Sashe 5
Zafin Wuta Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ke ƴar iskar yarinya kangararriya, dan ubanki zauna ki kama ma ta, maza-mazaa tun kan in rusunar da ke da belt."
Jin abin da Abba yace ya saka na suri bokiti, amma naƙuri aniyar bazanyi wankin da kyau ba, hakan ce ta faru dana tsoma kayan sai infitar in aje a ƙasa, nan da nan kuwa na gama na shanya, umma bata fito ba sai bayan wasu daga cikin kayan sun bushe, ranta fes ta kwashe zuwa ɗaki ta jibge, da sauranma suka bushe haka ta kwashe ta tsauna cikin jaka ta aikawa matar azo a amshi kaya, da fara'a matar ta zo sai yaren yarbannci take cakuɗawa da hausa, bayan ta idasa biyan Umma kuɗin wanki aka ɗauko ma ta, sai tace ba zata ɗauka ba sai ta linke, Umma harda shirin tayata linkewa, duk kayan da matar ta baibata sai tagansu duƙun-duƙun babu wanki, sai da ta baibaita kayan kaf sannan ta tashi tana dukan cinya gami da yiwa Umma kwakwazo akan bata yi mata wanki ba, nanfa Umma tashiga walimar idanuwa dan itama dai ta duba kayan dakyau, kuma taga basu wani wanku ba sai ma taso da ɗauɗa da aikai, haƙuri tashiga bawa matar amma kamar tana tunzirata, ana haka sai ga Abba ya shigo hannu na dukan cinya, jin hayaniya ya sakashi hanzari shiga ɗakin, nan Umma tai ma shi bayani akan abin da ya faru, aiko ya harzuƙa ya saka Umma ta bawa matar kuɗin wankin data bayar ta kwashe kayanta tana ta faman mita, bayan ta tafi ya dirar min ina ɗakin Mama ina sallah, baice da ni komi ba illa jan hanuna ƙiiii ya fice da ni, a daidai wani layi inda keda shaguna ya tsaya tare da shiga wani shago sukai magana da me shagon sai ya fita ya kuma fizgata, bayani Madom ɗin ta shiga yi man akan yanda ake siyar da kaya, wani na fahimta wani ban ganeba, sai bayan ta gama ne ta ɗauki kuɗi ta bawa Abba.
"Kika wani tsare ni da ito kina min kallon tuhuma, to bara kiji daga yau kece za ki ɗauki nuyin ciyar da kanki da kuma gidan baki ɗaya, idan ba haka ba sai de ki ficemin daga gida baki ɗaya, dan bazan zauna da ke ba, ai nayi ƙoƙarima ita uwarki tun da ta damƙa min ke bata sake yarda mun haɗu ba, dan baƙin hali da mugunta wato ta samu ta rabu da jangwam dole tai nesa da ni, idan kina son zama a gidana dole ki yi zaman shago ana biyanki kullum idan kuma ba haka ba idan kin fice daga nan ki kama hanya kiyi tafiyarki ko ƙofar gidana na ganki saina kusa halaka ki ƴar banzar yarinya me baƙin hali irina uwarta." bai jira komi ba ya fice bayan ya gama yaɓamin munanan maganganu.
Ganin zan iya faɗuwa daga tsayen da nike ya saka na durƙushe a wajen ina kuka marar sauti, Madom ɗin shagon ce tashiga yimin kwakwazo akan zan tara mata mutane, nan ta tasa ni gaba tasaka na wanke fuskata ta zauna dakanta ta gyaramin ita, nan da nan na fito fes da ni, sai ta bani takalma kasancewar bani da su, ta kama hannuna zuwa waje ta ce in zauna, nan ta sanar da ni ta canza shawara ita zata zauna a ciki ni kuma injanyo costomers, abin dariya ya bani, musamman data kwatanta min yanda zan dinga cewa, aiko hakan ce ta faru, du wanda yazo wucewa zan taryeshi da murmushi imfaɗi yanda ta ce sannan inkaishi shagon, kan kace me, tuni samari da magidanta sun cika shagon anata shige da dice, sai da marice liƙis sannan Madom ta sallame da kuɗi masu kauri harda kayan cinye-cinye a leda tana ta yimin godiya akan yanda na janyo mata ciniki sosai.
Lokacin dana koma gida cike da farin ciki na shiga ɗakin Mama ina bata labari akan yanda aikinda Abba ya samomin yai min daɗi, sai naga ta saki ranta ba kamar yanda na isketa a damuwa ba, nan ta bani busashiyar shinkafar da Umma ta liƙa can ƙasan kwano da sunan tawa ce, cewa Mama na yi ai naci abinci can wajen aiki, na fito da kuɗin wajena na raba biyu na bata rabi ni kuma na riƙe sauran da niyyar zan haɗa su da sauran wanda gare ni inje inso ƴan saye-sayen kayan amfanina.
