Sashe 4
Zafin Wuta Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Innalillahi! Abba ni!! ni Abbanah, tsinemin fa kake, wayyo Allah na shiga uku na lalace, dan girman Allah Abba kayafemin na tuba bazan ƙara ba, wallahi nayi nadama, daga yau bazan sake yi maka laifi ba."
Haka na durƙushe a wajen in magiya gami da roƙo, amma Abba fir ya kafe akan saina bar mashi gida, ni kuma sai kuka nike jin yanda yake tsitsinemin yana zagina gami da aibata ni, Umma ce ta fito ta dinga zuga shi ranta fes, dama ita ce ta haɗa min ƙulalliya har ya zo ya dake ni.
Sai da Yaya Hashim ya saka baki sannan Abba ya kyale ni, amma tsinuwa babu kalar da baiyi min ba, ni kuma sai kuka nike hankalina a tashe, Mama ma kukan take tayani dan abin da Abban yayi ya mugun bata mamaki, duk da ita kaɗai tasan bashine ya haifeni ba, amma babu tabbas akan tsinuwarshi ba zata bini ba saboda shi ya raine ni tun jarintaka.
Ranar barci sai de injiyo minsharin su Umma amma ko da wasa bai ziyarci idona ba, ganin babu barci babu alamunshi, ga tashin hankalin da ke sake ninkuwa idan na tuna da munana kalama Abba kawai sai na yanke shawarar raya daren da ibada, ko zan samu ɗauki daga Rabbil Izzati, hakance ta faru kuwa, ina kusanta kaina da Ubangijin tahalikai wata nutsuwa da rahama suka baibaye ni, aiko na ƙara ƙaimi wajen kai kokena a gareshi babu gajiyawa, haka na share dare tas da ibada ba ina neman agaji a wajen Allah, lokacin da safiya tayi zuciyata fes babu damuwa ko kaɗan saima wani imani da tsoron Allah daya sake mamaye ni, nan take na ɗaura aure da yin tazbihi da istigifari, ban saniba ko ibada ta ce tai rauni shiyasa Allah ke jarabtata da manyan ƙaddaroro iri-iri.
Kaima me karatu zaka iya gyara rayuwarka ta hanyar ƙara kusanta kanka ga Allah, ba wai sai idan matsala ta tasoka gaba ba, a'a ka tuna da Allah lokacin da kake cikin yalwa, shi kuma zai tuna dakai lokacin da kake cikin ƙunci, kuma ka ƙarfafa imaninka ta hanyar yarda da ƙaddara, kamar yanda Mubeena ke danganta al'amuran rayuwata da ƙaddararta daga Allah, kaima ya kamata ta dinga yarda cewar komi zai sameka ko ya sameka daga Allah ne, kuma rubataccene tun gabanin haihuwarka, a kwai lokacin da zaka ji ƙunci,damuwa ko talauci sun yi maka dabaibayi, a maimakon ka tsaya tunani da zargin wani yai maka asiri ko sammu, maza ka tashi tsaye ka kusanci Ubangiji, koda bai biya maka buƙatarka a lokacin ba zaka samu sauƙi da sanyin zuciya.Allah yayi manah jagora ya ƙara ƙarfafa imaninmu Amin🙏🙏🙏.
LITTAFIN ZAFIN WUTA🔥🔥🔥 PAID BOOK NE, ZA KI BIYA 500 KACAL DOMIN KI MALLAKI NAKI.
9136291920
MARYAM UMAR
OPAY
TAKU HAR KULLUM ME SON GANIN FARIN CIKINKU.
MARYAM STAR⭐⭐⭐ KE MUKU FATAN ALKIRI🙏🙏🙏.
🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥
LABARI ME CIKE DA
BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘
WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.
MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK FOUR 4
CHAPTE 41
بسم الله الرحمن الرحيم.
