← Book details Yar Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 14

Sashe 12

Yar Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da isan ta tayi cikin sitting room en daddy, aiko yana xaune shi da momy,kuka Afral tasa hadi da xubewa jikin daddy, girgixata ya hauyi amma bata fitar da numfashi,da sauri ya kimkimeeta hadi da nufan mota cikin xafin nama.momy ne tabiyo bayan su da sauri hadi da shiga motan.
Da kanshi daddy yayi driving har suka Isah asibiti.da isansu aka Karba Afral cikin gaggawa.
Haka daddy keta safa da mawa a asibitin,Wanda akaa tambaya shi blood group nashi.da na momy nan yabada hadi dacewa su duba mai Afral da sauri,kar wani ABU yasa meta.

Haka likitoci ke ta tsaye akan Afral har akasamu nasarar farfado wanta.
Da labari yasamu daddy yayi matukar farin ciki,Wanda yakasa sukuni har sai da ya shiga dakin shi da momy.nan sukaga Afral na bacci gefe guda kuma ansa mata drief.
Wata nurse taxo hadi da sanar masu da kiran doctor, kafin su fita sai da momy ta yima Afral addu,a sannan sukayi office en likitan.

Da shigansu suka gaisa da doctorn.
Bayan nan shiru ya biyo baya,don shi kan shi doctorn yakasa masu bayani...
Sai da yanisa sannan yace"plz Hajiya Afral er kice?
Momy ne tace"kwarai kuwa,'ya tace.
Doctor ne yace"xan iya sanin a asibitin da kika haifi Afral?
Ba tare da komai ba momy tace"a garin gombe,wani asibiti da yake da suna Al madina.
Shiru likitan yayi na wasu sakanni kan yace"xaki iya tuna likitan da ta amshi haihuwar ki a wannan lokacin.
Gaban momy ne ya fadi tuno da doctor zinah,tabbas itah ta amshi haihuwar Afral.
No baxan iya ba,but meye doctor?
Momy ta tambaya cikin rashin kuxari.

Doctor ne yanisa hadi dacewa"I'm sorry to said that Afral is not ur biological daughter.
Cikin rudu da karaji momy tace"mai kace likita.
Daddy ne ya daka mawa doctorn tsawa hadi da cewa mai kk nufi?I din't understand the matter.
Cike da tausayawa doctor n yace"nasan xakuji wani ABU na dabam,but munyi bin cike ga kuma takardun bincikenmu na cewa"Afral ba 'diyarku ba ne...
Wani kara momy tasaka hadi da xubewa kasa......

Hausawa na cewa laifin dadi karewa,a yaune free page dina ya kare,mai son cigaban novel din xai turo #100 MTN idan kuma VIP ne #200 ma wannan number 09137392680/08081202932.

Hajiyata yanxu labari take karki sake a baki labari,don ki karanta da kanki sai tafi maki armashi ko da bansan ba...

Maman teddy CE...
[12/29, 9:55 AM] mmn tedy: *typing...*
30/11/2020

*MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION*

*YAR WAYE???*
_(purely love and pity story)_

*story and written by:*
_maman teddy_

*GARGADI*
Ban yarda wata ta fitarmun da littafi ba...

Page 16 - 17

___________________________________

Saurin rikota Honourable Muhammad yayi,Wanda da sauri doctor salis ya kwala mawa wata nurse kira. A hanxarce taxo hadi da kama Arch.Rayhana xuwa emergency room.don ko numfashi baya fita mata.
Daddy kuwa gaba daya yagama fita hayyacin shi,jiyake cikin wani irin sabon yana yin da bai ta'ba shiga ba a rayuwan shi.
Koda aka shiga da momy emergency banda kaiwa da komowa ba"abun da daddy keyi.ya rasa mafita ta a rayuwanshi.

