← Book details Yar Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 14

Sashe 8

Yar Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kashe wayan shi Umar yayi hadi da nufan park road.
A ranshi kuwa banda gode ma Allah ba"abun da yakeyi,don yasan momy Raihana xata kulamai da amanan shi sosai,don yanxu ya dauki Amrah tamkar amana ne Allah yaba shi.
Da isan su park road Afreed yayi saurin fitowa daga motan shi.don a idon shi sukayi parking.da sauri yakarasa hadi da 'Dan dukawa ya hugging en Amrah ba tare da kyaman ta ba,duda yanda take.
Tsayawa Amrah tayi baki bude,a ranta kuwa cewa"take shi kuma wannan mutumin akan meye xai kama rungume ni?ko dai 'Dan iska ne?
Maganan Umar ne yadawo da ita tunanin ta.gata nan sunan ta Amrah plz nan da 2 weeks ka kawota school en dad dake Kaduna.but kasan boarding school ne,don haka kafin lokacin xan mata registration da komai da komai.
Afreed ne yace"OK yayi kyau ba damuwa My Amrah xomuje kiga sabuwan momyn ki.
Jan hannun Amrah yayi nan yaga ta rike Umar,kwalla ya ciko idon ta.
Don Allah hamma Umar karka barni,kar katafi momyn shi tace mun aljana.
Dariya maganan ta yabashi,sai kuma tausayinta ya kama shi.
No Amrah baxata ce ba.ita tana sonki,haka yayan ki Afreed. Umar yace hadi da nuna Afreed da hannu.
Murmushi tayi abunka da yarinta sai tace"wai haka ya Afreed momyn ka na sona?
Murmushi yayi hadi da kara riko hannun ta da cewa"sosai ma kuwa tana sonki,don yanxuma tace"nayi mata girma a 'da.sai dai kene 'yar ta.
Dariya tayi Wanda ya bayyana beauty point en ta(dimples). Nan ta saki hannun Umar hadi da cewa"toh muje na yarda ka kai ni wajen ta.
Murmushi sukayi hadi da ma Umar sallama da cewa"sai sun hadu a 'daya daga cikin school en dadyn shi.nan suka nufo hanyar Zaria.
A hanya Afreed banda surutu da yake jan Amrah ba'abun da yake.shine yatsaya nan yasai mata abu,shine siyan mata wannan.Niko maman teddy🧸 nace" ahhh lallai su Afreed anyi anwah,wannan surutu haka🤔
Kafin su Isah Zaria tuni Amrah tasaki da Afreed, don har da tayashi fira take.
Ganin haka yasa Afreed karajin da'di a ranshi. don bayan Son yakaita wajen momy ba tasaba da Shiva.
Don nan da gobe xasu koma barrack.
Horn yayi inda mai gadi yaxo da sauri hadi da bude tanfatsetsen get en.jin karan bude get yasa momy da sauri fitowa don ta tarbi 'ya'yan nata.side en Amrah tanufa hadi da budewa don ta fito.da fitowan ta momy tayi saurin daga ta hadi da rungume ta.don ko nauyin ta ba taji ba.ganin haka yasa Amrah sakarma momy murmushi.
A hankali momy tace mata"welcome home my daughter.
Shiru Amrah tayi don ba wani turanci takeji ba.tasan dai welcome don haka sai tabi momy da kallo.
Afreed ne a shagwabe yace"toh ni momy baxaki min welcome ba?wato kinga new baby.
Dariya momy tayi hadi da cewa"ae kai yanxu ka girma.don batakai nake ba,ta baby na nake.
Murmushi duka sukayi hadi da 'dunguma cikin sitting room.
Da shigan su momy takama hannun Amrah tanufi da itah 'dakin da tun jiya tasa aka gyarashi a ka kira masu decoration sukayi decorating 'din dakin.da shigansu 'dakin komai na room en coffee ne da milk. Don haka dakin yayi axaban kyau.
