Sashe 3
Zafin Wuta Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan Umma tahau masifa akan ita babu wanda ya isa yasakata shan shayi da rana, kuma dolene ya fita ya nemo abin da zata ci ita da yara dan sam bata san babu ba.
Ranar dai sai da ta ƙule Abba har sukai faɗa kaca-kaca, har maruka uku waɗanɗa sukai sanadiyar karyewar asirin da akai ma shi yai ma ta, dan takaishi maƙura, kuma ya tattare kayan shayin ya bawa Mama yace ta haɗa, cike da biyayya ta amsa tai yanda yace, bayan ya karya ya saka tai mana shimfida ni da shi muna fira ina yi mashi surutai barkatai har yai barci, lokacin da ya tashi anyi la'asar dan haka ya sake ficewa nema, bai dawo ba sai dare, nan ma Mama ya bawa ta sarrafa ta bawa kowa nashi.
Daga ranar Abbana ya koma kamar yanda yake kulawa da ni a baya, sai de hidima ba kowace nike samu ba saboda yanzu baya samun kuɗi sosai.
Babban abin da ke damuna bai wuce yanda su Yaya Sumayya ke kyarata ba, babu ruwansu da ni, idan ni naje inda suke to da kuka zan dawowa Mama wani daga cikinsu ya zalince ni....✍️
LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.
9136291920
MARYAM UMAR
OPAY
TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.
🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥
LABARI ME CIKE DA
BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘
WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.
MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK FOUR 4
CHAPTE 40
بسم الله الرحمن الرحيم.
Akwai ranar da Habiba na wasa iya kaɗai, sai nazo wajenta mukai wasan atare, mun jima mu na yin abinmu cike da jin daɗi, kawai sai ga Yaya Sumayya, aiko ta mammare ni ta kora ni, na je na faɗawa Mama ina kuka shine ta tashi ta je taji dalinta na marina, buɗar bakinta sai cewa ta yi.
"Yo ba Ummanmu ta ce mubar yin wasa da ita ba, saboda bata da Mama ba ke kika haifeta ba, kema Abbanmu ya aureki ne dan ki raineta, Ummanmu ta ce bada aure aka haifeta b...."
Zazzafan marin da Mama ta ɗauke ta da shi ne ya dakatar da ita, nan ta kwanta tana birgima haɗida kwalla ihun kuka, da gudu Umma ta fito daga ɗaki tana tambayar abin da ya faru, cikin kuka Sumayya ta faɗa ma ta komi, ranta ya ɓaci sosai sai ta juya wajen Mama tana faɗin.
"Halima kenan, badai akan wannan tsinaniyar yarinyar wacce uwarta ta biyewa Iroro sukai iskanci har aka haifeta babu aure kike dukan yarana ba, hummm to ki shirya amsar sakamako, dan wallahi sai na ɗaiɗaita rayuwar wannan shegiyar yarinyar wacce ta tsokane idon mijina, sai na yi walagigi da rayuwata ta yanda wanda zai tallafa ma ta zai yi wahala, indai ina numfashi to sai kinga wannan yarinyar acikin uƙuba, kuma ki kasa tallafarta, sai na maida ita abar tausayi wacce za'a dinga kwatance da ita, da Umma kike zancen muje zuwa."
Ranar haka Mama ta ƙarashe wuninta sukuku, maganganun Umma sun bala'in ɗaga hankalinta, dataga dai babata wa ta mafita sai ta fawwalama Allah komi, dan tasan komi zai samu bawa to muƙaddari ne daga Ubangijin sammai da ƙassai.
Watanni suka juye zuwa shekara, yayin da shekarar ta zo da sauyi me girma, ciki harda ƙalubalen da na fara fuskanta, babban abin da yafi ɗaga min hankali bai wuce yanda Abbana me ƙaunata ya juye zuwa babban mugu kuma dodo a gare ni ba, ko daga nesa na hango shi jikina ɓari ya ke, idan shi bai ganni ba ina da damar kuduwa in ɓuya, amma idan ya rigada ya ganni bani da wannan damar, dole zan tsaya har yazo ya sauke min nau'o'in mugunta da azaba.
Yanzu na girma, kuma na fara fahimtar yanda rayuwar gidanmu ta sauya salo, yanzu rayuwar ta juye min daga me daɗi sassauƙa zuwa, me azaba kamar ZAFIN WUTA, ina tsayawa inyi tinani da nazari akan yanda yanzu komi ya juye, amma sai in kasa gane komi, sai de inyi haƙuri, kullum ina tare da Mama, amma bata da damar tsoma baki ko tankawa idan anyi min wani abu, sai de ta shige ɗaki taita kuka ita kaɗai, data tafi ta barni gara ta tsaya kusa da ni tana rarrashina idan anyi min wani abin, dan Abba zaɓi ya bata, kodai ta ɗauke idonta idan akaimin wani abin ko kuma ya sallameta tai gaba, ta zaɓi zama ne dan in samu bangon da zan jingina inyi kuka, ta zauna ne dan tana min kallon wacce ta fito daga jikinta, ba zata jure tafiya ta barni ba.
