← Book details Zafin Wuta Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 13

Sashe 10

Zafin Wuta Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Uban wa ya aikeki shiga ɗakin Fauzan ɗin, ba jiya nace miki ki daina shiga kai tsaye ba, angaya maki yanzu kamar baya ne, bakiga ya samu lafiyaba, kuma da dukkan alamu so yake ya keɓe da matarshi, amma kunbi kun takura mashi, kin wani kwashi jiki kin raka Maimuna ɗakimshi, to uwar mi zata yo a ɗakin nashi bayan uwarta wacce tafi kowa isa da ita tayi ma ta katanga da shi."
Faɗin Hajjo ciki jin zafin abin da Sulaima ta yi, sai kuma ta juya ɓarinda Mommy ke zaune ta saka kan Moon a kan kafaɗarta tana rarrashinta.
"Fatima ya kamata kisan yanzu da baya akwai banbanci, dolene ki koyi kawarda kanki akan wasu lamurra, sannan kafin mudawo daga tafiya ki tabbatar da angyara ɗayan part ɗin, acan Fauzan zai koma shi da iyalinshi bayan mun dawo, ya isa hakanan yanzu lokacin da zaiyi rayuwar farin ciki shi da iyalinshi ne, baya ta wuce sai mu fuskanci gaba."
In banda gyaɗa kai babu abin da Mommy ke yi, ta mance yaushe rabon da Hajjo tayi mata magana a kausashe irin haka, yanzunma bawai faɗa take da hayaniya ba, anutsenta take illa ɗan kaurar harshe da tayi alamun ranta a ɓace yake.
"Sulaima daga yau kar in sake jin koda wasa kinkai Maimuna ɗakin Fauzan, kema na hana ki shiga hakanan kai tsaye sai kin nemi izini, ya kamata ku dinga aiki da ilimi."
Kasancewar kowa najin maganar Hajjo kuma babu mesan ganin ɓacin ranta sai Mommy da Sulaima suka shiga bata haƙuri, danda nan ta haƙura dama ita sam batada riƙo amma muddin aki ba daidai ba agabanta sai ta tanka, dalilin daya sake kusantata da Mommy bai wuce biyayya da sanin yakamatar da take dasuba, ga girmama mutane, saɓanin Hajiya Zulaihad wacce sam batada mutunci, sannan akwaita da baro zance babu tauna harshe, shiyasa sam basa shan inuwa ɗaya iya da Hajjo.

ABUJA
"Alhamdulillahi rabil'alamin, ikon Allah kenan, dan Allah kuce min ba mafarki bane, mijina ne nike gani a kusa da ni, Malam kana ganin abin da nike gani kuwa, kodai idona ne ke gani ba daidai ba." Tattausan murmushi haɗeda sanayun hawayene bayyane akan fuskar Hajiya Sadiya, haƙworanta goma sha reras a waje tsabar farin ciki, yau dai zata kira ranar da babbar ranar farin ciki, ko ranar da likita ya tabbatar mata da tana ɗauke da ciki batai irin wannan farin ciki, rungume Malam da ke sakar ma ta murmushi ta yi tare da faɗin.
"Nagode, nagode, nagode Malam ɗina, ban san da wane baki zan yi maka godiya ba, amma kasani cewa ina cikin mawuyacin farin ciki, da yardar Allah haɗi da jajircewarka mijina abin alfaharina ya dawo daidai." sai kuma ta sake shi ta nufi wajen Alhaji Umar shima tarungume shi ƙaƙam tana hawaye haɗi da sambatu.
Lallausan murmushi Alhaji Umar ya sakar ma ta bayan yayi nasarar cirota daga jikinshi, kallonta ya ke yana murmushi me taushi, cikin sanyi murya yace.
"Haba uwar biyu, wai dama haka kika tsufa ban saniba, kin kuwa ga yanda kika saka hijabin a karkace, ga hawaye harda majina, ina ganin dajine kikayi ko?." Yai maganar da sigar wasa, da sauri Sadiya ta sake shigewa jikinshi tare da goge fuskarta a jikinshi tana dariya, shima matseta yayi yana jin matsananciyar ƙauna gami da tausayinta na ratsa shi, bai san yanda akai ba sai ji yayi yanayin ya juye mashi, babu abin da yake buƙata sama da matarshi, cikin mantawa da inda suke ya shiga nunawa matarshi yanda yai kewarta, yayinda ta amshe shi hannu bibiyu itama tana gwada yanda tai kewarshi a aikace, tuni suka faɗa ɗuniyar ma'aurata, kasancewar lokacin asubahi ne da sauran iskar sanyi me saukar da shauƙi sai abin yai musu armashi sosai, dama Malam tunda yaga Sadiya ta rungume mijinta ya lalubi ƙofa yafice tare da kullesu yana jin kwanciyar hankali da farin ciki ganin murmushin Sadiya na ainahi ba irin wanda take yi me kama da yaƙen dole ba, cike da farin ciki ya koma ɗakinshi ya kwanta barcin kwana biyu dabai samun yin isashe.