Bin dakin Amrah tayi hadi kallon ko'inah.nan kuma a'inah take?kodai a aljannan da malamin allon suke gaya masu ne?
A xuciyan ta take ta wannan maganan.
Momy ne ta katseta ta hanyar cewa"baby na kinga room en ki,idan a kwai abunda kike so ko bayau ba kifadamun kinji?karki boyemun komai,don yanxu nine mahaifiyan ki,mai kaunar ki,Wanda xata iya sadaukar da komai a kanki kinji?
Daga kai Amrah tayi ma momy.nan momy tace yakamata yanxu in maki wanka,kici abinci sannan kiyi bacci don nasan kina bukatan Hutu.
Momy ne tajah hannun Amrah suka nufi privacy.nan Amrah taga inda tun da take bata ta'ba gani ba,bin toilet tayi da kallo,har momy tagama hada mata ruwa a bab bata sani ba.don banda waige²ba abunda takeyi.
Ganin kalle² nata ba xai kare ba yasa momy cewa"baby Amrah bimillh.
Nan taga tuni momyn ta hada ruwan wanka.a hankali momy tafara cire mawa Amrah kaya hadi da xata cikin ruwan 'dumi.brush ta dakko inda tafara wanke mata baki da shi.tun yana jini har ya dai na,don momy yarda su Colgate tasa ta na wanke mata da shi.kafin 30 minute tuni hakoran nan sunyi wani irin mugun Haske,don har kashe ido sukeyi.
Haka ma momy ta wanke mata jikin ta Tass,don sai da ta dinga sa'bawa,ta wanke ta Maya.
Har sai da taga tayi mata yanda take so,sannan ta barta hadi da daura mata towel suka fito bed room en ta.
Bayan ta tsane haka momy tashefe jikin ta da creams basu kyau da tsada hadi da goga mata powder kadan.
Wani English wears mom Rayhana ta samata.Riga da skirt mai launin pink da white.kyaun da tayi ita kanta Mom Rayhana sai da tace wowwww.😘
Bayan Afreed yagama kintsawa ne yafito hadi da nufan dirning, komai an tanaje shi naci da sha.zama yayi hadi da jiran fitowan su momy.dai²mom na fitowa hadi da nufo dirning 'din.hankalin shi na kan waya don haka baiga xuwan su ba.sai dai momy da tace"seat here my baby.nan tana ma Amrah kujera hadi daxama.nan Afreed ya dago idon shi nufan bakin shi cewa yy"wow so cute.mom Amrah ne wannan?
Dariya mom tayi hadi da cewa"No son ba itah bace,mai kama da ita ne.
Dariya yakuma hadi dacewa"wlh momy na tayi kyau sosai.
Murmushi momy tayi batare da tace"komai ba tafara serving en su.
Gaban Amrah momy ta'ajiye mata plate en pride rice da chicken sai ta Dora mata spoon da knife. Lacasera ta ajiye mata hadi da fara serving en Afreed.
Bayan momy taga ne har tafara cin abincin ta.kaman ance ta kalla Amrah, nan taga banda juya spoon ba'abun da takeyi.
Amrah yah bakya cin abincin?
Momy tace hadi da mai da hankalinta ga Amrahn.Wanda yasa Afreed saurin kallon Amrahn.
A hankali tace"momy ban iya ci da wannan bane.ta fadi hadi da nunama momy spoon. Murmushi Afreed yayi dacewa"bari inkoya maki. kallah.
Momy ne ta katse shi dacewa"no bari in baki da kai na.ka koya mata letter. Nan momy ta hau bama Amrah abinci a baki har sai da ta tabbatar da ta koshi sannan suka tashi hadi da nufan bedroom don Amrah tasamu tayi bacci.

