← Book details Zafin Wuta Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 13

Sashe 8

Zafin Wuta Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ba tare da na kalli gefen da yake ba na ɗago da kaina sannan na zira farar ƙafata ƙasa na sauka zuwa gaban basket ɗin, a faranti daban-daban nai niyyar zuba manah, amma sai ya dakatar da ni da umarnin in haɗe waje ɗaya, ban musa ma shi ba nahaɗe kamar yanda ya buƙata, harna yunƙura da nufin in hau da abincin kan gado sai ya dakatar da ni, ajiyewa na yi da sauri ganin ya tashi zaune ahankali, ganin abin da yake shirin yi sai nai ƙoƙarin dakatar da shi, amma ya girgiza min kai, badan naso ba na taimaka mashi, a mamakina bayan na ziro mashi sa ƙafafuwanshi ƙasa, sai naga ya dafa ni da kyau ahankali cikin dabara ya miƙe tsaye, amma sai jikinshi ya kama karkarwa zufa ta dinga keto mashi, da sauri na yunƙura in maida shi sai ya dakatar da ni, cikin dabara ya zame ya zauna akan carpet sannan ya muskuta dan ya jingina da bango, da sauri na suri pillows na saka mashi a baya tare da jera ma shi sannu, rigar jikina na saka tare da tafa kafaɗunshi na ding goge mashi zufar da ta tsatsafo mashi, murmushi ya sakarmin me taushi bayan na gama a hankali ya furta.
"Thank u dear."
Mayar mashi da martanin murmushin na yi nima sannan na curo vowl na wanke ma shi hannayenshi na bashi ruwa ya kuskure baki, toilet na je na zubar da ruwan nima na wanko nawa hannun sannan na dawo da janyo plate ɗin abincin na jere su a tsakaninmu.
"Spoon."
Ya furta yana kallon yanda na saka hannuna ina shirin fara kwasar ganimar girki.
Murmushi na saki sannan na ce.
"Aiga spoon nan a jikinka, yau da hannunka me albarka zaka ci abinci babu wani spoon."
"Da hannu kuma, gaskiya bazan iya ba."

"Sai de ka kwana da yunwa." na faɗa tare da fara aika loma abakina ina lumshe ido.
Kallon yanda nike taunar abincin kawai ya ke yana murmushi gami da haɗiyar yawu, dan favourite ɗinshi aka yi yana son kebab, share shi nai na nuna kamar baya wajen, tsintar muryarshi ni yana faɗin.
"Please tunda ban iya ba ki bani da naki hannun zanci."......✍️

LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.

9136291920
MARYAM UMAR
OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA

BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘

WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK FOUR 4
CHAPTE 44.

بسم الله الرحمن الرحيم.
Buɗe baki nayi zanyi magana kawai ya janyo ni gaba ɗaya na, saura kaɗan in zubar da abincin, daram na zauna akan ƙafafuwanshi, sai yai amfani da ƙafarshi ya turo plate ɗin gabana, a saitin kunnena ya raɗa min.
"Kinsan Allah mudin baki bani da hannunki me albarka ba sai de daga ni har ke mu kwana da yunwa dan kuwa kema bazan bari kici ba." ya faɗa tare da saka yatsun da nike cin abincin da su yakai bakinshi ya tsotse tas, sannan ya kashe min ido tare da nuna min plate da ido sai kuma ya buɗe baki.
Haɗiyar tsinkaken yawu na yi, sannan na kalli yatsun hannuna wanda nike jin danshin lemar yawunshi a kai, kamar marar laka na fara ɗibar abincin a slow na mufi bakinshi, buɗewa ya yi idonshi a cikin nawa, yana aika min da rikitaccen kallo wanda ke hautsina duniyar zaman lafiyata, ba tare da na ankare ba, sai gani na yi mun cinye abincin tas, idan na bashi a baki baya cinyewa duka sai ya juyar da hannuna zuwa bakina, sai ya tabbatar da na cinye tas sannan ya sake kaimin hannu zuwa cikin plate, mixs fruit juice ɗinma atare muka shanye abinmu, idan ya kurɓa sai ya maido zuwa bakina haka muka shanye na cikin cup ɗin tas, wani irin ƙoshi wanda zan rantse ban taɓa yin irinshi ba naji na yi, ba abincin bane ya ƙosar da ni, salon da yah Fauzan ke amfani da shi wajen ciyar da ni haɗi da tattausan sassanyan murmushinsa sune suka ƙosar da ni, shiru ne ya gifta a tsakaninmu bayan kammala cin abincin, babu me magana a tsakaninmu sai satar kallon juna da muke yi, ko kuma ince satar kallon yah Fauzan da nike yi, bana jin tun da na zauna wajen ya janye idonshi akaina na tsawon minti biyu, duk sanda zan kalle shi idomshi na kaina, ina jin na takura sosai da yawan kallon da yake min, amma kuma banaso inga ya daina kallona ina jin daɗin hakan sosai da sosai.

Bayan kwana biyu.

