← Book details Zafin Wuta Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 13

Sashe 11

Zafin Wuta Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

بسم الله الرحمن الرحيم.
"Anan duniya ban taba samun ƙawa wacce nike jin na ɗauketa kamar ƴar uwata ba irin ke, please lovely frien tell mi whats wrongh, kinga yanda kika rame kuwa, ki sanar da ni damuwarki, dama ina ji ajikina ko kowa ya gujeni ke kina tare da ni, nasan cewa zakizo ki nemeni da kanki, a jikina nike jin hakan." Sadiya ta faɗi tana sharewa Fateema Abbas ruwan hawayen dake shatata daga idanuwanta.
"Ina ciki tashin hankali, bana cikin walwala kusan shekaru ashirin kenan, ko barci nike ruhina bai taɓa hutawa da tunanin zalincin dana biyewa zuciyata na aikata ba, idan yau akace miki na faɗi na mutu to baƙin ciki da ciwon zuciya ne suka kashe ni, dan girman Allah ki yafemin Sadiya nasan na cutar da ke cutarwa me yawa azaman da mukai tare, tun muna school nike cin amanar ki, nayi nadamar mugayen halayena, dan Allah ki yafe min ƙawata."
Da kyar takai ƙarshen maganar saboda kukan da yaci ƙarfinta, itama Sadiyar hawaye ta ke gami da girgizawa Fateema Abbas kai, dan kalamanta sun matuƙar karya salihar zuciyarta, nan ta rarrashi Fateemar har sai da ta tabbatar da ta daina kukan sannan ta sakata wanke fuskar harma da shafa powder da jan baki, aiko fuskarta ta fito tai gwanin kyau, sai de kallo ɗaya za'ai ma ta a gano kwantaciyar damuwar da ke danfare a zuciyarta duda ta ɗan saki ranta harma da murmushi tana yi, haka suka fito gwanin burgewa suna taɓa hira suna dariya hannayensu ɗauke da babys da suka haɗe cikin tsadadun kaya.
A kaikaice Malam ke ƙarewa Fateema Abbas kallo, yana karantar kamanni da kuma yanayinta, bai samu nutsuwa ba sai da ya ɗauke su photo a ɓoye ba tare da ya bari sun ganshi ba, Alhaji Umar na lura da shi kawai de bai nuna yaga abin da yai ba, haka Malam ya saki jiki akasha fira da shi, aitama Fateema Abbas ta saki jiki sosai da shi, basu suka tashi ba sai da marice yayi, badan Fateema Abbas ta so ba hakanan ta tashi jiki a sanyaye ta tafi gidanta, tana isa babu jimawa sai ga Lawan shima ya dawo amma taƙofar baya, kai tsaye ya shiga gidan kamar yanda ya saba, sai de yayi mamaki daya iske Fateema na jere kayan abinci a ƙasan kan carpet, ga fuskarta fal fara'a sai ƴan wake-waƙe ta ke, ƙare ma ta kallo yai ganin shigar wando da rigar da tai ya zauna ɗas a jikinta kuma ya bayyana surarta a fili, haɗiyar yawu ya yi sannan ya ƙarasa zuwa inda take yana sakar mata murmushi, bata kulashi ba taci gaba da hidimar gabanta harta kammala jere abubuwanda zata buƙata, sannan tai bisimilla tare da fara aikawa cikinta, sosai Lawan ke mamakin yanda yanzu sam bata tsoronshi, yasan ta ganshi amma ta wani maze ta nuna batasan da zamanshi a wajen ba, hakanan ya ƙaraci surantanshi na daɗin baki ya tashi ya tafi dan sam bata bashi damar da zai kulata ba, yana shige ta tattare kayanta kaf kamar tasan shirinshi ta shige ɗaki ta kulle tare da barin key ɗin a jiki.
Da sauri Lawan ya watsa ruwa ya fito a gurguje dan yanda yaga Fateema cikin shigar riga da wando yanayinshi ya sauya, cikin shauƙin sha'awa gami da kewar irin ganimar da yake samu a wajenta ya nufi bedroom ɗinta, sai de ƙofar a kulle, yai bugun duniya amma tai banza ta share kamar bata ji shi ba, hakanan ya haƙura a hasale ya juya ya koma, du bayan mintuna sai ya fito ya sake dokawa amma shiru ahaka ya kwana ranshi a ƙuntace, ga gurguwar sha'awa dake neman illata lafiyarshi.

