi shine damuwata gaba daya bakiso na tabaki dana tabaki saiki bata rai jiya har kuka kika dingayi kifadamin meke faruwa dan'Allah.

Sunkuyar dakai kasa tayi sanan tace herty kayi hakuri amma ba abinda kamin, gyaran gida kuma da kaga banayi wallahi kasala nakeji a jikina ko tularen wuta bana sawa saboda banason kamshin, haka kuma banason kamshin abinci tashin zuciya yake samin, kasa tai da murya sanan tace and then hakama sai naji banason sex. Ko school danya zama dole nake zuwa

Ton kafin Muneera tagama magana mansur yafara murmushi rungumeta yai a jikinshi hade dasa hannu ya shafa cikinta sanan yace ba laifin ki bane laifin ajiyar da nayi anan ne shike saki haka.

Sake shigewa jikinshi tayi tana fadin herty babu wata ajiya a cikina da farko nima nayi tunanin hakan amma sai da naga period dina sainace ba ciki bane
Tallafu fuskarta yayi yana fadin da gaske kinyi period this month
Daga kai tayi sanan tace Eh herty
Hmmm to shikenan kuma dai menine gobe sai muje asibiti.

The next day da misalin karfe tara na safe Muneera ta tashi daka bacci saukowa tai daka bed dinta sanan tanufi parlor da mamaki take kallon koina murmushi dauke a fuskarta tasauka parlor kasa tana sauka ta iske Mansur na aje flask a dining

Fuska dauke da murmushi wanda takasa boyewa tafurta herty menine haka?
Naga koina tsab tsab kayi gyaran gida nuna tv tai da hannunta tana fadin kalla yanda ka goge tv da show glass dincan wallahi sunfita sossai.

Smiling yai sanan yanufi kitchen yana fadin kedai zuki zauna kici abinci dole nayi miki aiki tonda baby na bayaso kina wahala

Zama tai a dining tare dasa hannu ta shafa cikinta a zuciyarta tafurta Allah yasa idan munje asibiti ace ina da ciki bansan yanda zaiji ba idan ba ciki bane duk wahalan nan da yakeyi dani.

Chips and egg yai frying, nan yazuba mata sanan ya hada mata tea, feck yasa ya debu chips din har yakai bakinta saikuma yaqi samata a baki turo baki tai hade da bata fuska tana fadin nikam kabani

A baki yasa mata yana fadin sarkin shagwaba kawai, shafa face dinshi tai tana fadin herty wanan chips din yai dadi sossai irinshi zakana min kullum, murmushi yai sanan yace qalbe amma kamar nacika gishiri egg din kuma maggi yayi yawa

Cika feck tayi da chips sanan takai bakinta tana fadin a'a nidai banjiba a haka yamin dadi herty kayi kokari sossai
Yanda ta yaba mishi ba karamin dadi hakan yamishi ba

(Idan mijinki yai surprising dinki ta hanyar girka miki abinci daure kiye appreciating kice yayi dadi koda kowa beyi dadi ba daure kici koda kowa dakyar kike hadiyewa hakan zaisa yaji dadi gobe yai miki abinda yafi haka.... Duk dadai a zamanin da muke yanzu da wuya a samu namijin dazai zage yaima mace girki buuuuuuh nasan dai baza'a rasa ba shawara ce daka marubuciyar🙄)

Driving yakeyi tana zaune gaban mota hannunta rige da waya tana buga game... Uhmmm herty

Kallonta yai sanan yace qalbe ya akai?
Wani asibiti zamuje ne herty?
Smiling yai sanan yace wani hospital kikeso muje

Shiru tayi nadan wani lokaci sanan tace muje hermony private hospital ne asibitin su aunty sadiya

Sai murmushi nurse sadiya take tonda taga Muneera da mansur zama sukai sanan suka shiga gaisawa

Muneera idonki kenan ko?
Murmushi Muneera tayi kana tace aunty sadiya kiye hakuri ai inanan zuwa gaishe ki har gida.

Tohm shikenan
Kasa tayi dakanta tana fadin aunty sadiya daman so nake amin gwaji koina da ciki
Murmushi Aunt sadiya tayi sanan tace tohm hajiya Muneera

Kusan 30minutes suna zaune kafin komai ya kammala, cikin farin ciki ta miga musu wata takarda tana fadin congrat Muneera kina da ciki, rungume Muneera mansur yai yana fadin na fadamiki kina da ciki amma kinqi yarda kinji ko

Herty yaza'ai nayarda bayan nayi period this month kuma ance masu ciki basa period, nurse sadiya ce ta katseta daciwa waya fadamiki haka

Akwai wayanda koda suna da ciki suna menstruation nan tashiga mata bayani

Murna da farin ciki fal zuciyar mansur haka suka kuma gida yana tarairayan Muneera kamar kwai a cokali.

