← Book details Zafin Wuta Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 13

Sashe 6

Zafin Wuta Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

بسم الله الرحمن الرحيم.
Ina shirin tashi sai gashi ya shigo, a mamakina maimakon ya hauni da faɗa kamar yanda ya saba, sai yahau washe min baki yana fara'a gami da cewa in zauna manah, sakato na yi ina kallon Abba, zan rantse rabonda yayimin dariya tun ina ƴar shekaru bakwai, idan dai naga dariyarsa to shi da Umma ko su Yaya Sumayya ne.
"Yau kuma fira kuke taɓawa ke da ƴar ta ki." Abba ya faɗa yana jefawa Mama murmushin yaudara, bata tankashi ba sai kallona da take yanda na saki baki.
"Nifa alkairi tafe da ni, ba komi bane face samu ƙaruwar siriki da mukai, ƴarki ta yi goshi abokina Alhaji me dala ne yazo min da kanshi akan yana son Mubeena, banyi wani jinkiri ba na amince mashi, zuwa gobe zai fara zuwa fira, kinga shikenan tun da karatu bai samu ba sai kije can kiyi bautar aure, bari kiji ba ƙaramin alkairi za ki samu ba da auren Alhaji me dala, nan da wani ɗan lokaci rayuwarki zata canza, muna za ki canza mana tamu rayuwar, saboda me dala be iya so ba, gashi dai mugun marowaci amma kuma akwai kyauta ga wanda yake so."
Haɗa haruffan da Abba ke magana na fara yi dan su fassara min maganganun da yake yi, na fahimta amma ban gane wa yake nufi da auren ba, kallon Mama na yi ina tunanin ko ita Abba ke nufi da tai auren, sai kuma na tuna ai ita ɗin matarshi ce taya zatayi wani auren bayan bai sake ta ba, tsulum na tsoma baki jikina na karkarwa nace.
"Wai Abba Mama ce zatai wani auren ko kuwa, ni ban gane abin da kake nufi ba."
"Wace Mamar kike nufi, badai matata Halima ba ko? dan uwarki a ina kika taɓa jin anyi aure akan aure, ke Mubara nike nufi ba wata ba, kece zan yiwa aure da aboki kuma aminina, zai zo gobe sai ku sasanta kanku."

"A'uzubillahi Abba ni fa kace, a'a sai dai ko Yaya Sumayya ita ce keda samari harma take fita taɗi amma ni bazanyi aure ba har sai na gano inda Mama da danginta suke a can Abujar kayiwa Yaya Sumayya kawai ni bana so."
Zafafan maruka waɗanda suka gigita ni sauke min yakuma hauni da sababi akan ban isa ba aure kamar nayi shi na gama ne.
Daga wannan ranar rayuwa tai min tsanani, banda sukuni ko kaɗan, ko shago naje yanzu babu wannan walwalar a fuskata, har hutu Madom ta bani ganin yanda nike ciki damuwa, danasan yanda hutun da ta bani zai zame min wa ta damuwar da bazan yarda in tafi ba, dan kuwa yanzu Abba ko nan da can baya fita, kullum cikin maimaita min yake akan dole sai na auri Me dala idan ba haka ba zai sallame ni inbarmashi gida, Mama dai dakanta sai da ta shiga cikin maganar ta rarrasheni akan in amince, amma na kafe akan bazan auri abokin Abbana ba, ni auren ma gaba ɗaya bazanyi yanzu ba sai na gano dangin mahaifiyata, har dai Umma da ba ƙaunata take ba akwar ranar da ta kwaceni daga hannun Abba da ya bini yana jinga, cemin ta yi.
"Wai ke wace iriyar jakar yarinya ce, ki amince da auren mana tun da ya kafe akai, kin fi son yai ta jibgarki kamar yasamu jaka, ba gara kiyi auren ba ki tafi can ki huta muma mu rage mugun iri."
"Wallahi banzan auri abokin Abbana ba, ke zai hana ki bashi Yaya Sumayya ko yaya habiba tun da suɗin sun girme ni." na bata amsa idona a soye babu alamar kuka, aifa sai tahau tsinemin tana zagina akan ɗiyarta ba zata auri abokin Abbaba, nima na sake kafewa akan bazan auri me dala ba.
Nau'o'i iri daban-daban na azaba Abba ke gana min, duka zagi kyara gami da hantara amma duk basu sa na saduda na karɓi zaɓinshi ba, ana cikin haka ne Yaya Hashim ya zo gida, nan yaga abin da ke faruwa da ni, idan Abba zai dake ni shike riƙe ni ta yanda bazan iya guduwa ba, idan aka gama dukana kuma ya ɗaura min ruwan zafin inyi wanka sannan ya bani maganin ciwo jiki gami da yimin nasiha akan bin iyaye, jin shi kawai nike ban taɓa ɗaukar shawararshi ba, dan nayi rantsu na ƙara akan bazan auri me dala ba, Yaya Hashim ya nema min ayyuka da yawa amma ko ɗaya babu wanda Abba ya yarda inyi, hakanan naci gaba da karɓar uguba a wajenshi, shi kuma Me dala bai janye ƙudirinshi a kaina ba dan har zuwa yake fira wajena, firar da babu abin da ke cikinta sai baƙaƙen maganganu da alwuran bala'u da nike yi mashi akan muddin ya aureni to yayi sallama da farin ciki, sosai ya tsorata da kalamaina amma kuma ban janye daga neman aurena ba, sai de yace ba za'ayi auren ba har sai na amince dakaina dan yana tsoron auren dole kar inje in kashe shi a banza.
Ana haka na cike shekaru ashirin har da ɗoriyar biyu, amma babu abin da ya sauya daga hawalar da nike sha, sai ma abin da yai gaba, ga duka, zagi, tsinuwa gami da takura daga wajen Abba, ga tulin ayukan gida wanda ko ina halin ciwo ne sai nayi, sannan ga zuwa shago wanda shima ban daina ba, ga kuma karatun isilamiya wanda yanzu ba koda yaushe nike zuwa saboda rashin lokacin, a gefe ɗaya ga daɗaɗɗen burina na zuwa Abuja dan in nemi mahaifiyata ko danginta, ina da tarin tambayoyi da nike so inyi mata, zan fara da yi ma ta ƙorafi akan yarda ni tun ina tsuman jarintaka sannan in ɗaura da tambayarta dalilin dayasa ta zaɓi barina a wajen Abba alhalin tasan bashi da zuciya me kyau, daganan zan rungumeta inji ɗumin jikinta in kwanta akan ƙafafuwanta inyi barci, akwai wa ta sarƙa wacce Abba ya bawa Mama tun lokacin aurensu yace ma ta mahaifiyata ce ta bashi akan ya bani idan na girma, indai na rayu itama ta yi tsawon rai ban yarda sarƙar ba to tabbas zamu haɗu wa ta rana kuma ba zata kasa gane ni ba.

