Sashe 13
Zafin Wuta Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
بسم الله الرحمن الرحيم.
Bayan rabon gado Ahmad ya sake faɗaɗa kasuwancinshi, inda ya sake gina tamfatsa-tamfatsan gidaje a garin Legos da Abuja, yayinda ya zauna da Hajjo a ƙeraran ɗaya daga cikin gidajenshi na Abuja har zuwa lokacinda girma ya cimmusu, lokacinne kuma Abdallah ya ƙulla soyayya da ƴar wajen Zainaba cousin sister ɗin Hajjo wacce suke aminai na ƙut da ƙut, babu ɓata lokaci aka sha hidimar biki dan anjima ba'ayi taron hidima a gidanba, bayan auren Abdalla da matarshi Fatima Ahmad ya bashi kyautar babban companynshi da ke sauɗia a matsayin gudumuwar ƙoƙari da ƙwazon da yake yi a wajen aiki ba kamar Muhammad ba wanda bai da aiki sai shirirta da yawace-yawace, ko kuma bin Abdallah a baya duk inda yasaka ƙafa, kuma yana gani yana aiki amma bazai tayashi ba sai dai surutu da labarai da yake zaman bawa Abdallan.
Sosai Muhammad ya nuna jin daɗi gami da taya ɗan uwanshi murnan wannan gagarumar kyauta, bai ji hassada ko ɗaya ba sai ma nunawa da yake yafi Abdallah jin daɗin hakan.
Fatima kuwa itace ta zama uwar ɗaki ga Muhammad, komi ya samo sai ya nufeta, kuma baida me bashi shawara sai ita, shakuwa da fahimtar juna sosai ta shiga tsakaninsu, inda Abdallah yaji daɗin hakan sosai dan shawarwari masu kyau Fatima ke bawa Muhammad, kuma yana kwatanta yin amfani da shawarar tatah sosai.
Bayan shekaru biyu zuwa uku da auren Fatima da Abdallah Allah ya azirtasu da haihuwar tauraro me tsananin haske da walwali, suka haifi kyakkyawan bature kuma balaraben ɗansu wanda yaci suna Muhammad ake kiranshi da Fauzan, tun da fatima ta samu ciki shine ya fara ankara, kuma kullum ciki yo siye-siye yake ya kawo yace na Babyn da zata haifa masu ne, hatta Abdallah sai de ya kawo ido ya zuba musu, dan shaƙuwar da ke tsakanin Muhammad da Fatima wani al'amari ne na Ubangiji, kasancewar Muhammad miskili musamman idan yaga baƙuwar fuska, amma farat ɗaya ya sake da Fatimar tun ta na amarya.
Anyi bikin suna na garari, dan sosai iyayen yaro da kakaninshi hanshaƙan masu ɗumbin dukiya suka zazzafe aljihunansu wajen yima me jego da jinjiri kyauta ta ban mamaki.
Tun ranar da aka haifi Fauzan tauraronshi ya sake haskaka ahalinsa, musamman ta fanni kasuwancinsu, gashi yaro me farin jinin mutane, ko baka ƙaunar Allah idan kaga Fauzan sai ka tsaya ka ɗaukeshi kodan kyanshi me jan hankali.
Yana girma kyawunshi na daɗuwa, yayinda ya tashi tsumu-tsumu cikin soyayyar ƴan uwa da abokan arziki, duda irin ƙaunar da ake nuna mashi iyayenshi basu bari ya sangarce ba, sosai Fatima ta tsaya akan tarbiyarsa.