Kusan sati biyu kenan Lawan na ganawa Fateema Abbas nau'o'in azaba, musamman data tubure akan ƙin ɗauko jariran Sadiya, duk ta rame ta bushe dama can bawani jiki ne da ita ba, sai kayan idanuwa waɗanda suka sake firfitowa waje, sam batada kwanciyar hankali, sosai take nadama akan biyewa son zuciya ta cutar da Sadiya, Sadiyar da take yiwa so irina ƴan uwantaka, sau goma tana ɗaukar mota ta nufi hanyar gidan, sai ta kusa ƙarasa sai ta tuna batada kwarin gwuiwar kallon Sadiya a cikin damuwa, haka zata juya ta koma gida tana rizgar kuka, shikuma Lawan ya ƙara ma ta da duka, dan dakyar ya samu yashawo kan su Muhammad Bello, shima dan sunsaka shi wani aiki na daban kuma yayi aikin da kyau.

Sosai ƴan uwa da abokan arziƙi suka dinga tururuwar zuwa duba Alhaji Umar tare da tayashi murnar samun lafiya, kusan kullum gidan acike yake da mutane, yauma Malam ya fita a mota zuwa cikin gari, kamar yanda ya saba cin karo da motar Fateema Abbas akullum idan zai fita ko idan ya dawo yauma haka ne, dai de yau yayi nasarar ganin fuskarta, saboda ta buɗe glass ɗin ta ziro da fuskarta tana wankewa, kallo ɗaya yai mata yaji tsigar jikinshi ta tashi, nan take ya hango kamarta da iyayensu, sannan dogon hancinta sak irinza babansu Alhaji Abbas, bawa driver umarnim tdayawa yayi, ya dinga kallonta harta juya motar tai kwana ta koma gida, sosai yake mamakin abin da ke kawota layin gidan kuma bata taɓa shiga ba, barin komi yai a ranshi ya umarci driver daya ƙarasa.
A ranar da suka je yiwa Alhaji Umar da iyalanshi cuku-cuku na barin ƙasar baki ɗaya, dan cewa yai zai je hutu a shahararun ƙasashe kamar guda biyar shi da matarshi da ƴaƴanshi, kuma Malam ya walilta akan shirin tafiyar tasu, yau dai Malam a ƙafa ya tako zuwa farkon layin tsararriyar unguwar tasu, bai yi minyuna uku kwararaba sai ga motar Fateema Abbas, tana yin parking ya nufi wajen kamar zai wuce, yana isa wajen murfin ya wani fizgeshi da ƙarfin tsiya, dayake a buɗe yake bata saka lock ba sai ko ya buɗe Malam bai yi wata-wata ba yabi umarnin zuciyarshi kawai ya janyo Fateema Abbas wacce tsoro da tashin hankali ya gama tsureta, babu abin da take sai zazzare idanuwa, ɗaure fuska Malam yayi ba tare daya damuba kai tsaye ya shige da ita bayan ya gwada id card da lasisin zamanshi a unguwar, bai daina janta ba sai da ya isa main parlour da babu kowa face ma'auratan da ke cikin farin ciki sannan ya watsar da ita ta durƙushe a gaban Sadiya tana sakin zazzafan kuka.
"Kunga wannan matar kusan kullum sai naganta a layinan, nasha tambayar police masu gadi a mabanbantan gidajen layinan akan ko sunsanta, sai suce ih abaya tana yawan zuwa layin kuma nan gidan take zuwa, shine yau na shigo da ita." Sadiya bata gama jin abin da yake faɗa ba ta sauko daga kan sofa ta rungume Fateema Abbas tana jin kewarta na ratsa jini da ɓargon jikinta, sai kawai suka hau yin kuka atare, sai de ita Sadiya na farin cikin ganin Fateemar ne a daidai lokacin da take nemanta dan ta tayata farin ciki, sun jima sunayi babu me rarrashin wani, kafin daga bisani Sadiya ta ɗago da fuskarta wace ai jage-jage da ruwan hawaye sannan ga murmushi du alokaci ɗaya, cikin muryar kuka tace.
"I miss u Fateemana, kinzo a daidai lokacinda nike buƙatar ganinki, nagoda da wannan Fateema, ina cikin matsanancin farin ciki ƙawata, zo muje ciki muyi magana kar waɗanan mutanen su suka mana ido."
Wani busashen murmushi Fateema Abbas ta saki tare gyaɗawa Sadiya kai ta tashi gwuiwoyi a sage suka shige ciki.....✍️

LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.

9136291920
MARYAM UMAR
OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA

BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘

WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK FOUR 4
CHAPTE 47
Chapter 10 · 0% Book details