"To sai me, nace sai mi idan sun ƙara mashi aure, dama ai ba sonki ya ke ba, kece da baƙin nacin tsiya kika nace akanshi amma shi sam batake yake ba, bari kiji wani abu, tunda kika tsallake kika barshi lokacin da yake cikin halin ciwo, kuma yake buƙatarki daga lokacin kika fice daga ransu baki ɗaya, dama suna duba zumincinda ke tsakanin, amma tunda kika yarda kika bimu London kika barshi a halin rayuwa ko mutuwa, daga lokacin alaƙarki da shi ta yanke, zaifi maki kyau ki tattare du wani ƙulafucin so ki aje gefe kizo mu haɗa kai wajen wannan yaƙin da ke tunkararmu, dan yanzu babu ɗaga ƙafa, dolene ya fito da dukiya abamu namu kason."
Hajiya Zulaihad ta faɗi tana dafa kafaɗar Moon.
"Ya isa haka Mom, ya isa ki barni inji da gobarar tashin hankalinda ta tunkaro ni, ke kuɗi da abun duniya ya dama, ni basune agabana ba, rayuwar farin cikin da kika gaza bani ita nike so, ina son rayuwa me tsari ba irin wacce kika ɗoramu a kai tason abin duniya da kwaɗayiba, na tsani halayarki Mom, ji nike dama bake kika haifeni ba, tun daga ranar da kika tsinke igiyoyin aurena na fara danasanin saninki a rayuwata, idan mutuwa za kiyi sai dai ki mutu amma babu wanda ya isa ya hanani komawa auren Fauzan, a wajenshi ne kawai nike samu farin ciki da...."
Maganarta ta yanke sakamakon taurarin da suka gifta tacikin idanuwanta, wani shiru ya ratsa ta masarrafar jinta, kamin ta dawo hayyacinta daga suman wucin gadin da tai ta cinkayo muryar Jaleela cikin hargowa ta na faɗin.
"Ƙaryar iskanci kike Moon, da ace Mom bata haifokiba da bazakiga wancan ɗan iskan har ya ɗauke maki hankali ba, kamar yanda kike danasanin haihuwarki da tayi, itama haka take danasanin haihuwarki, da tasan zata haifo kafafiyar yarinya me azababben taurin kai irinki da tun ranar da za ki zo duniya za ta murkushe kanki min koma, kin ƙi tsayawa ki gane irin gatanda tayiwa rayurki na rabaki da ɗan waccan muguwar matar wacce kanta da ƴaƴan kawai tasani, aurene ke da shi har gaban abada, kamar yanda Mom bazata taɓa bari ki komawa aurenshi ba, haka shima waccan farar baturiyar tsohuwar wacce ke nuna banbanci ƙarara tsakanin jinita da ita sarauniyar uwarshi me juya ragamar mulkin gidan ba zata bari ya maida ke ba, gara tun wuri kidawo hayyacinki ki gane gaskiya kafin kwaɓarki tai ruwa."
Faɗin Jaleela a ƙufule, dama wuya take da Moon ganin yanda ta waresu gefe ta shige cikin mutanen gidan.
"Jaleela ina so ki sani bazan sake biyewa son zuciya irin naku in jefa kaina a alaka ba, idan zaku ku daina tsayani dan ni yanzu na gane gaskiya, bazan sake maimaita irin kuskurenda nai abaya ba sanadiyar biyewa son kanku, ku barni rayuwata ce nike da right ɗin yankewa kaina hukunci daya dace da ni, dan Allah kubarni hakanan.

