← Book details Zaman Hostel Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 43

Sashe 21

Zaman Hostel Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dafa shoulder nabeela tayi hade daciwa Qawata yanaga kin rame?
Kodai kinsamu cikine yana baki wahala?
Turo baki nabeela tayi kana tace hmmmm Muneera kenan ba ciki bane kawai dai ina cikin wane haline hankalina ba'a kwance yake ba kedai kitayane da addu'a akan rayuwar aure na

Murmushi Muneera tayi sanan tace nabeela wallahi kin burgeni da baki zama mace mai fallasa sirrin mijin ta ba tonda nake dake baki taba boyemin wane sirrin ki ba sai yau, kuma naji dadi da baki fadamin ba. Amma abinda nakeso dake shine ki dage da addu'a ki tsaya ma Allah kidage da sallan dare kina fadama Allah kukanki ki kara hakuri nabeela watarana komai zai zama tarihi daka karshe inaso nafada miki karda kice zakiyi hakuri dazai cutar da kanki ako wane irin lamari kika tsinci kanki ki kasance mai hakuri amma ba hakurin dazai zama cutarwa a garekiba

Tashi Muneera tayi kana tace nizan tafi saimun hadu a Kaduna. Kinga duniyar gudu takeyi kamar yau mu uku muke tare amma kinga yau an waye gari kinyi aure gashi salma itama zatai watarana sai nikuma, hawayene yazuba a idon nabeela dasauri ta goge batare da Muneera taganiba
Maganarki gaskiya ce Muneera Allah yasa mugama lafiya barin miki rakiya, gaba Muneera tai tana fadin Ameen. kibarshi kawai nagode.

A gidanso Muneera babu wanda besan salma da nabeela ba koda tasanar dasu zataje bikin salma ba'a hanata ba, saidai anyi mata nasiha akan ta suturta jikinta kuma takama kanta domin ita matar aure ce.

Da misalin karfe hudu Muneera taisa gidanso salma tasan gidan dan sunsha zuwa ita da nabeela da salma. Muneera taji dadin yanda mutan gidan suka amsheta ton balle mama sai nan'nan take daita abinda yabata mamaki kowa yanda yaya sa'ad yake zuwa idan sun hadu yaita janta da hira yana wasa da dariya, zuwan Muneera yasa salma tasamu yanci Brothers dinta suka fara sake mata fuska wayarta da suka amsa sun maida mata saboda hidimar biki duk inda zasuje driver yake kaiso.

A ranan da Muneera tazu salma tafara amfani da maganin matse data kawu mata, memo da set din tularen wuta Muneera tabama salma a matsayin gift, tayi murna sossai kuma taji dadi

Memo dinne rige a hannunta karanta sunayanso da aka rubuta tayi kana tace hmmm auren dole kenan da auren soyayya ne aida hoto na dana mijina za'asa, murmushi dauke a fuskar Muneera sanan tace ummusalma kenan idan baki saniba ai wani auren dole yafi auren soyayya lasting dakuma albarka saboda iyaye kikaiwa biyayya nidai abinda nakeso dake shine ki dage kicigaba da amfani da maganin'nan

Insha'Allah Muneera ai bazanyi wasa ba, yauwa nace yaushe zamu kuma school?
Saura 3weeks
Hmm ok Allah ya nuna mana
Ameen

A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yau auren salma saura 10days. Nabeela tai anko da kudinta bata tsaya mijinta yai mata ba batama sanar dashi maganan bikin ba daman yau ta yanke shawaran sanar dashi.

Zaune yake a dining bayan tagama serving dinshi itama zama tai tanacin abinci... Shiru ne ya ratsa tsakanin'so
Gyaran murya tayi kana tace swthrt
Daga ido yai ya kalleta hade daciwa baby
Swthrt Qawata ummusalma zatai aure
Allah yasanya alkhairi abinda kenan yace
Amsawa tayi da Ameen kana tace na dinka anko yau bikin saura kwana goma ton yarage two weeks Muneera ta tafi shine nace sai yarage one week zanje karasa maganan tai dayin kasa da murya kamar zatai kuka.

