free

Zaman Hostel Part 1 Complete Hausa Novel

AuthorJamila Umar

22,109 views356 downloadsEN language
BOOK INFORMATION

Details

Available
Category
Love Stories
Format
TXT
Access
Free
Reader
Prepared
Reading parts
43 chapters/parts
Published
Aug 27, 2025
Updated
Oct 25, 2026
BOOK IDENTITY

Author & publisher

ABOUT THIS BOOK

Description

Unexpected News
 
Zaune take akan gado hannunta riqe da handout tana karatu sosai da natsuwa. Wayarta ta fara ringing, cikin sauri ta dauka ta ce:
 
“My one and only umma, kin wune lafiya?”
 
Umma ta ce, “Muneera kizo gida yanzu. Muna da bukatar ganinki, akwai magana mai muhimmanci.” Sai ta kashe wayar.
 
A rikice Muneera ta mike, tana addu’ar Allah yasa lafiya. Da hanzari ta shafa powder, ta fesa turare, ta dau mayafi da jaka ta fita. Tana barin hostel budurwar da ke shirin shigowa ta tambaye ta, “Muneera ina zuwa haka?” Amma bata tsaya amsa ba, kawai ta furta a hankali: “banza kawai sai shegen tambaya”.
 
Da ta isa gida, sai ta tarar da mahaifinta, mahaifiyarta, da kuma yayansa Baba Bello da matarshi. A mamaki ta durkusa ta gaishe su, ta zauna.
 
Baba Bello ya kalle ta da natsuwa ya ce:
“Muneera, ki buda kunnuwanki da kyau ki saurare ni. Abinda muka zaba miki ba cutarwa bane sai dai alheri. A yau na daura miki aure da Mansur.”
 
A zabure ta mike tana ihun:
“Ne! Aka daura min aure da Mansur kuma?” Sai ta fadi kasa luuu.
 
Umma da Inna Talatu suka riketa da ruwa, ta dawo da numfashi, hawaye na bin fuskarta.
 
Baba Bello ya ce, “Maganar aure ce ta firgita ki har kika suma? Ko farin ciki ne?”
 
Da kuka take cewa:
“Abba wai dagaske aka daura aure na? Ba zan iya gaskatawa ba!”
 
Abba cikin tausayi ya ce:
“Eh, Muneera. Baba Bello ya daura aure naki da Mansur bisa dalilai masu karfi.”
 
Ta rarrafa da kuka:
“Don Allah ku fada min dalilin. Me nayi da kuka hukuntani da aure cikin sirri?!”
 
Baba Bello ya yi murmushi:
“Babu laifin da kika yi. Mansur yana sonki, iyayansa kuma sun bukaci aure. Kuma shi kansa Mansur yace babu wadda yake so sai ke. Mun daura aure cikin sirri, daga baya za’a sanar da duniya.”
 
An tashi da taron da albarka. Muneera ta koma kan cinyar Umma tana kuka, Umma na shafa kanta tana rarrashi.
 
Tears of Muneera
 
Cikin kuka ta ce:
“Umma, na lura Baba Bello da matarshi basa kaunata. Me yasa zasu aurar da ni a sirri? Ni ban taba kaunar Mansur ba. Auren sirri ne, ba tuntubi na, ba shawara, ba so na!”
 
Umma cikin tausayi ta ce:
“Haka Allah ya tsara rayuwarki. Ki dauki abin da ya same ki da biyayya. Kar ki manta, a wannan zamanin da yan mata da yawa suna neman aure sai wanda Allah ya yi wa rabon miji nagari. Ki yi hakuri, aure arziki ne.”
 
Sai ta koma hostel zuciyarta cike da kunci. Kan gadon hostel ta fadi, babu wacce daga kawaye ta kula. Sai Nabeelah ta ce:
“Babe, what’s wrong? You’re so silent.”
 
Muneera ta girgiza kai kawai ta ce, “Komai normal,” ta fice daga dakin. Bayan ta fita, Salma da Nabeelah suka kwashe da dariya suna cewa:
“Ban gane wannan Muneera ba, kamar mai iska kullum tana daure fuska.”
 
Who is Muneera?
 
Muneera ’yar Ibrahim da Aisha ce. Mahaifinta na da mata uku, mahaifiyarta ce ta biyu. Ta taso cikin gata, domin mahaifinta mai arziki ne.
 
Chocolate colour ce, ba gajera ba kuma ba doguwa sosai ba. Ba mai kiba ba, amma tana da hips da kyau. Hancinta dogo, lips dinta karami, komai nata daidai ne. Ita ce ta biyar a dakinsu, tana da kanne biyu. Yanzu tana shekara 19.
 
Ta tashi a cikin gata, daga primary zuwa boarding school. Mahaifinta ma ya taba baiwa Bello (yayansa) kyautarta domin bai da haihuwa. Duk hutun makaranta tana gidan Baba Bello kafin ta koma hostel.
 
Muneera haifafiyar Bauchi ce, yanzu tana karatun Mass Communication a ATBU Bauchi, tana zaune hostel da kawaye uku: Nabeelah, Kareema, da Salma.
 
Who is Mansur?
 
Mansur dan Abubakar da Ameena ne. Mahaifinsa babban dan kasuwa ne, mai arziki. Mansur shi ne na uku a gidansu, yana da kanne mata biyu: Rukayya da Hajara.
 
Shi pilot ne, kullum tafiya kasashe daban-daban. Tunda ya fara ganin Muneera ya fada mata yana sonta, amma kullum tana wulakantashi. Sai dai zuciyarsa bata daina son Muneera ba.
 
Lokacin da mahaifinsa ya bukaci ya fito da matar aure, sai ya fada masa yana son Muneera. Mahaifinsa ya dage akan cewa dole ya aure ta. Haka aka daura auren cikin sirri.
 
Life in the Hostel
 
A hostel, kawayen Muneera suna da bambancin hali.
 
Salma: Asalinta yar Kaduna ce, auta a gidansu, fariyar mace mai jiki daidai.
 
Nabeelah: ’Yar Bauchi ce, bakar fata amma mai kyau sosai, hanci da manyan ido, ga jiki mai kyau.
 
Kareema: Ba kamar sauran ba, ta fi su da kudi, da wayoyi, da kayayyaki. Ita ce ke jan hankali sosai.
 
 
Wata rana Muneera ta dawo daki cikin jump suit, ta tarar da Kareema sanye da doguwar material mai matse jikinta tana feshe turare. Salma ta yi tsokaci, Nabeelah ta yi dariya.
 
Muneera cikin mamaki ta ce:
“Rayuwar iskanci da shigar banza ce kuke so? Abeg you guys should be content with what you’ve.”
 
Salma ta saki tsaki, amma ba ta ce komai ba.
 
Daga nan suka fita waje don haduwa da wani saurayi mai suna Lukman. A lokacin wata sabuwa soyayya ta fara bayyana tsakaninsu, musamman a zuciyar Salma, wanda hakan zai haifar da sabbin rikice-rikice a rayuwar su gaba.