Zazzaune muke akan dinning bayan an kammala break fast, Mommy da Papah ne ke tsara yanda tafiyarmu zata kasance zuwa India dan yiwa yah Fauzan aikin fata, jifa-jifa Sulaima ke tsoma musu baki, yayinda ni kuma zama wajen ya takurani sosai, ina so in tashi amma ina jin nauyin su Mommy suganni na yi hanyar ɗakin Fauzan, ƙarar buɗe babbar ƙofar shigowa parloun ce ta tattaro hankulan mu.
Fara doguwar matashiyar mace me aji da ji da kai ce ta fara shigowa hannunta riƙe da trowly, sai wata wacce zata kirme ma ta da shekaru ba masu yawa ba a bayanta, amma ita baƙa ce sosai, daga ƙarshe kuma wadda nike kyautata zaton mahaifiyarsu ce duba da yanayin kammani da kuma shekarunta, itace ta fara takowa zuwa cikin ɗakin tana ƙarewa komi na ciki kallo a ɗage, sai wani yatsina ta ke yi kamar wacce ta ga kashi.
"Sweet mother inlow, i miss u." fara doguwar matar ta faɗi tare da ƙarasowa ta rungumi Mommy tabaya tare da bata kyawawan sunba.

"Moon saukar safiya kuka yi kenan." Mommy ta faɗa tare da janyo hannun Moon ta zagayo da ita kujerar getenta, zama wacce aka kira da Moon ta yi, sannan ta marairaice fuska tai kwalkwal da idanu alamar gab take dayin kuka.
"Please Mommy, for give me😔."
"No kar muyi haka da ke kuma, bana so kuma kin sani so take care." Mommy ta faɗi tare da ɗan bubbuga kafaɗun Moon.

"Zamu iya komawa muda ba'a maraba da zuwanmu ko." Mom ta faɗa aɗan hasale, zuciyarta baƙi ƙirin saboda tsabar baƙin cikin abin da Moon ta yi.
Taɓe baki Jaleela ta yi tare da wurgawa Moon baƙar harara wacce ta nuna kamar batasan da zamansu ba ta maida hankali wajen gaisar da Papah da Hajjo, su kuma suka amsata cike da kulawa.

"Hajiya Zulaihad, ƙaraso mana, murnar ganin ƴata ce ta ɗauke min hankali, you are wellcome." Mommy ta faɗi tare da nunawa Mom wajen zama.
"Mtswwwww, aikin banza kenan." Jaleela ta faɗi tana aikawa su Mommy wani kallo a kaikaice.
Ban san lokacin da bakina ya kubfe ba wajen faɗin.
"Wa ta sabuwa inji ƴan caca." sai da Sulaima ta taɓo ƙafata ta ƙasan dinning sannan na lura da afili nai maganar, murmushi ta sakar min nima na mayar mata, ta ɗage min gira alamun yadai, nima na maida ma ta tare da watsa hannayena alamar nothing.
"Wow so preety, Sulaim a ina kika samu wannan beatiful Queen ɗin."
Moon wacce ta faɗi kyawuna na kashe ma ta ido zan tun zamanta a wajen take zuba surutu sam bata lura da ni ba.
Hakanan na ji Moon bata wani burge ni ba, saima wani haushinta da bansan ko na miyeba ke lulluɓe ni.
"Hi beautyfull, how are you?." ta faɗa har lokacin murmushi kwance akan fuskarta.

Haɗiya yawu na yi sannan na amsa ta a sanyaye, yanayin yanda nai maganar sai da ya sake burge Moon wacce lokaci ɗaya ta ji na bala'in burgeta.
Ban ankare ba sai ganin Mom da Jaleela na yi sun ƙaraso tare da zama kujerar da ke kusa da ni suka saka ni a tsakiya, ban yi nauyin baki ba na gaishe da su a jimlace tare da yin baya da tawa kujerar na miƙe tsaye, sai jin muryoyinsu Mommy nai na tambaya ta.
"Mubeenah, ina za ki je kuba kina tsaka da break fast."
Ban san lokacin da na shagwaɓe fuska ba sannan cike da girmamawa mace.
"Mommy na ƙoshi wallahi, zanje in haɗawa yah Fauzan maganinshi saura na yau kawai ya rage bai kamata ace nayi jinkiri b."
"Jeki kiyi aikin ladarki kinji rabu da waɗannan ƴan jaridar."
Papah daya fahimci so nike in tafi ya faɗi yana sakar min murmushi, cike da bashi girma na amsa sannan na wuce, ina jiyo muryar Hajiya Zulaihad na faɗin.
"Ita kuma wannan uwar feleƙe da iyayinfa a ina kuka samo ta." Wannan karon Hajjo ce ta bata amsa da faɗin.
Ƴa daga Allah kenan, yarinya farar haihuwa, ai wannan da kike gani yanzu kaf ahalinan alfahari muke da ita, bakin gwargwado akwai tarbiyya da girmama mutane." Hajjo ta faɗi ranta fes.
"Lah Mom bakusan yah Fauzan ya...."
"Zaki maida hankali wajen yin abin da ke gabanki kokuwa za ki tsaya surutun banza da wofi." Mommy ta katseta muryarta cike da gargaɗi, tuni Sulaima ta hango laifinta nan da nan ta gumtse bakinta taci gaba da aikawa cikinta lafiyayyun kayan break fast.
Chapter 8 · 0% Book details