Dukda Muneera batason mai aiki amma ba yanda ta iya danko mansur saida yasa aka kawu mata yar aiki saboda aike aiken gida Muneera bayi takeba cikin yasa mata kasala dasan jiki bata da aiki sai bacci.

A yanzu salma da najib zaune suke lafiya bawani tashin hankali a tsakaninso amma saidai data tina zai kara aure sai taji ranta na baci

Zaune suke a parlor suna kallon news magana nacinta amma tana tsoran furtawa candai ta daure tace

Yaya najib nace yaushe ne daurin auren naka?
Batare daya kalleta ba yace saura two weeks
Ta6e baki tayi kana tace har abun ya matso haka lallai karasa maganan tai daciwa Amaryan yar kaduna ce?

Eh a kaduna take causin dita ce ma!
Gaban tane taji ya fadi a zuci tafurta lallai wato yar uwarkace auren zumunci shikenan za'a hademin kai

Wata tambayar tasake jefa mishi aina Amaryan zata zauna?

Sai a wanan lokacin ya juyu ya kalleta kana yace anan gidan zata zauna a wancan flat din zata zauna amma zata fara zama anan zuwa lokacin dana karasa gini saita kuma gurinta

Zare ido waje salma tayi tana fadin zata zauna aina
Haba dai yaya najib sanin kanka ne two bedrooms ne anan bata karasa ba ya katseta daciwa a dakina zata zauna ba naki ba

Cikin bacin rai salma tace ok fine idan kace a dakinka zata zauna karda ka manta kayan dake dakin ai daka gidanmu naxu dasu, sanan kuma kitchen daya zamuna sharing shima kayan kitchen din ai mallakinane and then parlor ma haka kayan ciki duk daka gidanmu naxu dasu.

Fuska a hade najib yace wanan duk mai sauki ne bed dinki dake dakina za'a fitar dashi amarya zatasa nata kafin nakarasa mata gini, sanan kuma maganan kitchen da parlor da kikeyi babu abinda za'a taba miki anan da kayanki zatai amfani kafin takuma nata bangaran bawani dadewa zatai anan ba befi tayi wata biyu zuwa uku ba, hakuri zakiyi idan takuma bangaranta sai a dawu da bed dinki dakin.

Saboda kishi tine salma taji zuciyarta na zafi kamar zata fasa kirjinta tafito cikin daga murya take fadin haba haba aiwanan cin fuska ne wallahi. Saboda an rainane kuma ba'a daukeni da daraja ba shine za'a wulakantani ta wanan hanyar gaskiya bazan yarda ba. Tonda baka da wajan dazaka ajeta saika hakura da auren har zuwa lokacin dazama kammala gini

*WATA SABUWA ANYA AMMA SALMA ADALCI KOWA???*

Keep following me i need more and more comments read and share😘😘😘
💖💖💖💖💖💖

*ZAMAN HOSTEL💞*

💖💖💖💖💖

STORY
AND
WRITTEN BY

RAHEEMA🔥

DEVOTED TO👇🏻
(YUSUF)💋

_Wattpad👉🏻Fatimamuneera001_

🅿71-72

Migewa najib yayi batare da yacema salma komai ba, itama tashi tayi tabishi a baya tana fadin yaya najib dakai nake magana kaima kasan baka kyautamin ba kor?
Be saurareta ba ya shige dakinshi hade dasa ma kofar key.

Jingina tayi a jikin kofar wasu hawaye ne masu zafi suka wanke fuskarta a fili tafurta ne kenan kullum cikin tashin hankali daka wanan sai wancan.

A bangaran nabeela kowa ton daka wanan ranan bata da kwanciyan hankali Alhaji shehu ya matsa mata ya takura mata abu kadan zatayi sai masifa yanzu abun nashi yaci tira ya matsa mata da sex a rana saiya nimeta sau uku da daddare bayan sallan Asuba guraran karfi daya saiya zankado yadawu gida koda kowa tana school tosai ta dawu gida.

Duk tabi ta rame yasata a gaba magana kadan sai duka, kwance take a gado yayin da take kyarma tana rawan sanyi sama sama take sauke numfashi saboda azababen ciwan kai da takeji wanda ko yaya ta juya sai taji kamar an kwada mata guduma.

Kuka sadiq yakeyi hakan yasa ta rungume shi a jikinta kana tasa mishi nono a baki taci sa'a yayi shiru. Tana kwance a haka taji a budo kofar batare da sallama ba
Chapter 36 · 0% Book details