← Book details Zafin Wuta Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 13

Sashe 1

Zafin Wuta Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🔥𝐙𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐖𝐔𝐓𝐀🔥

LABARI ME CIKE DA

BAN TAUSAYI,😩MATSANANCIYAR DAMUWA,😭
KUNCIN CUZIYA,💔
SADAUKARWA,💌
ZAZZAFAR SOYAYYA ME TSAYAWA A RUHI.💋💘

WRITING BY
MARYAM STAR ⭐⭐
YAR BAIWAR JJRT.

MARUBUCIYAR📒✍️
RAYUWAR SAMHAD
DAFIN MACIJI
A DAREN AURENA
AND NOW
ZAFIN WUTA🔥

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

PAID BOOK 500 ONLY👌
BOOK FOUR 4
CHAPTE 38

بسم الله الرحمن الرحيم.

Kamar yanda Hajjo ta umurce ni, wanka nai gami da gabatar da sallah, sannan ta saka aka haɗomin kakkauran tea, dan in gasa hanjina da nike ji kamar anmin sata, sosai na ji daɗin jikina bayan na kammala shanye tea ɗin, dan haka ta sake taso ni gaba muka koma ɗakin Fauzan, inda yanzu aka mayar kamar dandalin fira, yanzu babu Papah a ɗaki, amma Mommy wacce ƙafafuwanta suka kumbura ta na nan zaune, da alama bata tashi ba daga inda take tun ɗazu, da sallama muka shiga, hannuna na cikin na Hajjo wace ta riƙe ni da kyau, a cewarta wai kar in faɗi, niko murmushi kawai nike cike da jin daɗin yanda suke gatanta ni tare da nunamin niɗin me daraja ce.
Su dukaninsu sukai min sannu da jiki, ban amsa su ba sai murmushi dana sakar musu, bana son yin magana saboda harshena yamin nauyi sosai, duba nakai gefenda nike jin idanuwanshi na ƙoƙarin buda tsokar jikina saboda azabar kallon da yake bina da ita, wata iriyar mummunar dokawa ƙirjina yai, ban san sa'ilin da na kai hannu ina murza idona ba, sai de ta tabbata azahiri ne nike ganin abin da na gani, tsananin firgici da tashin hankali ne ya baibaye ni, tsoro gami da fargaba suka sake ninka kasalar da tasaka na kasa koda motsa yatsar hannuna.
'Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, hasbunallahu wani'imal wakil.'
Na shiga maimaitawa a zuciyata, dan ji na yi bakina ya min nauyi, na kasa koda ƙwaƙwaran motsi, na ɗauki lokaci me ɗan tsayi sannan na dawo hayyacina bayan ɓacewar abin da nai tozali da shi, da tsananin kasala na ja ƙafafuwa zuwa bakin gadon da Fauzan ke kwance, sam banji wani ɗar da zaman su Mommy a wajen ba, abin da na sa ni shine, wannan Mubaraka ce ba Mubeenah ba, wacce tasha gwagwarmayar rayuwa, idona ya buɗe da wayewa irin wacce naga mutanen da nike rayuwa yanzu a cikinsu sun mayar da ita ɗabi'a, sam banji nauyi ko kunyar tallafar kanshi na ɗaura akan cinyata ba, abu ɗaya ne ke sake kwarara ni, shine jin yanda kusan kullum Hajjo ke sake maimaitamin ƙulalliyar alaƙa wacce ta saka na cure cikin ahalinsu, kalmarta a kullum bai wuce dangantani da jininsu wanda suke bala'in ƙauna da girmamawa, "Mijinki." wannan kalmar na sake warware wani ƙulli da yake a cikin kaina, sannan ta haɗu ta alwashi gami da alƙawarin da na ɗauka tun kafin wanzuwar ƙaddarar da ta sarƙafemu ni da shi ba tare da shirinmu, lokacin da Abba ya juya da jakar da aka biyashi sadaki da kuɗin aikatau ɗin da aka ɗauko ni, lokacin na ɗaura ɗamarar yin aiki tuƙuru, ba tare da gazawa ko gajiyawa, na alƙawartama kaina yin aikin ne dan in kawo sabon sauyi daga baƙar rayuwa me cike da azaba wacce na baro a baya, yanzu da nike jin ina da cikakkiyar dama da zan sake gina burina dole ne in yakice wa ta kunya wajen yin gini na daga tushe, bana so infara ɗaura bulo daga sama, sai bayan nayi nisa ginina ya rushe, zanbi komi tiryan-tiryan kuma ahankali ta yanda zan amfanu da ƙwaƙwaran ginin da zanyi dan fakewa nan gaba kaɗan idan baƙin hadarin da nike hange ya ɓalle da ruwa me ƙarfi.