WACECE MOM, KUMA WACECE HAJIYA FATIMA, SUWAYE FAMILYN SHURAIMA???.

Shuraim ahamad balaraben Saudiya ne, babban ma'aikaci ne a companyn tashe gwalagwalai, ya shahara sosai a harka gwalagwalai inda sunanshi dana mahaifinshi Haroon yai fice a gabaki ɗaya ƙasar Saudiya, suna yawo ƙasashe da dama don gudanar da kasuwanci, a wani zuwa da sukai America shi da Abu shuraim wato Haroon acan ne suka haɗu ya hadu da kyakkyawar baturiya musulma me suna Ayusha, itama suna harkar gold da mahaifinta, soyayya ce tashiga tsakanin Shuraim da Ayusha inda mahaifansu sukai farin ciki da hakan nan take suka aje magana dan sun fahimci juna, bayan ɗan lokaci ƙanƙani aka ɗaura musu aure bayan gudanar da al'adar ƙasar kowanensu, soyayya me tsafta suke gudanarwa a gefe ɗaya kuma suka haɗa kai wajen tada nasu kasuwanci, inda suka gina company nasu nakansu sannan suka nemi shares daga ƙasashe daban-daban, da taimakon Allah dana mahaifansu da yanzu suka shahara suma nasu kasuwanci ya fara haɓaka, wani wayo da sukai shine, suna siyen ɗanyan gold daga ƙananan ƙasashe da ƙananan companys, sai su sarrafa su kuma siyarwa ƴan ƙasar da suka saida musu, ana cikin haka ne suka yanke shawar gida companys a ƙasashe uku inda Nigeria ta faɗa cikin lissafinsu duba da yanda suke samun ƙaruwa sosai daga ƴan kasuwar ƙasar, basuyi ƙasa a gwuiwa ba suka tada kamfanoni a ƙasashen, ana cikin aikin ne Allah ya azurta su da samun ƙaruwar Ayusha ta haifi santalele balarabe kuma baturen ɗanta inda aka saka mashi suna Ahmad, haihuwarshi ta zo musu da goshi dan kuwa kasuwanci sai sake haɓaka yake musamman wanda suke yi a Nigeria, kamfaninsu ya amsu sosai a ƙasar, kasancewarmu masu arziƙin ƙasa, noma gami da kiwo, ayuka suka tararwa hamshaƙan ma'auratan inda yanzu zama ƙasa ɗaya ke musu wuya saboda shahara da sukai, duda suna da tarin ma'aikata kwararu masu fasaha da ƙwazo, haka rayuwa taci gaba da gara musu da tarin nasarori, Ahmad ya girma shima yabi sahun iyayenshi, yana yawan bin Shurai ƙasashe musaman ƙasar Nigeria dan sosai ƙasar da mutanen cikinta ke burgeshi, bayanshi Ayusha da Shuraim basu sake samun haihuwa ba, hakan ya saka suke tsananin sonshi, ɓangaren kakaninshima haka suna matuƙar son shi, kuma sunso ya zauna a wajensu amma yaƙi yace shidai sai iyayenshi, babu ruwansu da takura yaro sai suka kyaleshi yayi yanda yake so.
Alhaji Muhammad haifafen garin Kano ne, kuma babban ɗan harkar kasuwancin haƙar gold ne, yana aiki a Legos a manyan wuraren haƙar gwalagwalai, yana cuɗanya sosai da turawa inda shima soyayya me ƙarfi ta shiga tsakaninshi da ɗiyar oganshi.....✍️

LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.

9136291920
MARYAM UMAR
OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA

BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘

WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK FOUR 4
CHAPTE 48.
Chapter 11 · 0% Book details