Ina girma ina sake fuskantar ƙalubalen rayuwa, lokacin da shekaru suka ciki sha biyar cif, babu kalar aikin gidan na ban iya ba, dan komi ni ke yi, harda wankin Umma da ƴaƴanta, sannan in wanke na Abba, ita kuma Mama ta wanke nau da nata, daidai da rana ɗaya bata taɓa sakani aiki wanda yake na ta ba, sai de tayi ƙoƙarin taimaka min, ƙiri-ƙiri ina ji ina gani Abba ya fidda ni daga makaranta, wai bai da halin biyamin karatu shima takanshi ya ke yanzu, dama kusan Mama ce ke ɗawainiya da ni, itama kuma yanzu bata da komi, dama kayan ɗakinta ne ta dinga yiwa ɗauki ɗaiɗai tana siyarwa ta biya min kuɗin makaranta, to tinda ta samu ta ƙuƙuta da kyar ta biya min har na gama secondary school sai ta tsaya anan, banda yanda zanyi sai haƙuri kawai, amma ina bala'in son karatu, danaga babu damar yinshi sai na koma karatun hadda a wata ƙaramar isilamiyya da ke can gaba kaɗan daga layinmu, lokacin da naje makarantar ɗaliban shiririta kawai suke ba wani karatun kirki, ganin haka sai na kama kai na, na duƙufa na fara gyara nawa karatun, idan malami ya zo yai ƙari, kafin ya fita sai in tsaida shi in biya ma shi wanda ya ƙara sai ince ya sake ƙarani, nan da nan naiwa sauran fintinkau na wuce su, idan na koma gida ina aiki ina karatuna, nan da nan sai harda ta zauna min, lokacin da na shiga shekara sha kwai nai nasarar hardace izufi talatin cif, Mama ta so ta haɗa min walima sai Allah bai yarda ba, hakanan ta bani haƙuri muka ci gaba da gurgura rayuwarmu wacce take zuwa a hagunce.
Yanzu Abba tsakanina da shi sai zagi da munana kalamai, kaɗan zan kuskure ya dinga aibata ni gami da jifana da bala'u iri-iri, akwai wa ta rana bayan yayi baƙo daga Katsina ɗanɗan wa ta ƙanwar Lubabatu ne ya zo Legos neman kuɗi, sunanshi Hashim kuma matashi ne, tun da ya zo garin jinina da nashi ya haɗu, yana ririta ni sosai saboda yanda nike girmama shi, Yaya sama Yaya ƙasa, haka nike kiranshi sannan gaisuwar safe daban ta rana daban, idan nice zan zubo mashi abinci sai plat yai soro, sosai zuwanshi ke ɗebe min kewa, idan ya dawo aiki haka zai yo min tsarabar abin da yasan zai saka ni farin ciki, sannan dadaddare ya tasamu gaba ni da Mama yana bamu labarai, muyita dariya muna jin daɗi.
Ashe Umma nanan ƙule da mu, saboda Yaya Sumayya ta yi ma shi rashin kunya shi kuma bai da haƙuri, shine ya wawwanka mata mari, Umma ganin an mari ɗiyar so sai ta ji haushi ta ƙullace shi, shi kuma ganin yanda ta ke ɗaure mashi fuska ko gaisuwarshi dakyar yake amsawa sai ya kyaleta kawai ita da ƙurar da ta kwasota.
Muna zaune muna fira sai dariya nike, ina jefa tambaya a inda ban fahimta Yaya Hashim na bani amsa, kawai sai ga Abba ya hwaɗo mana hannunshi riƙe da belt, kaina ya nufo gadan-gadan yana huci kamar kumurcin maciji, sanin idan ya riƙe ni ba zatai min dakyau ba, sai na kwasa a guje nai waje ina ihu kaina ko ɗankwali babu, rufo man baya yai har wajen yashiga laftamin belt a ko ina na jikina, ni kima ban fasa gudu ina ihuba gami da neman ɗauki, wasu yarene suka tare ni matar ta ɓoye ni a bayanta mijin kuma ya tinkari Abba ya na mai faɗan bai kyauta ba, Abba da zuciya sai yahau zagin mutumin a hasale, nanfa dambe ya kaure a tsakaninsu, can zaka ga wannan jibgegen ƙato ya saɓi Abba sama ya tiƙa da ƙasa, ni da ke kuka sosai ganin yanda ake daga Abba sama ana maidowa ƙasa ban san sanda dariya ta kwacemin ba, dakyar aka samu aka raba su, shima dan akwai musulmai kima hausawa sosai a wajen da abin sai yafi haka, kuɗi matar mutumin ta bani wai inje a duba ni asibiti dan sosai Abba ya farfasa min jiki, ban ja danisa ba na amshi kuɗi bayan Yaya Hashim ya sungumi Abba zuwa gida, nima bin bayansu nai ina soshe-soshen azaba da raɗaɗi, dana shiga gida lokacin an shimfiɗar da Abba akan tabarma, har zan wuce ɗakin Mama sai jiyo mutyarshi nai yana faɗin.
"Karki kuskura ki shigarmin ɗaki, bankaɗaɗiya tsinanniyar yariya ƴar iska, Mubeena nayi danasanin saninki a rayuwata, ban haifi ɗiyar da zata gagareni ba dan haka ki tattara kayanki sahu a likafa kibar min gidana, na fidda ke daga cikin iyalaina me farar ƙafa kawai, tun ranar dana same ki nai bankwana da farin ciki, ga baƙin talauci daya dabaibaye ni tako ina, ni banga amfaninki ba dan haka maza ki kama hanyar Abuja ki nemi dangin Uwarki me zubin munafukai."