Bayan munci abincin dare Abba ya sanar da ni zan komi ɗakin da ke kusa da Mama, bazan sake kwana a ɗakinta ba dan yanzu na girma, shi zai dinga kwana a ɗakin Mamar, naji babu daɗi amma sai na yi tunani ƙilan damace zan damu ta gyara tsakanina da ƴan uwana, sai naji hankalina ya kwanta, amma da aka wayi gari na gyare ɗakin, Mama ta bani katifa na saka na jere kayana ina jiran su Yaya Summaya amma na ji shiru, sai hankalina ya fara tashi, na fara tunanin ko nikaɗai zan zauna a ɗakin, har naje shago na ƙarashe wunina acan na dawo gida gab da magrib, babu su babu kayansu, sai na shiga ɗaki Umma ina tambayar sai yaushe zasu dawo, amma sai suka bini da dariyar rainin hankali gami da yaɓamin baƙaƙen maganganu Yaya Sumayya harda faɗin.
"Lallaima yarinya, mu ai ƴaƴan so ne, muna nan gaban uwarmu babu wanda ya isa ya rabamu da ita, ke da taki uwar ta manta da ke sai kije ki ji da zaman kaɗaici."
Ban taɓa bawa kaina damar tunani akan mahaifiyata ba sai a ranar, duda Mama ta koyar da ni yi mata addu'a badan ta rasu ba, ban musa ba haka kullum nike yi ma ta addu'a amma ban taɓa jin ina so in kusantu da ita ba sai a wannan ranar da nai kwanan kaɗaici, ga dugu, ga zafin zuciya na maganganun da Abba ke jifana da su, saboda rashin samun isashen barci a washe gari makare na je shago, da yake Madom ɗin ji take da ni saboda yanda nike janyo mata hankalin costomers sai batai min wani faɗa ba, sai ma tayin kakkauran lafiyayyen tea da soyayyen kwi da tai mani, da farko ƙin amsa na yi, amma sai data takura ni na amsa, naci nai nak ina hamdala, duda gida Abba baya barinmu da yunwa du yanda zai yi sai ya yi ya nemo mana abin da zamu ci, sai naji nayau ɗin yayimin daɗi sosai, haka na zauna ina yiwa mutane sannu d zuwa fuskata da fara'a duda iya fuskar ne batakai zuci ba, amma yanda maza ke shagala da kallona har wasu na tuntuɓe ko kuma su na tafiya su na waiwayena sai abin ke bani dariya, wasu kuma dan kawai inyi magana suji muryata ya saka suke zuwa wajen, da naga ana samun ciniki, kuma kullum banda kuɗin Abba ta na ware wasu tace nawu ne kusan dubu biyu, sai na fara yin cincin da haƙorin madina ina sakawa a cikin ɗan farin bokiti ina ajewa gabana a wajen shagon, aiko nan da nan yake ƙarewa musamman yanda nayisu da daɗi sosai, anan na tara ƴan kuɗaɗena na bawa Mama ta sayomin yadin hijabai sabbi dogaye har ƙasa kusan guda huɗu, da na sake tara wa ta ribar sai na bayar ta siyo mana takalma ƙafa biyu ni ɗaya ita ɗaya, a hankali na fara taya kaya da sauran abubuwan buƙatu, alfarmar zuwa makaranta na nema a wajen Madom sai ta maida min zan dinga zuwa da safe dai intafi da azahar in dawo da magrib har sai lokacin tashinta ya yi, ban musa ba muka tafi akan hakan, nakoma makaranta naci gaba da harda ga sabbin litattafai da malamai kemin ƙari ni kaɗai, saboda sun fahimci yanda nike da naci dason karatun, sai suka tallafamin na samu karatu bakin gwargwado.
Wa ta rana bayan na dawo daga shago na iske Abba da wani abokinshi zaune a ƙofar gida su na gaisawa, har zan shige ganin yanda abokin Abban ke wani bina da kallo tun daga sama har ƙasa, sai kuma na tsaya na gaida su, baki washe ya amsa ina jinshi yana tambayar Abba ni ƴarshi ce, banji amsar da ya bashi ba na shige gida raina fes, dan sabbin fitulu na siyo guda uku ni ɗaya Mama ɗaya, ɗayar kuma nakaiwa Umma, kamar ba zata amsa ba sai kuma ta amsa amma sa wani yatsina ta ke, ficewa nai na barta da halinta na shige wajen Mama muka ɗan taɓa hira kafin Abba ya shigo ya fatattake ni....✍️
LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.
9136291920
MARYAM UMAR
OPAY
TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.
🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥
LABARI ME CIKE DA
BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘
WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.
MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK FOUR 4
CHAPTE 42