Washe gari Afreed takoma barrack, bayan tafiya shi ne momy ta dauke ta suka nufi wani katon shopping mall.English wears tasiya mata kayan gayu iri²ba irin Wanda bata sayama Amrah ba.
Bayan komawan Afreed ne yakirasu har suka gaisa da Umar. Umar yaji da'din yanda yaji Amrah na cikin koshin lafiya...

Safiyar littini garin Kaduna cikin wata makaranta da ake kira *ASHSAFF INTERNATIONAL SCHOOL*
Staffs ne da students gaba daya a asmble ground...tun daga SS xuwa jss one gaba daya a farfajiyan makarantan.malaman su kuma daga saman su da'alama first term ne don da new students aciki.
Amrah ne tataho fillin assembly en kaman yanda aka kwatan ta mata.
Gaba daya students da malaman idon su takoma gareta.ciki harda Umar farouq,kowa cewa yake wannan 'YAR WAYE??ganin irin kyaun da tayi,da kaganta kaga 'ya'yan Wanda naira ta tsumasu.shi kanshi Umar bai ganeta ba. Don sanye take cikin uniform din ta Wanda yake fadi skirt kuma dark blue da ratsin yellow.gashin ta ne dayasha gyara mom tasamata ribom fari,hadi da Dora mata baret a kan gashin.kadan ta kuwa wani jubga jubgan combo's ne fari,sai kaman bayan ta baki.
Wata malaman ne da ake kira Anty Dorcas tace mata.hyy dear which class ar you?
A sanyaye tace"jss 1
OK go to that Line. Layin jss tayi mata pointing.nan Amrah tanufi layin,teemah ne tayi mata alama da hannu wato taxo nan.daganin haka yasa Amrah xuwa bayan teemah ta tsaya.
Dama cikin introducing din Kansu sukeyi,don ka'idan school en kenan. Duk Sabon xuwa sai yy introducing en kanshi tukunna.
Bayan en SS 1 sunga mane sai en JSS 1 sukafara a haka akaxo kan teemah fita tayi hadi da nufan saman inda Malam suke,nan tagabatar da sunan da na class en ta.sannan ta koma layin su.
Cikin tafiya ta kaman mai tausayinta kasa take takawa har ta Isah saman Dan steps din da malaman ke kai,hadi da pacing en daliban a sanyaye hadi da xaxxakan muryan ta tace"my name is Amrah moh'd suraj.
Nan fillin ta dai ihun da sowan daliban wasu na cewa"beauty wasu kuma na kwaikwayon muryan ta.
Jin koda Umar yayi tace"sunan ta Amrah sai da yahau tantama itace kuwa Amrahn nashi.
Xuwa tayi xata wuce malaman kallon shi tayi hadi da sakarmai kayattacan murmushi😊

Free page xai kare a page 15 mai son cigaba novel din xai turo #100 MTN idan kuma VIP ne #200
Ma wannan number 09137392680

More typing...
More comment

Maman teddy ce🧸
[12/29, 9:55 AM] mmn tedy: *TYPING...✍🏻*

*MANAZARTA WRITTERS ASSO...*
23/11/2020

*MARYAMU SARAUNIYA RETURN*
( *YAR WAYE???*)

*story and written by:*
*Ayshar moh'd* (maman teddy🧸)

Facebook @maman teddy.com
*wattpad*
Eashert 2020

*GARGADI*
Ban yarda wani ko wata suyi amfani wajen juya mun labari ba😎

*DEDICATION*
This novel is dedicate to my Creator and inspiration. After my creator is the vehicle that drove me to the word from the person of Alh.Mohammed and haj.safiyya...
Finally this novel is dedicated to every pupils and my fans who love what I love Hausa novels❤️

~About the novel~
Labari mai cike da tsantsan soyayya, tausayawa hadi da makirci iri² pure love and pity story📚🖊️

Episode1️1️

____________________________________

Koda Afreed yakoma cikin sojoji duk in an tambaye shi aminin nashi cewa yake ya Dan yinisa.don haka bawanda ya kawo komai a ranshi,don ansan halin farouq en.bason xama cikin mutane yake ba.ya gummaci kullum ya dinga yin abunda ya dace da rayuwanshi.
Koda Ammar ya tambaya shi Umar haka shima yace mai yanufi cikin daji...
Don haka nan Ammar ya cigaba da sha'anin shi.
Shiko Afreed yakasa sukuni tunanin farouq yakeyi,ko a wani hali suke yanxu?ita kuma wannan yarinyan 'YAR WAYE??? Ganin bamai bashi amsa yasa shi mikewa hadi da nufan Ammar da yake can suna xuba love da precious.
Chapter 8 · 0% Book details