Lokacin da wahalhalu sukai min yawa ne Yaya Hashim ya zo da maganar sama min aikin jinya, da farko Abba bai amshi zancen ba, amma daga baya bayan sun keɓe sai ya amshi batun da hannu bibiyu, da rawar baki ya sanar manah, yayinda Mama tai bore akan lamarin ƙiri-ƙiri ta ƙi nuna goyon baya, Abba kuma ya kafe akan hakan, a ranar da za'a kawo ni nan gidan na haɗu da cutar makanta, kuma a lokacin ne na tabbatar da lallai Abba baya sona, duda bana gani hakan bai hana shi tahowa da ni ba, ni kuma na zaɓi zuwa aikatau ne dan inyi nisa da rayuwar gidanmu, na zaɓi inyi jinyar mara lafiya duda ban san ya ciwon na shi yake ba dan in nisanta kunnuwa sa jin zafaffan munanan maganganun Abbana masu kama da ZAFIN WUTA a zuciyata, kuma Alhamdulillah buƙata ta tabiya, kuna na samu tarba me kyau yanzu hankali a kwance yake, ina jina sakayau banda wa ta damuwa illa sanin inda mahaifiyata ta ke, na amince da auren da aka ɗaura min ne saboda banda yanda zanyi, kuma dole na yarda tunda Abbana ya riga da ya karɓi kuɗinku, sannan na ƙarfafa kaina ne akan gara in zauna inyi jinyar da igiyoyin aure a kaina, tunda marar lafiya baligi ne wanda ba muharramina ba, anan na jinjinawa karama da hangen nesa irinna Papah, wanda bai kasance meson kanshi ba, duda a matse yake akan neman lafiyar ɗanshi, hakan bai saka yayi aikin irinna jahilai ba, ina matuƙar girmama karamcin da Papah ya nuna min."
LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.

9136291920
MARYAM UMAR
OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA

BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘

WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK FOUR 4
CHAPTE 43

بسم الله الرحمن الرحيم.
Ina dasa aya na ja numfashi me ɗumi gami da fesarwa, sannan na ɗaga kaina ina kallon yanayin kowa, da Sulaima na haɗa ido sai nai tozali da fuskarta face-face da ruwan hawaye idanuwanta sun kaɗa sunyi jazur, sai ta soma girgiza min kai, kamin tai nasarar fizgo magana da kyar daga ɗan mitsilin bakinta.
"Haƙiƙa tun da Mommy da Papah suka haife ni, ban taɓa cin karo koda a cikin labarin film ko novel uba me irin halin Abbanki ba, haƙiƙa ya cutar da ke cutarwa me tsanani, ya mance da faɗar manzon Allah s,a,w da yake cewa.
"Mutum me kiwo ne a cikin ahalinsa, kuma abin tambaya ne akan kiwon da aka bashi.", sai bai duba raunaninki kasancewarki mace, ya cutar da ke ta hanyar hana ki abin da kike so, sannan ya tirsasaki akan abin da sam bai dace da ke ba, idan abu ya shafe ki za'a samu ya tsaurara sosai, shi bai raga maki ba bare matarshi bare kuma yayunki waɗanda ke ware ki daga cikinsu, gaskiya kina da haƙuri da juriya na sara maki da irin ƙoƙarin da kikai, insha Allah sai ke da iyayenki kunyi alfahari da kasancewarki a cikinmu kuma mata ga yayana abin son kowa a cikin ahalinmu, nasan wanene mahaifinmu, muddin yaji cikakken labarinki zai taimaka sosai wajen inganta rayuwarki, sannan nasan wacece Mommynah itama zata taimaka sosai wajen ganin ta bada tata gudumawar, kakata kuma Hajjo tuni take baki tata gudummawar ta hanya saka soyayyarki me tsanani a ranta, ta na matuƙar ƙaunarki sosai."
Kamar ƙadangaru haka suka shiga gyaɗa kai likacin da Sulaima ke magana.
Ganin lokacin sallah yayi yasaka kowa ya tashi jiki ba kwari dan gudanar da sallar magrib.
Chapter 6 · 0% Book details