Dago fuska yayi ya kalleta kana yace kin dinka anko batare dakin sanar dane maganan aure ba, saboda ke kike da ikon da kanki kinsa ma zuciyarki lallai zakije biki to madalla
Kallonshi nabeela take batare datace komai ba saboda niman zaman lafiya

Cikin sanyin murya tace kayi hakuri tonda hakan be maka dadi ba insha'Allahu zan kiyaye gaba, tafiyar tawa zata kasance ranan alhamis

Aje spoon yai hade da kallonta daka bisane yace baby babu wane bikin dazakije dama a cikin garin bauchi ne zan iya yarda kije amma har kaduna gaskiya ban amince ba yarinyar da batazu bikin ki ba.

Rai a bace nabeela tai magana cikin daga murya
Baka isa ka hanine zuwa bikin salma ba... ina dalili dazaka namin kulle bane da ikon zuwa wane guri ko sha'ani akeyi a family dinmu baka barina naje idan ko kabarne to saika hadani da excord, wallahi nagaji sanan da kakeciwa batazu aure naba ai rashin lafiya tayi toina ruwanka da wanan ma? karka kuskura kace zaka shiga tsakanina da kawayena domin tamkar yan'uwa na jini suke a gurina ton kafin nasanka nake tare dasu.

Daka mata tsawa yai hade da nunata da yatsa yana fadin waya fadamiki mace namin tsawa?
Kinci sa'a ina kaunar'ki da badan hakaba dana kowa miki hankali, da girmana da mutuncina da arziki ki tsaya a kaina kina dakamin tsawa, karasa maganan yai daciwa bari kiji nafada miki wallahi, wallahi, wallahi banyarda kije bikin ba yana karasa magana yadau key mota zai fita

Shan gabanshi nabeela tayi hade dasa hannu biyu a waist dinta sanan tace dama haka namiji yake?
Wallahi kabani kunya danasan haka halinka yake da banyin kuskuren auren kaba

Nunata yai da key din mota yana fadin karda ki manta taimaka miki nai na aureki ina sane ban mantaba wane dan iskan kika bama budurcinki acan titi nikuma na taimaka miki na aura raguwar titi, aikinga dole nadinga miki kulle gudin karki koma ruwa a kawumin dan shege dan wane a sunan dana... dan haka babu wane kaduna daza kije.

Hawaye kezuba a idonta hade dawani irin baqin ciki zuciyarta cike da dana sani akan rayuwar datai a baya shiya mamaye mata zuciya lokaci daya takasa furta wata koda kalma daya ce.

Kauciwa yai zai wuce ta gefenta tare shi tayi hade daciwa idan ne yar iskace kaima dan iskane dukda kana tagaman bakai kai disvirgin dina ba, na tabbata Allah kadai yasan yaran mutane daka bata sai yanzu nake yarda da maganan matarka. Bata karasa magana ba ya hankada ta gefe kan kujera ta fada tim.

A tsawace yadu6eta yace ne zakima rashin kunya yar iska mara tarbiyya wace bata fito gidan mutuncin ba wacce bata samu tarbiyya arziki ba iyaye sunyi sake kin lalace kinzama karuwar gida.

Be karasa maganaba ta daukeshi da mari har guda biyu kana ta nunashi da yatsa tana fadin akule dinka niba irin macen dazata dauki raini agun na miji bace, karda ka kuskura kasa iyayena a cikin zaginka domin basa da laifi ko kadan akan lalaciwan tarbiyya ta, duk abinda na aikata sanadin *ZAMAN HOSTEL* ne karasa maganan tai da kuka.

Saboda takaici dakuma mamaki Alhaji rige kumatun'shi yayi yana kallon nabeela domin ya manta rabon da'a mareshi tabbas yakamata yadauki babban mataki a kanta, fincikota yayi sanan yashiga dukanta kuka take tana ihuuuuuu dukanta yake hade da takata yana fadin lallai kincika karuwa kin zageni na daga miki kafa batare dana dauki matakiba wato shine kika mareni saboda rashin tarbiyya zaki nunamin halin yan tasha, da mutuncina da arzikina kinyi kadan ki wulakantani ayau idan naga dama zan aure irinki uku

Dakyar nabeela tasamu ta gudu. dakinta ta shiga hade dasa key jingina tayi a jikin kofa hade da sulalewa kasa tazauna kuka takeyi daka daki tana jiyu sautin muryanshi da yake dura mata zagi, saida ya zageta iyasan ranshi sanan yafita.

