← Book details Zafin Wuta Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 13

Sashe 2

Zafin Wuta Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana gama faɗin hakan ya ja hannun Sumayya da Habiba waɗanda suke kaca-kaca babu wanka, kai ko ɗankwali babu yai hanyar ɗakin Umma alhalin ɗakin Mama ya ke a ranar....✍️

LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.

9136291920
MARYAM UMAR
OPAY

TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA

BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘

WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK FOUR 4
CHAPTE 39

بسم الله الرحمن الرحيم.

Umma ce ta bi bayan Abba da ledojin da ya yasar lokacin da ya kifamin mari, tana tafiya tana juyawa Mama ɗuwawuka, har suka shige ciki.

"Mamanah, na yiwa Abbana laifi ko?."
Na katsewa Mama suman wucin gadin da tai, kallona ta yi hawaye na taruwa a idonta tana kallon yanda farar fuskata tai jawur, babu ƙarya na maru a wajen Abba, jan hannuna tai zuwa ɗaki tana ture dukan damuwarta akan abin da Abban yai gefe ta dawo da hankalinta kacokam a kaina ta na faɗin.
"Ai Mubeenar Abbanta yarinyar kirkice, sam bata laifi a wajen Abbanta, ba ke yazo duka ba hannunshi ne ya goce ya sameki, kiyi haƙuri kin ji ƴata."

"To amma ai naga yana yi maki tsawa da faɗa, kamar yanda yakeyiwa Umma idan ta dake ni ko ta saka Yaya Sumayya tai maki rashin kunya." na faɗi ina kallon yanda Mamar ke kokowa da hawayen da keson zubo ma ta, batace komi ba ta rungume ni tsam cike da tausayi da soyayya, sai nima na lafe a jikinta ina jin zafi da raɗaɗin marin na zagaye kewayen kaina tare da safkarmin da ciwon kai nan take, indai taurin zuciya ne da anzo wajena to anrufe ƙofa, abin da zai sa ni kuka ba ƙarami ba ne, koda kuwa bani da lafiya bana kuka, sai de in shige jikin Abba ko Mama in lafe inyi shiru.
Ranar da zazaɓi na kwana, dana juya sai ince wa Mama.
"Wai haryanzu Abbana na ɗakin Umma, to yaushe zai fito yazo mu kwanta?."
Sai Mama ta shafi kaina tace. "Yarinyar Abbanta yanzu zai shigo, yana aiki ne a can shiyasa."
Sai inyi shiru kawai, amma da an ƙara jimawa sai na sake tambayarta, amsar dai ɗayace ta ke bani, ba wani abu ya saka nike ƙulafucin zuwanshi ba, face bani sweet ɗin da tun ina ƴar shekara biyu ya saba bani ita, daya shigo gida zan tafi wajenshi ina murna, haka zai ɗaga ni yai juyi da ni a sama sannan ya dire ni tare da bani ledar sweet ɗin wacce na daɗe da hardace kalarta, ko fita akayi da ni naganta a waje wani ya sha ya yar sai na nuna ina kuka ina kiran.
"Sweet Affana." haka za'aje shago mafi kusa a sayomin dan samun zaman lafiya.

Ranar barci rabi da rabi na yi, ita ko Mama ban tunanin ta samu rintsawa, musamman yanda muryar Umma ke tashi daga ɗakinta ta na dariya ko faɗar wasu maganganu waɗanda sukai nauyi da yawa.

A ɗaki ta ƙule ita da Abba wanda yake ganin Ummar kamar ita ce sarauniya mata a duniyarsa, wani haske gami da walwali na musamman yake gani tattare da ita, yayin da haske ya disashen kyawu da tsarin mu ni da Mama wanda yake gani ya ji wanh sanyi na ratsashi, hakanan yake jin wata iriyar soyayyar Umma na fizgar shi, ji yake idan bai yi ma ta abin da take so ba zai iya rasa ranshi gaba ɗaya, umarninta kawai yake jira shi kuma ya zartar ba tare da jinkirtawa ba.
Wani irin farin ciki ne baibaye da Umma ganin yanda maganin da ƙawarta ta amso ma ta a wajen wani wanda ke fakewa da sunan malunta yana dulmiyar da mata masu son zuciya gami da haramtawa mazajensu abin da Allah ya halasta musu, ganin yanda Abban ya wani susuce ya saka kanta ya fasu, nan tai ta fi'ili kala-kala, yayinda ta ƙuduri niyyar sai da gasa mana ɗanyat gyaɗa a hannu ni da Mama, musamman ni da Abba ya ware daban yana nuna min soyayya, tattali gami da kulawa, babban abin da ya sake kafa tsana ta a zuciyar Umma bai wuce yanda kullum asirtacen kyawuna ke ƙara bayyana ba, ga farin jini, kowa ya zo gidan zai kula ni, hakan ba ƙaramin dasa ma ta tsana ta yai ba, ga uwa uba yanda sam Abba baya gajiyawa wajen hidimta min.
Ranar kwanan farin ciki Umma tayi, hankalinta kwance gata ga mijinta kusa da ita.
Yayin da ni da Mama mukai kwanan ƙunci, dan Mama sam bata runtsa ba, saboda tsananin mamakin yanda Abba ya share bai ko leƙo mu ba, abin da yasa ta kasa barci bai wuce son ganin lokacin daya shigo ɗakin ba, bata so yace ma ta ya shigo ya iske ta na barci, gefe ɗaya kuma ga damuwar zazzafan zazzaɓin daya rufar min, gashi da na ɗan yi barci na farka saina tambayi Abba yazo, tun tana amsa ni da zaizo har ta gaji ta ce da ni.
"Zai zo amma ba yanzu ba sai gobe da safe, idan kina so ya zo to kiyi barci da safe dakin tashi za ki ganshi."
Da haka ta samu nai barci sosai.