"Yah Fauzan."
Na faɗa da wa ta iriyar murya wace bansan ina da ita ba.
Bai amsa ni ba, amma ya kama hannuna ya danƙe a cikin na shi, ban damu da rashin amsar ba, sai na ɗora da faɗin.

"Yah Fauzan in idasa maka labarina?."
Nai maganar ina leƙen fuskarshi, sai de a maimakon shi da nikewa maganar sai jin muryar Hajjo wace suke fira da Mommy nai ta na faɗin.

"Yauwa yarinyar kirki, ƙarasa manah maricen yau da labarai masu faɗakarwa waɗanda nasan dole zamu ilimantu da su."
Ta faɗi a ƙage da jin cigaban labarina, ɗauke idona na yi daga kanta na maida akan Fauzan yanda ya saki murmushin gefen bakin wanda ya sakani ci gaba da magana da karsashi.

CIGABAN LABARINA.

"Tun ranar da Halima ta saka ƙafa a gidan Iroro, rahama da albarka ta bai baye gidan, duda Umma ba ta huta da fitinar Iroro da amarya Halima ba, amma su sam ba ta ita suke ba, dan awannan gaɓar Iroro shareta ya nuna baisan tanayi yayi ba, ko magana ya daina yadda ta haɗasu sai a dole, shima idan ta haɗasu a dolen umarni ne zai bata, daga nan yai tafiyarshi, ganin yanzu bata ita Iroro ya ke ba, ta amaryarsa da jinjirarsa yake ya saka ta sauko, amma bahar zuci ba, ta sauko ne dan tasan matsaya akan kudaɗen da aka tsara yin wadaƙarsu da ita, amma reshe ke neman juyewa da mujiya, dan ta lura shigowa goma da Abba zai yi hannunshi da leda, ita kuma amarya Halima ta taryeshi cike da kulawa gami da girmama, haka za ta sarrafa koma minene na raba ta bawa Umma nata kaso, ita kuma da sabuwar ɗiyarta da Iroro su shige ɗaki su saka yarinyar a gaba da wasanni cike da ƙauna, ganin yanda ake waɗaƙa ya saka ta nemi sulhu da kanta, dan ta ga alama so ake a maida ita da babu duk ɗaya, tun da gashi sai sabbin tsari Iroro ke aiwatarwa shi da amaryarsa ita sun ware ta gefe.
Lokacin da aka samu sasanci Umma da mijinta harma da Amarya Halima, sai ta yi likimo akaci gaba da cin duniya da ita, nan ne ta fahimci sanyin hali da biyayyarda Halima ke da shi, koda wasa bata taɓa yi mata magana cikin rashin girmamawa ba, sai ma wani sunne kai da take idan zatai magana, bata kiran sunanta kai tsaye sai de ta ce, "Umman yara kaza, ko Umman yara anyi kazah."

Sai Umma taso tai amfani da wannan damar wajen muzguna ma ta, da Iroro ya farga da yanda Umma ke wasu abubuwan waɗanda basu dace ba nan take ya shata ma ta dogon layin gargaɗi wanda ya dugunzuma zaman lafiyarta, ya kuma saka ta ɗauki alwashin bin hanyar da ta zama silar rushewar katangar ingantaciyar soyayya, tattali gami da kulawa da uba ya gina tsakaninshi da ƴarshi da sabuwar matarshi wacce yake alfahari da samhwarta gareshi.
Shuɗaɗun abubuwa sun faru, daɗaɗa da kuma munana, daddaɗan labarin shirne ƴar Iroro jinjirara wato Mubaraka wacce ake kira da Mubeenah, ta girma, girman da yazo ma ta da tarin ƙalubale, wanda da ace za'a bata zaɓi to babu makawa zata zaɓi taita zama a tsumman jarinta, saboda girman ƙalubalen rayuwar da ta shiga."