*BANGAREN UMAR DA AMMAR* kuwa cike da bacin rai suka bar side 'din Ummu maryam.koda suka shiga side 'din Umar. hada kayan shi ya hauyi ba tare da yace ma Ammar komai ba.kallon shi Ammar yayi hadi da cewa"Umar ina xa kaje ne?badai gidan momy ba?don yau daddy cike damu yake,mun taba 'yar lelenshi.
Murmushi Umar yayi hadi da cewa"ba gidan daddy xanje ba,yau xanko ma barrack Ammar. Wani irin barrack kuma Umar?
"Ammar yace" hadi da son jin na bakin Umar 'din.shiko Umar bai kula shi ba sai daukan kayan shi yayi hadi da nufan hanyan fita.
Bin bayan shi umar yayi, don yasan yau bamai dakatar da Umar daga tafiyan na shi.da xai shiga mota ne Ammar yace"toh uba na 'yan zuciya a gaida major.bai bashi amsa ba har driver yaja motan suka bata iska xuwa Kaduna...
Addu"a Ammar ya bishi da shi,kan shima yafitar mawa kanshi da mafitan ' abun da xaiyi.kasaitaccen murmushi yasaki hadi da shafa sajen fuskan shi,tunowa da yayi da Amrahn sa.don haka a lokacin ya yanke shawaran nufan Zaria don yau sai yaga Amrahn xai iya samun sukuni.dai² wayan shi ta hau 'kara,screen 'din wayan ya kalla hadi da ganin sunan Lubnah, Jan dogon tsaki,yayi hadi da maida wayan ya nufi motan shi.
Koda ya Isah gida bai tunanin komai ba,ganin basu daddy a falon.don haka da murna yayi dakin shi hadi da daukan abunda ba arasa ba,sannan ya fito hadi da daukan hanyan Zaria.
Xaune Amrah take momyn ta na yimata lalle a hannu,don doctor zaituna banda ciwon baki ba"abun da take mawa Amrah,akan bata son yin lalle...
Hmmm momy wlh banason wannan 'yan daudun nayi mun lalle ne shiyasa."Amrah tace"hadi da turo 'dan kararramun bakin ta.
Murmushi momy tayi hadi da cewa"toh Amrah na, Ae kina son nawa lallen ko?ehhh mana momy kimun mai kyau,karfe 10am xamu shiga lectures.
Amrah tace"hadi da kallon tan kamemen agogon falon.
OK ae lallen na da kyau,yanxu xaiyi.bayan Amrah tagama shirinta staff ta nufi A.B.U da xuwan ta su teemah ke sanar mata da cewa"yau xasuje asibitin A.B.U shika.da sauri suka nufi school bus,don basa son a cika motan basu samu wurin xama ba.
Bayan sun Isah ne,banda aiki ba abunda su Amrah keyi,sune bin wannan likitan can,sune bin shi can.cire drief,kama majinyata xuwa privacy da sauran aiyukan majinyata.Doctor Samuel ne yace"Amrah taje ta cire mawa wani patient drief.da isan su wurin Ashe irin tsofaffin nan ne fitinannu.sannu baba."Amrah tace"hadi da kokarin cire mai drief.su feenart da sauran students duka suna bayan ta,ana iyayi a dole ga professional doctors din nan.
Wani xullo wannan tsohon yayi hadi da fixge hannun shi.ganin haka yasa Amrah saurin jah baya da su teemah.cike da bala'i da masifah tsohon ya hau cewa"ni xakuxo Ku koyi aiki a gangar jikina? kufitah kubani wuri....cikin tsawa yayi maganan,jin haka cike da firgici su Amrah sukayi waje.sauran majinya ta kuwa banda dariya ba'abun da sukeyi...koda ko su Amrah suka fita banda dariya ba"abun da sukeyi,don lamarin tsohon nan ba"abun da ya basu sai dariya...