Ko da safiya ta yi banyi yunƙurin kwanciya barci ba, tashi nai na fara ayyukana tun kafin ayimin magana, sai da nazo hura wutar koko naga babu icce, sai kuɗin da matar jiya ta bani suka faɗo min a rai, rintse suke gam a hannuna, duk badaƙalar da akai ban sake su ba, sai da komi ya lafa sannan na tuna dasu shine na saka a hulata, ban jira kowa ba na fice wajen masu saida gawayi na siyo ina murnar ba zan sha wahalar hayaƙin icce ba, a tsanake na gama komi, lokacin kuma kowa ya tashi, nan nakaiwa Umma kununda na dama dan ta zuba mana namu, na haɗa da gaisa Abba, sai de da nasan bai huce da ni ba koda wasa da bazan nemi yi mashi maganaba, zagi da tsinuwar da bana so sune ya ɗuɗɗura min, zuciyata ta sake ƙuntata sai de banyi kuka ba kuma ban nuna damuwata a fili ba sai ma sake sunkui da kai da nai harya ƙaraci faɗanshi dan kanshi, sannan na tashi na fice ina jin ɗaci a zuciyata, gashi idanuwana sun soye babu alamu ko ɓirɓishin hawaye bare in samu in rage nauyin da zuciyata ta yi, ɗakin Mama na koma na kwanta akan cinyoyinta ina maimaita tazbihi, ahaka barci ya ɗauke ni me nauyin gaske, bata tada ni ba kuma bata sauke ni daga kan ƙafafuwanta ba har saida kiran Umma ya tada ni.
"Mama miyasa baki tasheni ba, ko kuma ki sauke kaina ƙasa, so kike ƙafafuwanki suyi ciwo." Na faɗa da sanyayar muryata ina kallonta da kumburarun idanuwana waɗanda ke cike da gajiya da barci.
"Haba ƴata ai shanuwa bata gazawa da ƙahonta, kuma keɗin nawa kike da har nauyinki zai saka ni ciwon ƙafa, ai waɗannan ƙafafuwan har jikokina sai sun hau sunyi dambarwa akai." Ni da Mama mun mance da kiran da Umma ta kwalla mi sai fira me daɗi ta ɓarke a tsakaninmu.
"Ke dan uwarki har kin isa a kira ki a gidannan kiyi banza da mutanen saboda tsinancewa, yau ni naga jaraba, so kike baƙin cikinki dana uwarki yayi ajalina ko, to ahir ɗinki wallahi nan gani nan bari, nafi ƙarfin mayu irinku, tun kafin in ɓallaki ki tashi kije za kiyi Umma aiki banzar yarinya kawai." Abba ya faɗi daga bakin ƙofar ɗaki, jikina na rawar mazari na miƙe gami da raɓashi zan wuce, aiko ya hamkaɗa ni da ƙafarshi har sai da na faɗi, da sauri na miƙe tare da nufar Umma gabana na luguden duka.
"Dama ba komi bane wankau ne na amso na gidansu Toyin, shine za ki zo ki taya ni dan sauri suke masu kayan."
Bance komi ba illa ƙure kayan da nai da ido ina ƙare musu kallo, zuwa can na nisa na kalli Umma a sanyaye sannan nace.
"Umma dan Allah kiyi haƙuri, bazan samu damar yin wankinan ba saboda banjin daɗin jikina, wani lokacin idan aka kawo zan taya ki kiyi."
"Innalillahi, yanzu Mubeena ni za ki kalla kai tsaye kice baza ki taya ni wanki ba, ni Umma ɗiyar babbanta naga takaina."
"Mike faruwa kuma, halan wani halin banzar ta nuna ma ki." Abba ya fito yana tambaya yana muzurai.
"Iroro wannan ƴar taka nema ta ke ta gagaremu cikin gidannan, wankin da mace ta kama man ne tace wai bazata iya ba, yo Allah na tuba uban mi take tsinana acikin gidannan, yarinyar da aiki ai taga dama take yi, nifa taimakonta zanyi dan ta tada jinin jikinta."