Share hawayen da suka silalon n yi, sannan na sake kyara zaman kan Fauzan akan ƙafata ta yanda bazan takura ba, sai na saci kallon gefen da Hajjo suke zaune sunyi jigun su na saurarena, ga Sulaima wacce bansan lokacin da ta sulalo ta zauna ba, itakan tagumi tai da hannu biyu ta tallabe fuskarta, ajiyar zuciya na sauke sannan naci gaba.

Kwanaki sun shuɗe zuwa makwanni, haka zalika makwanni sun shuɗe zuwa watanni, yayinda watanni suka dinga tseren gudu har suka koma shekara, shekara ɗaya ta zo ta wuce, haka tabiyu itama ta zo ta wuce, ta uku ma haka ta shuɗe ta wuce, a cikin ta biyar ɗin rayuwa ta sauya, sauyi me ban mamaki, ƙunci ya dabaibaye zukata biyu, yayin da aka wayi gari wacce Iroro wanda nike kira da Abbana ya rasa tudun dafawa, wacce ya dogara da ita tai ɓatan dabo, ya nemi layin wayar data bashi wanda aduk lokacin da yake buƙatar kuɗi ya ke nemanta kai tsaye, kuma ya same ta, bata nuna gazawa wajen biyan shi maƙuden kudaɗe, wannan dalilin yasaka muka shiga hali, sau biyar yana aika ma ta da saƙo daga Legos zuwa Abuja amma shiru, babu alamun saƙon ya isa gareta, hakan sai ya gina wa ta katanga wacce ke neman raba uba da ƴarsa wacce tafi soyuwa a gareshi.
Hankalin Abba ya tashi sosai da ya tabbatar Hajiya Fateema tai ma shi ɓatan dabo, gashi yayi wani irin sabo da yiwa kuɗi kisan gilla, baya tsoro ko shaka wajen siyen abu me tsada, kanshi tsaye ya ke zare ko nawa ne ya biya buƙatarshi, da wannan damar ta rashin nutsuwar Abba Umma tai amfani wajen yin farraƙu tsakanshi da ni, bazan mance wa ta ranar alhamis ba, Halima wacce nike kira da Mama tai min tsifar kai ta zubamin ƙananan kitso, ta ɗauko beath ta saka min, sannan tai min wanka ta shirya ni cikin ƙananan kaya, itama ta shirya cikin tata sassauƙar kwalliyar, muka zauna akan tabarma bakin ƙofar ɗaki mu na jiran shigowar Abba.

Daga gefe kuma Umma ce zaune ta kashe ɗankwali ta na taunar cewing gum, sai waƙoƙi ta ke tana sakin habaici, tare da jefa mana harara ni da Mama, sam Mama bata ita take ba, shiyasa ko sau ɗaya bata taɓa nuna ta damu da habaicin da dayawan lokuta take yi ba.

"Oyoyo Abbana, sannu da zuw....."
Ji kake "Tarassss." ya saukemin bahagon mari wanda ya saka ni nai baya-baya na kife cikin ruwan kwatamin wanda Umma tai wanki bata sharce ba, da wani irin hanzari Mama ta tashi ta nufe ni ranta fal mamakin abin da Abban ya aikata min, bata gama shiga mamaki ba ashe, dankuwa juyawar da zatai ta na faɗin.
"Haba Abban Mubeenah, irin haka ai bai dace ba, tayaya zaka daki yarinya ƴar shekara biyar kamar ka samu sa'arka, Mubeenah ce fa, Mubeenarka, yarinyar da..."
"Ke dallah Halima sauraramin, shin tuhuma ta kike akan na daki wannan abar ko ko mi? dan rashin tunani da hankali irinnaki tayaya zan dawo gida na gaji ki wani turo wannan yarinyar ta dabaibaye ƙafafuwana tana neman kayar da ni ƙasa, ya ishe ni haka, daga yau kar in kuma ganinta akan hanyata idan zan shigo gida, idan ko ba haka wallahi yanzu na fara sauke mata maruka."
Chapter 1 · 0% Book details