Keep following me i need more and more comments read and share😘😘😘
💖💖💖💖💖💖

*ZAMAN HOSTEL💞*

💖💖💖💖💖

STORY
AND
WRITTEN BY

RAHEEMA🔥

DEVOTED TO👇🏻
(YUSUF)💋

Dedicated to *UMMIE JAURO* yar amanan Raheema kenan😃
Ina miki fatan alkhairi tare da godiya mai dumbin yawa Allah yabar kauna tawan🙌🏻

*YAR ZINA CE*
(Kaddarar Iyayyena)

Story and written by
*MUNEERA*

Masoya karda kubari a baku labarin book din nan wanda zai fito nan bada dadewa ba ya kunshi abubuwa da yawa sanin kankune marubuciyar tana da hazaga da basira karda ku bari a baku labarin karda ku manta da sunan *YAR ZINA CE*
(Kaddarar iyeyyena)

🅿43-44

Kawayenta yan kai amarya su biyar ne daka Muneera sai kareema a cikin yan school dinso, sai wata childhood friend dinta ramatu sauran kowa duk cousins dinta ne

Yan'uwa da abokan arziki sunyi mata nasiha sossai, bayan anfito daita daka dakin daddy gurin mummy aka nufa daita

Kanta a sunkuye hulan alkyaba dake sanye a jikinta shiya rufe mata fuska
Allah yasanya miki albarka nabeela, duk wane abinda yakamata nafada miki yan'uwa da abokan arziki sun fada miki, amma bazan gajiya gurin fadamiki kiye hakuri, kiye hakuri, kiye hakuri, rayuwar aure tabbas saida hakuri koda saurayi kika aura balle kuma mai mata, idan kina niman soyayya mijinki to ki kula da yaranshi ki rigeso da zuciya daya karda kizama mai yawan complaning akan komai ki iya harshenki kizama mai tauna magana kafin ki furta. Allah yayi miki albarka tashi kitafi.

Kuka nabeela tasa hade da rungume mummy itama mummy kuka takeyi duk yanda taso ta daure ta gagara, haka dai aka lalashi nabeela sanan aka fita daita

Bawanda zai kwana a gidan amarya, tsofafin da suka kawu nabeela sukam sunkuma gida, kawayen amarya ne sukaqi tafiya sai anyi siyan baki zasu tafi... Shiru shiru har shadaya da rabi ba ango ba alaman'shi, Muneera ce tadau wayarta hade da rubuta sanan ta migama nabeela
Nabeela kinga haryanzu angon naki yagi zuwa gashi dare nayi...

Bayan ta karanta saita rubuta wallahi kowa Muneera aiko idan basuzo ba karda kuje koina aiwanan wulakancine ko zaki kirashi?

Kiranshi Muneera tayi a waya ringing daya wayar tayi saiya dauka
Hlo
Muneera daman yanzu zan kiraki, kufito waje na sallame ku, kindai san niba karamin mutum bane kuma wanan bashine aure na nafarko ba, saboda haka kufito waje na sallame ku, kashe wayan Muneera tayi batare da tace komai

Nabeela ce ta kafeta da ido, maida hankalinta tai gurin sauran kawayan sanan tace uhmmm yan mata ango na waje yace mufita zai sallame mu, tashi sukai suna fadin duk zaman damukai wato bezu da abokai ba uhmm lalle

Fatan alkhairi sukaima nabeela sanan sukai waje, suna fita Muneera ta dube nabeela tace to Qawata Allah ya bada zaman lafiya ina miki fatan alkhairi, Allah ya kauda duk wane sharri dakuma tashin hankali a cikin zaman auren ki, hunging dinta nabeela tai tana fadin Ameeen Muneera nagode sossai, Allah yasaka miki da alkhairi yabaki miji nagari.
Chapter 21 · 0% Book details