Bangaren daddy da Arch.Rayhana sai dai muce alhamdullilah.don momy Rayhana xaune take banda hawaye ba"abun da takeyi...daddy ya xamuyi yanxu?ya xanyi da Afral?kuma ni inah 'ya ta?Afral daddy "yar waye?
Momy Rayhana cike da kuka take maganan.inda daddy yakasa bata amsa,don shi kanshi bai San ya xaiyi da Afral ba.cike da dauriya da maxan taka daddy yace" karki damu Rayhana,kuma maganan Afral mu rufe shi anan na cewa"mu ba iyayen ta bane.don ba Wanda yasani sai mu din.momy ne tayi saurin katse shi hadi dacewa"haba daddy kaji fah inda akace mana namu 'yan take? cikin wannan bakin kauyen xan bar jini nah?impossible daddy,I can't.momy tace hadi da kauda kanta gyafe.
Cikin tautausar muryan lallashi daddy yafara cewa"No ba haka nake nufi ba,kinga xai yiwu itah "yan mu ta saba da rayuwan kauyen kuma may be tana jin dadin can.
A" a daddy ba Wanda xaka ganshi cikin kauye kace yana jin da'din xaman shi a can.wai toh ma munje munga halin da take ciki ne?kamata yayi mufara xuwa muga irin rayuwanta da takeyi acan.indai tana rayuwan wahala gaskiya baxan iyah barin ta ba dadyn Afral.
Momy takarake maganan da kashe daddy da idonuwan ta.OK badamuwa Rayhana but kiyi mun alkawarin baxaki taba tona asirin cewa"Afral ba diyan mu ba ce.
Sai da momy tayi shiru na wasu mintoci sannan tace"toh daddy nayi maka,amma ya makoman "yata?
Daddy ne yayi saurin cewa" karki damu sai murinka xuwa muna kulawa da itah,koda ba tare da tasan mu iyayen ta bane.momy ne ta daga mai kai cike da gamsuwa,don yanxu ta yarda da xancen daddy tun da dai xata rinka ganin 'yar ta duk lokacin da taga dama.
OK daddy tashi mu duba baby Afral muga halin da take ciki.
Cike dajin dadi daddy yace"gaskiya kam,xaki iya xuwa kuwa Rayhana?murmushi momy tayi sannan tace"xan iyah mana dadyn Afral.A hankali momy ta mike hadi da bin hanyar fita.daddy ne yabi bayan don xuwa dakin da aka kwantar da Afral 'din....
Mutuwan tsaye momy tayi sakamakon ganin Wanda bata xata ba.dady ne yace"muje mana hadi da yin gaban ta.shi kan shi tsayawa yayi ganin su a tsaye a bakin kofan ba karamun daga mai hankali yayi ba.shi kenan sirrin da suke kokarin boyewa ya bayyana,ko ya xasuyi yanxu?

_______________________________

More typing...
More comment

Maman teddy ce
*08081202932*
[12/29, 9:55 AM] mmn tedy: *Typing...*
*1/12/2020*

*"YAR WAYE???*

*story and written by:* Aysha moh'd (Maman teddy)

*GARGADI*
Banyarda wani ko wata suyi amfani wajen Satan fasahana ba😎 kema Hajiya kije ki girgire naki....😍🤩

*DEDICATION*
I dedicate to you my dear fans like your comment😍kadan daga cikin comment din *"yar waye???*

🌹🌹💦YAR WAYE 🌹🌹💦

COMMENT

😏😏😏😏😏😏😏😏😏😏Kai wannan zuciya na ya Umar ai se Allah, Allah dai ya sanyayamai zuciyarsa😏😏😏😏😏😏😏😏😏

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞Allah sarki Ammar Allah ya barka da Amrahn ka💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

😰😰😰😰😰😰😰😰😰😰Allah sarki Mummy Rayhana Allah yasa yarki tana lfy ,ke kuma Afral Allah ya baki lfy ya kuma tashi kafadar ki🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽

🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽Allah yasa ba as irinsu Mummy bane ya tonight.I pray 🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽

Up
Up
🧸🧸🧸Maman Teddy🧸🧸🧸Allah ya Kara basirah da karfin ido.Muna yinki ❤️💯
*by zarah*😍😘

Page 18 - 19

________________________________
Chapter 12 · 0% Book details