Tun da Mama ta tashi sallar asubahi barci ke fizgarta amma ta tsaya jirar shigowar Abba, shiru bai ko leƙo ƙofar ɗaki ba, bata jin yau ya tashi yai sallah, dan haryanzu ɗakin Umma a rufe yake, kasancewar kyauren ɗakinta ƙara gareshi, idan an buɗe ko yaya ne zata ji ai.

Sai da gari ya waye tar sannan su Abba suka tashi, cike da kunya ya shige bayi yai alwala sannan yai wuf ya gudu ɗaki ya gabatar da Sallah, zai rantse tunda Mama ta shiga rayuwarshi ya mance yaushe ne ya makara a sallah, tun tana tada shi har ya koma shike riganta tashi saboda abin yabi jikinshi, amma sai gashi ranar yayi sallar safe.
Fakon idon Umma yai da tana salla ya sulale ya shiga ɗakin mama, lokacin harta haye gadonta zata kwanta taganshi ya shigo yana sanɗa, a hankali ya ƙaraso gabanta yana faɗin.
"Halimatu dan Allah kiyi haƙuri, wallahi da ke na kwana a raina, ni kaina ban san miyasa na kasa zuwa duba ki ba."
Wasu raunananun hawayene suka zubo a idon Mama kafin ta ce komi sai suka ji disashiyar muryata na faɗin.
"Abbana ashe ka zo ban tashi ba."
Wajena ya ƙarasa tare da zura hannunshi a aljihu ya duntso sweet ɗina ya bani, tare da shafa kaina kwalla na taruwa a idonshi, kafin yace wani abu sai jin sautin Umma mukai ta na faɗin.
"Irorona, wai ina ka shige ne."
Zaram ya miƙe ya fice jiki na rawa yana faɗin.
"Ganinan Umma na je wajen Halima ne induba ko sun tashi sallah tun da yau gidan makara mukai."
Saurin janye shi tai suka koma ɗaki ta kulle.
Ahaka muka jera kwanaki bama samun kulawa daga Abba sai de a ɓoye, kullum kusancinmu da shi na sake nisa, muna ji muna gani idan ya shigo Umma za ta tare shi tana rangwaɗa da karairaya ta zanje shi su shige ɗaki, bamu zamu sake ganin shi ba sai lokacin cin abinci idan mun haɗu, shima sam bata bari fira ta haɗamu da shi, daga ta ɗauko labarin wannan sai ta ɗauko firar wancan, haka za ta kanainayeshi su manta da mu a wajen suyita firar, tun ina yiwa Mama ƙorafin yanzu Abbana baya so na su Sumayya ya ke so, har nagaji dan kaina na daina ganin irin yanda ta ke shiga damuwa.
Ahankali Umma ta mallake gida, sai abin da tace, Abba kuma baya saɓa umarninta, idan ta ce ayi, kai tsaye yake yi, haka zalika idan tace abari kai tsaye ake bari, sai da ta tatse sauran kuɗaɗen Abba tas ta na turawa ƙawarta ta na zuwa wajen bokanta yana sake sabunta ma ta aiki.

Wata rana muka wayi gari da masifar Umma tun da sanyin safiya, ita da Abba ne akan ta ce yau shayi take so a sha kuma babu kayan shayin, shine yace da ita bai da kuɗi naira dubu ɗaya jal ta rage ma shi, nan tashiga masifa akan koma ina ne zai je ya samo sai ya nemo su, dan bataga abin da ya isa ya hana ta shan shayin a ranar ba, bawan Allah haka ya fita yaita garagambar aikin ƙarfi, bai dawo ba sai kusan ƙarfe ɗaya saura, lokacin ni da Mama har mun dama kunu mun sha ganin shiru ba'a aiko manada kayan kari ba, ni kuma banda jumurin yunwa ko kaɗan, ba wani cin kirki nike yi ba amma ban jure zarce lokacin cin abincina.
Amaimako Umma ta amsa ta yi godiya sai tahaushi da sababi akan daɗewar da yai, memakon yaji haushi sai bata haƙuri kawai yai ya zauna jiran ta haɗa ta kawo mashi, ganin shirun bata kawo ba ya saka ya bita ɗaki yana tambayarta, sai tace ai ta ga Mama ta dama kunu ɗazu shiyasa tabari sai kuma gobe tunda yanzu lokacin abincin rana ya ƙarato.
"A,a Umma ki haɗa shayinan kawai kowa yasha yanzu, dan wallahi babu kuɗin da zasu isa ayi hidimar yin girki yanzu, idan na sake fita na yawato zuwa dare sai a ɗaura girki." Abba ya faɗa muryarshi da alamun gajiya.
Chapter 2 · 0% Book details