← Book details Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 38

Sashe 8

Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

🙎 YAR BAIWAH 🙎1⃣8⃣
Maman Ussee😘
Doctor ne ya fito daga room dinda aka ajeyi Rukayya , Daddy ya tarbesa cikin hanzari yadai likita ,cemasa kawai yayi ya biyosa zuwa office din sa, batare dawani bata lokaci ba yabi bayansa mummy kuma Room dinda Rukayya take ciki ta shiga koda tashiga ganin Rukayya tayi kwance abinta sai sharar bacci takeyi ana mata karin ruwa,
Tausayintane ya kama , Allah sarki Baby Ruky Ashe bakida lafiya shine kikaki fada min har sanda Abu yayi tsanini ban kyau taba daban gano cewa , ur not felling too well ba but I promiss daga ,yau zan kara himma wajen kula dake banason ko kadan wani Abu yasameki Rukayya Allah yabaki lfy , ta sa hannu ta Shafa fuskarta mai haske ,
Abangaren daddy kuma bayan yashiga office din Doctor ya zauna, Doctor yamaida hankalinsa a gurin daddy Dama ba wani dogon matsala bace kawai dai tasha wahala ne matuka watakilla ko ansaka wani aiki ne mai wahala or something, like that kuma ga period, dinta yafara zuwa da ciyon Mara Wanda duk shine yakara tsanata akan yawan. Dukin da tayi tayi that why yasaka mata fever Dan jinin bai sauko, a gurin. Da yakamata ba but Insha Allah she wll soon be fine, yanxu tana bukatar Hutu nayi mata aluran bacci Insha Allah koda zata tashi ba wata damuwa kawai dai a kiyaye gaba Dan gudun faruwar irin hakan,saboda worm dinta bayada karfin. Da juriyar daukar wahala sosai irin hakan nan,
Ajiyar zuciya Daddy yayi kamin nan ya yima Doctor godiya yakarbi takardar magani Dan yaje yasayo,
******* ******* *******
A gida kuwa Sajeeda banda aikin kuka ba abinda takeyi su Fadil ke Rarrashinta hankalinta duk yakasa kwanciya, ganin har 6 :pm ba mummy kuma ba Daddy gashi ita. Ba wayace da ita. Ba balantana, takira taji ko lfy duk ta rude ta kasa aikata komai tunanin, a wane hali yar uwarta take a ciki kawai takeyi jitake, kamar ta dawo da ciyon yadawo kanta, tun daworsu har yanxu uniform, ne a jikinta , takasa cirewa ko Islamiya ma yau. Ba Wanda yaje a cikin su gidan yayi quit sosai, ba dadi su Abdallah ma haka suka yita bata hkr amma, takasa daina kuka shigewarsu sukayi nasu dakin kowa yayi jugum,
Mummy na zaune ita da Rukayya daketa barci daddy yashigo, da ledar magani an rubuta NATA Benji Pharmacy,
Ajewa yayi ya zauna akan kujera yafara jeroma mummy question , kinasa Rukayya aiki mai wahala ne? Meyasa baki fada min batada lfyba saida Abu yayi tsanari? Dama kinsan batada lfya Amma shine baki badaminba? Wane aikine kikasa ka Rukayya mai wahala a yau? Answer me ,
Sukuyarda kanta tayi kasa tafara bude baki Daddyn Yara wllhi bansan cewa Rukayya batada lfya ba kaima sanin kanka ne lfy lau muka rabu da ita dazu da safe ,aiki kuma ni banda shara da wanke wanke ba abinda suke min a gida yauma ba abinda sukayi da dawowarsu daga school ne fa nakiraka a waya Dan Sajeeda CE ta shigo da Rukayya ko tafiya ma bata iyayi kawai dai mujira farka warta sai mutanbayeta ko dakwai wani mai takura matane bamu sani ba,
It's OK Allah yabata lfy kinga an kusa magrib zanje gida na duba su Sajeeda sai na taho muku da sauran kayan bukata Dan nasan maybe nan zaku kwana, badamuwa mummy ta amsa .
Da zuwansa gida car kawai ya ajeye ya fada masallaci Dan ya gabatar da sallah, bayan yakarene yashiga cikin gidan , bakowa a Fallon kiran sunanta yafara yi a Hankali Sajeeda, Sajeeda , naam ta amsa cikin sanyi ta fito INA k'annen naki , Daddy inaga sun tafi masallaci OK to ki kwantar da hankalinki sister dinki taji sauki sosai ki je dakin mummy dinku kidauko , blanket da kayan ta ki hada harda na Rukayya ki dauko cups da spoon da flalet, kinji ki dauro Ruwan zafi ki saka a Flak's kamin nayi wanka kin shirya komai sai muje hospital, din Ku dubu Rukayya kinji To ta ansa kamin nan ta fara hada abinda aka umurceta tayi guri daya , Basu bar gidan ba sai bayan Isha ,saida Daddy yafara biyawa super market ,ya sayo musu kayan tea kamin nan ya biya restaurant, yayi musu take away,
Basu zarce ko INA ba sai a ,Asibiti, Daddy ya dauko sauran kaya yayinda Sajeeda dasu Abdallah suka dauko saura, Room dinda aka kwantar da Rukayya nan suka shiga sai dai har yanxu bata farkaba Sajeeda da gudu ta isa bakin gadon ta k'amk'ame ta tana Hawaye Mummy CE ta CE ke lfyarki kuwa inkinka jimata ciwo fa kin wani riketa kamar saceta za,ayi shikuma Daddy tausayinsu yagani kasancewar yasan yanda suka shaku da junansu ,
Cikin bacci Rukayya taji kamar an riketa bude ido tafarayi tana gani bishi bishi kamin idonta suka bude fabaki daya, ta kalli Sajeeda Sist meya faru dani Inane nan, Daddy ne ya dafa kanta sorry Babynah nan Asibitine bakyada lfya ne shine muka kawo ki hpe dai bawata damuwa ko eah ta amsa yayinda tashiga tunanin abinda Yafaru da ita dazu tsaki taja a cikin zuciyar ta sake cewa mugu kawai saida yayi sanadin kwanciyata asibiti Allah ya isana mummy CE ta taimaka mata tashiga toilet ta gyara kanta duk kunya ta isheta bayan ta canja kaya mummy ta hada mata tea mai kauri ta mika mata tasha sai Sajeeda ta dauko Take away tafara bata a baki tanaci kadan kadan tanajin dadin kasancewa tare da family dinta Dan soyayyar da suke nuna mata shiyasa a kullun sai tayi musu addu,ar gamawa da duniya Lafeeya.

Maman Ussee😘

🙎 YAR BAIWAH 🙎1⃣9⃣
Maman Ussee
Chapter 8 · 0% Book details