Sai da Fauzan yakai shekaru goma cif, sannan Allah ya nufa Muhammad ya samu damar ɗaya daga cikin masoyansa masu nace masa, Zulaihad matashiyar yarinyace ƴar ƙarya dason abin duniya, tun ranar da tafara sanin irin ɗumbin arziƙi da dukiyar da familyn Shuraim suka tara, ta fara farautar hanyar da zata shiga cikinsu a dama da ita, tun daga ranar data mallaki number yawar Muhammad Ahmad Shuraim, bata raga mashi ba wajen kira da turo saƙonni, kota ina ya waiga sai yaci karo da saƙoninta dan sosai ta dage akan ta mallakeshi duda dafarko bashi tayi hari ba, ganin bata samu abinda take so ba shine tadawo wajenshi, sai kuma tayi sa'a ya zaɓeta daga cikin tarin masoyanda ke kawo mashi hari, itama ya zameta ne saboda shawarar da Fatima ta bashi, bai saba musu ko jayayya da shawararta ba, shiyasa kai tsaye ya amincewa Zulaihad amma baiyi ƙasa agwuiwa ba wajen faɗa ma ta wacce tabashi shawarar zaɓenta, ya kuma ɗora ma ta da buƙatar son ta ɗauki Fatimar a matsayin yaya ko uwar ɗaki sannan ta girmamata kamar yanda yake yi, bata musa mashi ba da farko dan kwantar da kai tai ta dinga zuba ladabi da biyayya kafin tashiga daga ciki, dan tayiwa kanta alƙawarin zama hamshaƙiya wacce har ƴan cikin familyn Shuraim zasu dinga taƙama da yin misali da ita, Zulaihad ba daga baya ba wajen kyawun fuska, sai de suririyace sosai, danma tan saka ciko shike taimakawa taɗanyi fasali amma doguwace samɓal ba gaba ba baya, da yake Muhammad bata ita yake ba kawai de zaiyi aurene dan toshe bakin manyan Family da suka sakashi gaba.
Ba'a ɗauki lokaci me tsayiba aka sha biki na garari, wanda shidai ango babu wani ɗoki ko murna, kaf tsare-tsaren komi Fatima wacce tazama hamshaƙiyar Hajiya ce ta shirya, yayinda Hajjo ta koma gefe cike da jin daɗin yanda Hajiya Fatima ke tafiyar da komi cikin tsari da burgewa, sannan ta kasa ta tsare wajen tarbar baƙin d ke zuwa daga ƙasashe mabanbanta musamman dangin Shuraim, waɗanda rabonsu da Nigeria tun lokacin haihuwar Fauzan, gashi yanzu ya girma sosai dan ya shiga cikin shekara ta shidda, sai de ba'a nan gida Nigeria yake karatu ba, Saudiyya Alhaji Abdallah yakaishi acan yake karatunshi.
Bayan ansha bidiri da shagulgula aka kawo amarya a katafaren gidanda Ahmad Shuraim ya tamfatsa don tara iyalanshi waje ɗaya, sosai aka ƙawata ɓangaren na amarya komi sai sheƙi da walwali yake na sabunta, yanda Hajiya fatima ta marabanci amarya da ƴan uwanta ya saka dangin amarya bawa Hajiya Fatima amanarta, dan yanda sukaga larabawa da turawa na ta karakaina a wajen sai jikinsu yai sanyi, amma ganin babu wulaƙanci ko nuna launin fata sai suka saki jikunansu, to kuma sai alkairin da Hajiya Fatima ta nuna musu yasanyasu yaba hallayarta suka kuma kwantar da hankalinsu da cewa ƴar uwarsu ta samu dangin miji na gari, kuma masu kirki, bayan ƴan kai amarya sun watse aka bar amarya ita kaɗai sai kwalla idanu take, yayinda kafatanin tururuwar dangin ango suka cike shashen suna gabatar ma ta da kansu ɗaya bayan ɗaya, taji daɗin yanda suka nuna mata kulawa, amma babban abin da ya ɗaure ma ta kai kuma wanda bata ganeba shine, wai wacece wannan Fatimar wacce kaf dangi dashi kanshin Muhammad ɗin ke yabawa da hallayarta, kusan kowa sai yayi ma ta fatan zama kamar Fatima, harma suke nuna mata yanda sukejin daɗin alaƙa da ita, bata nuna komi ba afuska haka taci gaba da amsar gaisuwa gamida kyaututtukan da suka dinga bata, kunsan bature dason bada gift, sosai taji daɗin kyaututtukan, sai de basu shafe ma ta tunanin inda Muhammad ya tsaya har zugar danginsa suka fice baizo ba.
Yayinda dangi ke gabatar da kansu a wajen Zulaihad, Hajiya Fatima nacan na fama da ango Muhammd daya je sashenta ya danƙare yana kwasar daddaɗan girkinda ta haɗawa Oga, bayan ya gama ne ta tasa ƙeyarshi har toilet ɗin ɗakin da yake sauka ta ajiye mashi kayan da zai saka d sukkan abubuwan da zai buƙata sannan ta koma up wajen me gidanta da yawani narke ma ta wai shi ya gaji, Abdallah kamulallen mutum ne me dattako da sanin yakamata, idan kanason ganin taɓara da shagwaɓarshi to aje wajenshi lokacin da ya keɓe da Fatima, koma m ta yake kamar Habibynta Fauzan wanda bai yadda ya rabu da ita muddin yazo hutu gida, bata gazawa wajen kulawa mijinta, yana samun dukanin kulawa da soyayyar da yake buƙata, shiyasa ya bata babban matsayi zuciyarshi, kuma bai mata shamaki da dukkan abind yake nashi me ba, harma wanda ba nashi ba, kaban ta gama ciyar da shi sunyi shirin barci sai ta saka hijabi shima ta bashi jallabiya ya saka suka fice dubo su Hajjo ko zata buƙaci wanin abun idan batai barci ba, amma mi, su na sauka down suka iske Muhammad kwance abinshi yayi ɗaiɗai yana kallo, da wani irin sauri ta ƙarasa wajenshi tare da doka mashi pillown kujera, a maimakon ya tashi ya fice sai ya shagwaɓe murya yace.
"Haba my lovely Auntie mi nayi miki zaki dakeni a tshohon darenan."
"My ƙane ka fita idona in kulle, miye haka zaka wani zo ka zauna anan ga yarinyar mutane can kabarta ita kaɗai." ta faɗi tana bashi umurnin tashi ya fice da hannu.
'Tab aiko babu inda zanje kin manta ita tace zata aureni a haka, nifa ba wani sonta nikeyi ba kawaide dan in toshe bakunanku da kullum ke ƙara tsini wajen mitar na girma na ƙi aure, shiyasa na aureta amma ni ai ban isa aure ba har yanzu."
Yai maganar yana zagayawa inda Abdallah ke tsaye yana dariyar dramar su da bata ƙarewa.
"My ƙane ka fita idona wallahi, maza ka wuce ka tafi kafin ranka ya ɓaci yanzunan."
"Haba my lovely taya zakiyi min haka, nidai idan baki daina yimin ihuba bazan tafi ba anan zan kwana tare da Big brother ko Abdallahn Hajjo." Ya faɗi da sigar tsokana, murmushi kawai Abdallah yayi dan miskiline na ƙarshe, a wajen Hajjo, Fatima da Muhammad kaɗai yake sakewa yayi surutu, shima bakoda yausheba sai sa'i sa'i.
"Sweet heart ka kyaleni da wannan ƙanin nawa, karm ka shiga tsakani dan babu abin da zai hana inyi ma shi duka muddin bai fice ya tafi wajen yarinyar mutane ba."
"To na ji zan tafi amma muyi abu ɗaya, ku kama hannuna ke da Big bro ku kai mata amanata, idan kuma ba hak ba babu inda zanje."
Har zata yi magana sai kuma tayi shiru ganin ogannata yayi amman da zancen babu yanda ta iya haka Abdallah ya kama hannunshi ita kuma ta kama na Abdallan suka jera gwanin sha'awa, har bed room ɗin suka shigar da shi inda Zulaihad ke kamule akan gado ta maida mayafinta ya lulluɓe fuskarta gaba ɗaya.
Ta daɗe tan jin yanda Muhammad ke ƙoda Hajiya Fatima, sai de ganin da tai ma ta ya doke labarin haɗuwa da tsarinta da Muhammad ke bata, cikin bugawar zuciya da wani kakkauran yawu daya jima da daskarewa a maƙogaronta ta kalli Fatima da hannunta ke sarƙe cikina Abdallah, mutumin da tai hari da farko bata samu ba shine ta koma ga ɗan uwansa,cikin rarrabewar harshe ta gaisar dasu a jimlace dan jikinta karkarwa ya soma yi...✍️
LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.
9136291920
MARYAM UMAR
OPAY
TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.