← Book details Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 38

Sashe 14

Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

★ Da Sallama suka Shiga yayinda wani Daddad'an kamshi mai sanyaya zuciya ya doki Hancinsu da Sanyi mai Dadi ya Ratsa su har Kuryan Daki inda Rukayyah take suka kai Farouq sai Daukan su Photo akeyi gwanin kyau Haka aka yi Barkwanci da Haka dai suka karasa komai suka D'auki Su Sajeeda Domin kaisu gida ya Rage daga FAROUQ sai RUKAYYAH . What a wonderful Day Shurune ya Ratsa Nadan wani Lokaci Yayinda Farouq yayi gyaran murya yamatso kusa Da Rukayyah ya Bude mayafinya tare dacewa . Amincin Allah ya Tabbata gareki yake ma,abuciyar Kyau. Girgiza mata Kai yayi Dan Ganin Hawaye ,, a Fuskarta Hannu ya sanya yashiga goge mata Fuskarta yayinda ya umurceta data tashi ta Dauro Alwala su nunawa Allah Farin Cikin su Da Zuwan Wan nan Ranar mai Albarka.
" Ba musu tashiga toilet tayi Alwala shima yashiga yayi yajasu jam,in Sallah Raka,a Biyu sukayi kamin ya matso kusa da ita ya Dora . Hannunsa akanta yashiga yi mata Addu,ah da kuma Fatan Samun Zuri,a Tagari . kamin ya je ya Dauko Plate da cup ya dauko Leda Wata gasaasar kaza yazuba a plate din ya Dauko fresh milk ya zuba dakyar ya lallab'a ta ta ci kadan bada yawa ba kamin tayi brush Shikuma ya fita anan ne Rukayyah ta samu ta zauna a saman bed duk sai taji wani iri saboda Bata saba ba . farouq kam Dakinsa dake part din Rukayya yanufa yashiga Toilet ya washa Ruwa kamin yafito ya feshe Jikinsa Da Turare Yana katewa ya nufi Room D'in Rukayyah Zaune ya tarar da ita Yace a,a wai Ke Zama ma kikayi ,sunkuyar da kanta tayi kasa ya matso kusa da ita yace kinga kidai kije ki cire wan nan kayan ko na cire miki su da kaina Rasa mezatace masa tayi sai murza yan yatsun ta takeyi matso wa yayi kusa da ita ya ,, Fara Rike mata Hannu wani Shock ne taji yajata Dakyar ya lallabata tayarda tacire kayanta ya Dauko mata wata Sleeping Dress .Purple colour. Had'ararriya ta Hadufa ba karya gaskiya yaja Hannunta suka fara zagayawa sanda yanuna mata komai dakomai hard Room dinsa saida yakaita ita dai Takasa sakewa Bayan yakare nuna mata komai ya dawo da ita zuwa Room Dinta Upp din. Wuta yayi yakara A,c suka kwanta Yajawota ya Rungumeta can cikin Jikinsa Jikinta ne yafara Rawa Dayaga Haka sai ya Rada mata a kunne just be Free ba Abinda zan. Maki duk da Haka Bata Sake ba Haka yashiga wasa da ita son Ransa Sanda yakusa Wuce gona da iri Rukayya ta Fara masa kuka badan yasoba ya barta A haka sukayi Bacci Wanda zankira da An daiyi maganin Ace Ba,ayi ba Dan Ba Wanda yayi Baccin kirki acikinsu Sai guraren Asuba ya barta yatashi Dan zuwa masallaci ita kuma ta Shiga Toilet wanka tafara yi kamin tayi Sallah ta zauna tafara karatun Al-Qur,ani Mai Girma har gari ya waye.

★Tun ficewarsu Farouq Salma takasa Zaune takasa tsaye da kyar ta iya control din kanta ledarma ko Kallon ta batayiba fuu tashige Room Dinta kawayentane sukaci kazar Banda kukah ba abinda Salma keyi ba irin Zugarda Zuciyarta batayi mata ba O my God yanxu Farouq dina na can tare da wata ko wane karatun yake koya mata oho Ashe haka mata sukeji idan An masu Kishiya da gaskene Ashe Ba,a Bacci haka ta wanxu cikin Tunani Matar tasiri Har Garin Allah ya waye yanda taga Rana haka taga dare . Shigowar Farouq ne ya sanyata ta fara Baccin karya kamar gaske tayar da ita yayi yace taje ,, tayi Sallah Lokaci yayi kamin yashafa cikinta yabata kiss ya wuce mtsewww taja Tsaki Aikin Banxa Bayan ka gama Lalacewa da wata shine zakazo kamin Dadin baki( Hattara mata wallahi muji Tsoron Allah yakamata musan irin abinda zamu gayawa mazajenmu saboda mumuke Neman Aljannah a gunsu Allah yasa mudace Ameen.) Haka ta Daure taje tayi Alwala tayi Sallah ta Shiga wanka bayan ta idar da Sallah tafito tashirya cikin wata Atamfah Dinkin mai kyau tana ta wani cika da batsewa kamar wadda Akayi wa laifin Wani Abin.

" Bayan ya dawo daga masallaci part din Rukayyah ya Nufa ya tarar da ita tana ta karatu murmushi ya sakar mata kamin ita kuma ta Gaidasa ya Amsa ,, yace Yauwa Sarkin tsoro murmushi tayi cike da kunya kamin ta gama ta fito tadan gyara wasu abubuwan Dayake ma komai Normal yake sabo ne kawai dayi Sai Farouq kam Room dinsa ya nufa ya koma Bacci Rukayya ko rasa abinyi tayi taje kawai ta kunnah T.v tashiga Kallo Abinta.
" misalin 8:30Am Afra tashigo gidan D'auke da Kayan Breakfast nasu Da murna Rukayya ta tareta tace sai yanxu Afra tace tab koyanxuma sakone,, yakawo ni kinga Ficewata ma zanyi Dan Banaso Yaya ya Yiman surutu yafara cewa INA masa ,,Sakko tun da safe a gidansa ,, Murmushi tayi ta karbi kayan ta jera a dinning table Afra Bata wani jima ba tafice tace Zata dawo zuwa anjima Rukayyah cigaba tayi da kallonta sai gurin 9. farouq ya fito D'auke da Fara,arsa yasha wankan Boyel milk colour ,, yace yadai my Angel ,, tace lfy Lou Kinci Abinci ne ta girgiza masa kai yace A,a Ba tun dazu aka Aiko Da Abincin ba tace eah INA Jirankane yace OK to zo muje muci tare suka ci Abinci saida Farouq ya Tabatar taci ta koshi kamin ya barta Ta gyara gurin ,, ya umurceta data Dauko mayafinta suje part din Salma ,, Ba musu ta yi yanda yace yayinda yake Gaba tana biye dashi Baya har suka is a Part din Zaune suka tarar da ita Da. Sallama suka Shiga Rukayyah ta gaidata Wanda dakyar ta Amsa Farouq ne yanuna mata guri ta Zauna Shuru ne yadan Gifta kamin FAROUQ yafara magana kamar haka :

★ Salma Kinga ga Rukayyah nan Amanace a gurinah kuma a gurin ki Banason Fada,, Kuma Ku zauna lfy da juna Ku mutun ta junanku duk kanku INA sonku shiyasa na zauna tare Daku Rukayyah Ki Baiwa Salma Girman ta karki Rainata kibita Duk abinda takeso indai bamai wahala bane kimata kinsan Junah biyu gareta sai kinyi Hakuri da ita kinji Tace Insha Allah yace Good . Allah yayi maku Albarka yabani Ikon yin Adalci a Tsakaninku Rukayyah tace Amin kamin ya fice ita ma takoma part dinta Dayake Yan Yinin Amarya sun Fara Isowa haka dai Suka kasance Har Rana tayi.

Maman Usseey😘

🙎 'YAR BAIWAH 🙎5⃣9⃣

~Maman~ ~Usseey~😘
Chapter 14 · 0% Book details