← Book details Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 38

Sashe 27

Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaya mustyna,ashe da rabon rai ya k'ara ganin rai tsakaninmu?"

Sai kuma ta soma hawayen farin ciki.

"Yaya mustyna??" Ya maimaita a zuciyarsa,ashe har yanzu Yasmeen bata mance dashi ba?

Har lokacin hannuwansu harde cikin juna,Haris ya kauda kansa ya wucesu zuwa ga mutanen gidan suna gaisawa. Kasancewar gwaggo Hajara ta samu labarin kowanene a wajen Baharu wanda yakai mata tsegumin zuwan Tasleem yasa ta ganar dasu. Nan fa murna ta k'aru,suka shiga tambayarsa mutanen Kano yana amsawa. A karshe yayi musu sallama bayan ya dire musu rafar kudi 'yan dari dari guda biyu ya mike suna fadin ya barshi amma da azama ya nufi waje. Ganin haka tasleem tabar hirar bayan rabuwa da Musty tabi bayansa a da sauri. Ganin yana shirin wuce zaurensu ne yasa tayi azamar riko hannunsa wannan yasa shi juyowa ya watsa mata kallon da yayi kama dana farkon ganinta dashi. Ta saki hannun dayake kanta a waye yake ta nuna kamar bata gane yanayin fuskarsa ba ta hanyar marairaicewa da langabar da kanta

"Yanzu tafiya zakayi shine babu ko sallama?"

Ya dan tabe baki yana mai zura hannunsa cikin aljihun wandon jeans dinsa,ya daga kafada

"Gani nayi kina hira da yan uwanki banson katseki ne."

Murmushi tayi kawai,ta soma fahimtar wani abu kadan akan fuskar Haris, mai yiwuwa yana dauke da ciwon da itama take dauke dashi. Ya katse tunaninta

"Zan wuce."

Ga mamakinsa yaga ta durkusa har k'asa tana dubanshi
"Har na rasa manyan kalmomin da zanyi amfani dasu kuma wajen yin godiya agareka yayana,kayi jihadi babba wajen ceto rayuwata daga halaka. Daga yau na baka matsayi babba gareni. Zuwa yanzu bani da wanda yafimin.."

Ya katseta shima ta hanyar yin durkuson a gabanta,yana kafeta da wannan idanuwan nasa masu kara fama mata ciwon dake ranta. Saidai ita kanta tana raina kanta a gaban Haris,duk wani haduwarta ganinta takeyi tsumma a gabansa. Ita kanta ta riga tasan Babban Goro sai magogin karfe,me namiji irinsa zaiyi da 'YAR BARIKI? Ta kauda kanta daga dubansa ganin bashi da niyyar kauda nasa akanta. Wai daman akwai abunda take ko kuma zata tabajin kunya acikin mutane? Bata taba kawowa ba kuwa ko a kanta,ya katseta a karo na biyu ta hanyar mikewa

"Tashi Tasleem."

Ta mike tsaye,bai kara dubanta ba yace "Kina iya rubutamin lambar wayarki,watakil na leko gobe kafin na wuce."

Har ya soma tafiya sai kuma ya juyo dauke da murmushi saman fuskarsa wanda bata taba ganin irinsa ba a tattarr dashi. "Sannan ki sani,matsayin kanwata kike Tasleem. Bana bukatar ki yawaita godiya gareni. Ki cigaba da godewa Ubangijinki. Hakanan ya dace kiyi istibra'i. Sai Allah Ya kaddara saduwarmu Tasleem."
Ya soma tafiya da baya da baya, hawaye taji sun taho mata yayinda ya juya ya fita da sauri saurinsa. Ta tsaya cak tana binshi da kallo zuwa lokacin hawaye sun sauka saman fuskarta. A gaban idanunta yaja motarsa bai k'ara ko kallon kofar gidan nasu ba.

"Small."

Taji muryar Yaya Musty ya fadi ta bayanta,wannan ya fargar da ita a inda take tsaye.

'YAR BARIKI

©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)

(45)

Ta dubeshi tana murmushi,yayinda damuwa ta sauka saman fuskarsa shi kuma.

"Kin tsaya anan? Ko bakiso ya tafi bane?"

Abunka da wacce bata iya boye damuwarta ba tace

"Banso ba,ya tafi ya barni da damuwa marar misaltuwa saidai yace watakil kafin ya wuce ya biyomin muyi sallama."

Musty ya k'ura mata ido yana kallon kwayar idanunta. Akwai wani kwantaccen sirri game da Haris a cikinsu.

"Kanwata are you in love?"

Tayi tsai domin batayi mamakin jin wannan tambayar ba,inda takeson Yaya mustin nata kenan,nan da nan ya dago damuwarta ko wace iri ce. Ta basar ta hanyar dariya ta soma tafiya tana fadin

"Yaya mustyna kenan,ina Haris ina mace irina?"

Ya riko hannunta wanda yayi silar tsayuwarta,ya jawota baya kadan yana dubanta da idanunsa da suka bayyana bacin rai da damuwa karara a cikinsu,mamaki ya hana baby magana sai ya rigata da cewa

"Ya kike irin wannan maganar sisna,wa zaik'i mace kamarki? Ko kina da wani aibu ne?"

Ya karashe bayan ya saketa yana murmushi a sanyaye,bata yardarwa kanta hakan yayi niyyar fada ba sakamakon zafin da ya nuna a farko. Batace komai ba banda murmushi da "Uhm" daga haka tayi ciki.

Ya bita da kallo rai a bace,wai daman Tasleem ba sonshi takeyi ba kamar yanda ya jima yana yaudarar kansa? Yaya mustyna! Yaya mustyna! Me hakan ke nufi?!! Tsaki yaja bazai kuma iya komawa cikin gidan ba kawai sai yayi gaba zuwa gidansa rai babu dadi domin ya gama lura Haris ya samu gurbi a zuciyarta.

*****
Mutanen gidan sunyi farin cikin ganinsa sosai. Nan aka shiga hidima dashi,sai abinci ake ajiyewa agabansa. Hankalin Haris ko kusa baya kan yan matan da suka had'e cikin kwalliya sunata shawagi a falon wajen kawo mishi abinci,ya tabbata an riga an basu labarin abunda ya kawoshi. Sai hirarsu sukeyi da kakarsa,Hajja. Koda ya kammala mikewa yayi ya nufi sashen kishiyoyinta suka gaisa kafin ya nufi bangaren kakansa,Malam Hussein.

Nan ma suna hira yake sanar dashi tare sukazo da Tasleem diyar gwaggo maryama 'yar amininsa Liman. Ai sai Malam Hussein ya tashi zaune fuskarsa a sake sosai. "Jikar Abdulmalik ce? Ikon Allah,daman kunsan juna ne acan Kano?"

Haris ya rasa amsar da zai bashi a karshe yace "Eh munsan juna,tare mukayi makaranta saidai banma san 'yar gwaggo maryama bace saida muka hadu itama zata zo nan take bani labari." Kakan nasa yayi dariya,cike da mamaki yace

"Wai kuwa d'an tsoho wane irin aminta ke tsakaninka da Liman? