← Book details Yar Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 14

Sashe 14

Yar Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahhh...ahhh...maxajen nawa ne agidan yau? Lale marhaban,ahhh su Umaru ne da Ammaru sannun Ku da xuwa.
Hajiya kaka take cewa" cike da farin cikin ganin en jikokin nata.
Murmushi sukayi hadi da cewa"hmmm yau dai munxo ganin er tsohuwa ne,muga lafiyan ta.
Hajiya kaka ne tace"kai Ku rufamun baki,ni nan da kuka ganni na fiku lafiya,irin abincin da nake ci ba kwaci,kun tsaya bin na zamani da duk an kashe da sinadarai.
"Ammar ne cike da biye ma " yar tsohon yace"haba hajiyan mu jube mu fah,gadagau muke,don lafiya har yy mana yawa mah...
Maganan da Ammar yayi shiya sa Umar dariya sosai,don duk insun xauna da Hajiya kaka sai anyi dariyan lamarin nasu,Ayi fada a shirya,a haka kullum suke.Amma a haka in Hajiya kaka bata gansu na kwana biyu ba,ta dinga magana kenan.musamman Umar da yake da sunan mai gidan nata.
Dariya sosai Umar keyi...Hajiya kaka ne tace"hmm kai kanka mai gidana kayi dariya ai,hmm toh yanxu dai kuje Ku huta sai mu xauna Muyi hira,don yau na gaji, kiran iyayen Ku xanyi akan Ku fitar mun da matan da xaku aura.jiku duka kun haura shekara 30, amma ba kwa ko maganan Aure.toh yau baxa ku koma ba, sai naji kwakwkwaran magana ga iyayen Ku...toh Hajiya wannan xuba haka? Mai da wukan,don ni tuni nasamu Wanda xan aura.
Ammar yace"hadi da yin ma Hajiya kaka murmushi.
Cike da rashin gamsuwa da maganan Ammar Hajiya kaka tace" anyah kuwa da gaske Kakeyi Ammar? Nifah nasanka da shegen son mata,kace yau wannan gobe wancan,har gomma Umaru na.
Murmushi Ammar yayi hadi da kallon Hajiya,nan yace" hmm Hajiya da gaske fah nake wlh inna xauna inah fada maki yanda nake son ta sai mu bata awan ni bana ma ba.
Kai Mara kunya rufe mun baki,wlh Ammar baka da kunya mai gidana ba haka yake ba.Hajiya kaka tace"hadi da kallon Umar da yake danna wayan sa,kaman bai San suna yi ba.
Toh Hajiya na lura kaman kishi ki keyi,amma koda kishi xai kashe ki sai na nuna maki hoton ta yau.sai dai Umar din ya biki shima Ku mutu tare.duka Umar ya kai mai hadi da cewa"kai toh bari in fada maka duk kyaun budurwan naka baxa ta kai Hajiya na ba,don da tsohon xuma ake magani...Hajiya kaka ne tace "kyaleshi Umar ya nuna mun Wanda yake ikirarin tafi ni.
Dariya Ammar yayi hadi da cewa" shiyasa kullum nake jin ki a raina ya kaka,bari kiga my shining star,my beauty,Angel....kai duk ya isah, ni dai nuna mun yarinyan.bama ganan banxa ba.murmushi Ammar yayi hadi da cewa"toh Hajiyan mu bari ki ganta.
Kauda kai Umar yayi don shi yanxu yarasa ya xai fara tunkarar ta,Wanda ya dade da son ta a birnin xuciyan shi,kullum da soyayyan ta yake kwana yake tashi,Wanda kullum yake mafarkin ta xama uwar "ya'yan shi...nan take lokaci guda ya fada duniyan tunanin ta.Wanda yasa ko su Hajiya kaka ba yajin irin draman da sukeyi da Ammar 'din.
Hajiya rufe idon ki,kiyi addu" a don kyaun ta in kika gani sai ya firgita ki,don ba irinsu a nijeriya,kin gako baki saba gani ba.mtsswww Hajiya kaka tayi tsaki hadi da cewa"ni bana son shashanci in xaka ban kaban in baxaka nuna mun ita ba,ka kyaleni kawai.murmushi Ammar yayi hadi da cewa"eyyah Hajiya kiyi hakuri kar kishin ki ya fito sarari mana,ke din ae har yanxu ta daban ce.haka yayi ta xolayan Hajiya kaka sannan ya bata wayan nashi,hadi da nuna mata hoton Amrah.
Hajiya kaka batasan lokacin da bakin ta ya subuce ba tace"kai masha"Allah,a inah take? 'YAR WAYE??? kuma.hmmm Hajiya a Zaria take,Hajiya ne tace"kai masha,Allah.mai gida na farouqu kai fah ina taka matan? Kai kuji mun tsohuwa da shishigi,toh ni bani da wata Wanda na keso a yanxu.Hajiya ne tace"toh ai shi kenan Allah ya Baku mata duka na gari,Wanda xamuyi alfahari da su nan gaba.hada baki sukayi wurin cewa" Ameen.mikewa Umar yayi hadi da cewa"Hajiya na bari mu shiga daga ciki.toh farouqu yanxu nima xan shigo...barin sitting room din Hajiya sukayi hadi da nufah dakin su da yake permanate na sune.bin Umar da kallo Hajiya tayi hadi da cewa"a xuciyan ta,tabbas a Kawai abunda ke damun farouqu,shiru tayi hadi da cewa"komai nashi kalan na mahaifiyan shi,murmushin sa,miskilancin,yawan alkhairin sa,kwallah ne ya ciko idon Hajiya kaka, nan ta daga hannu hadi da yima mahaifiyan farouq din addu'an duk inda take allah ya bayyana ta,inkuma ta mutu ne Allah yaji kanta,yasa duk abun da Hajiya tayi mata ta yafe mata...
Xaune feenart take a dirning ba kunya, da su dadyn farouq hadi da shi kanshi farouq din.don xasuyi break fast ne. addu'a Umar yayi kafin ya fara cin abincin.
Kallon Juna momy kubrah da leenart sukayi,don xuciyan su fari take kal yau,don sun San bukatan su ya biya ya gama.
Haj.kubrah kuwa cewa"take a xuciyan ta ai yau Umar ko kwana kake akan buxu kana saukan alkur'ani kullum yau sai wannan maganin ya cika...
Haka haj.kubrah su kayi break fast cikin jin dadi tana cin abincin ta hankali kwance,haka ma leenart, don har wani shige mawa Umar din take,shi kuma sai shareta yake,yana wulakanta ta,don wani abun raga mata yake yi saboda momyn na shi...anan daddy yake kara mai maganan company Wanda yace" mai nan da 1 week xa"a bude companyn insha,Allah...
Murmushi Umar yayi hadi da cema wa"daddy Allah ya yarda daddy.haka suka dinga cigaba da firansu na kasuwancin su da sauran abubauwa,don komai daddy xai yi sai ya nemi shawarar Dan nashi,don shi daddy irin mutanen nan ne hoxlar Wanda basa tsaya mawa abu daya,sai gashi Dan nashi ya biyoshi har ma yana Neman yafi uban na shi.daddy ne kan ya tafi yace" mawa Umar yaje yayi tunanin sunan da xai sa ma companyn na shi.a haka sukayi suka rabu da daddy akan xai tunanin sunan da xai sa mawa companyn...

Amrah ki sauko kiyi lunching ko don kinga yau ba school kuma Ammara ta xo? Murmushi su Amrah da Ammarah sukayi hadi da cewa"toh mom gamu nan sakkowa.mom ne ta juya hadi da cigaba da shirya masu lunch din na su.sai da sukayi consuming kusan 30 minute sannan suka sakko,tahowa suke a natse,inda mom zaituna ke bin su da kallon sha,awa da kauna,kullum shakuwan su da son junan su ka ruwa yakeyi,don yanxu ta kaima in Ammarah ba taga Amrah na kwana daya ba, bata iya sukuni.haka itama Amrahn,don da in Amrah xataje gidan su Ammarah mom zaituna hanata takeyi,amma yanxu ganin shakuwan su da yanda itama Ammarah ke xuwa yasa mom barin Amrahn,Wanda da Afreed yaji labari bakara mun fada yayi ba.sai daga baya yaga yanda itah Ammarahn bata iya kwana bata ganta ba,da yanda take kwana a gidan mom zaituna kaman gidan su,yasa Afreed amin cewa"da kawancen na su.don yanxu har kwana Amrah keyi a gidan su Ammarah, Wannan yasa matan baban Ammarah sabawa da Amrah, Wanda yanxu alhmdllh tana jawo Ammarah a jiki sosai.a haka har tanemi sabawa da doctor zaituna,inda suke xumunci fiye da tunanin mai tunani.
Xama Ammarah tayi a daya daga cikin chairs na dirning din,haka itama Amrah,sun fara serving din kansune dai² Afreed yayo sallama...sanye yake cikin wata t.shirt na sojoji, wandon jikin shi na sojoji haka takalmin shi, daka ganshi kaga irin maxan nan da"ake cemawa ingarman namiji.murmushi yayi hadi da lumshe segxy eyes din shi,hadi da budewa,da dan gudu Amrah ta nufe shi,bude hannayen shi yayi hadi da ware su gareta,da sauri ta shige jikin shi hadi da rungume shi.a hankali da sanyayyayiyar muryan ta tace"welcome back my boooo.
Murmushi yayi hadi da kama hannun ta da cewa"ya kike my Amrah?
Lfy ya Afreed...Amrah tace hadi da sakarmai dariya.OK masha"Allah my baby muje ko?
Afreed yace"hadi da kama hannun Amrah sukayi inda su mom zaituna suke.
Barka da gida momy,Afreed yace hadi da samun daya daga seat en ya xauna.
Shafa kanshi momy tayi hadi da cewa"ya hanya my son?lafiya momy ya Amrah?murmushi mom tayi hadi da cewa"gata nan ae har yau taki hankali.dariya duka sukayi hadi da kallon Ammarah ne tasaci kallon mom ba tare da sun gani ba tayi ma Amrah gwalo,hadi da cewa"har yanxu kin ki yin hankali,kukan shagwaba Amrah tasa hadi da bubbuga kafan ta,tana cewa"sweat mom kin ga kinsa Ammarah tana yimun gwalo ko?
Dariya Afreed da Ammarah suka sa,nan momy tayi saurin rungumo ta hadi da cewa"rabu da su babyn momyn ta.
Haka sudai su Afreed ke tayin dariya don yanda mom ke treating din Amrahn wani xubin kaman karaman yarinya er shekara biyar.
Afral maxa ki shirya kifito don xuwa gombe da Dan karan nisa fah.momy tace"hadi da daukan hand bag din ta ta nufi farfagiyan gidan, inda daddy ke jiran su don su tafi gomben...
Don yanxu Afral tuni ta dauki kaddararta na rashin daddy da mom Rayhana a matsayin iyayen ta,don yanxu har su daddy sunyi bin cike akan exchangin din Afral din da,akayi,inda suka gane cikin kauyen da diyar su take,don haka ko da Afral taji labarin momy xasu,sai tace"itama xataje.haka daddy ya amince akan xasuje da itah Afral din.nufan Zaria suka farayi inda suka biya G.R.A suka gaida Hajiya kaka sannan suka dau hanyar gombe,ba tare da Hajiya kaka tasan inda xasu dosa ba.
Amrah ina ne xakije kk kokarin saka face mask?doctor zaituna ta tambayi Amrah dake shirin fita.budan bakin Amrah cewa tayi momy xanje shagon can ne,na waje na siyo choculate don nawa duka sun kare.OK a dawo lafiya.mom tace"hadi da nufan stairs...
Xumbulelen hijab. amra tasa hadi da rufe fuskan ta da face mask don sanyin da akeyi,ga kuma iska.nufan shagon takeyi har ta kusa,sai taxo xata tsallaka titi,batare da ta lura ba,wata mota ta kusa kade ta.saurin jah baya Amrah tayi Wanda yasata buguwa da wata motan dake gyefen ta.da sauri honourable moh'd ya fito hadi da cewa"sorry my daughter ban ji maki ciwo ba ko?
Kakkabe jikin ta Amrah tayi hadi da cewa"ehhh.daddy ne yace"ko in kai ki asibiti ne?da sauri Amrah tace"A,a ba,abun da yasa meni,hadi da nufan shagon mai provision din.komawa mota daddy yayi,inda momy tayi nisa wurin kallon Amrah,don tunani ta tsaya yi a,inah tasan idon nan.
Ita ko Afral sai da sukayi Dan nisa ne tayi gigib,kaman Wanda aka tsungule ta tace"daddy waye wacannan??? A inah take???

More typing...
More comment

Maman teddy ce...
Chapter 14 · 0% Book details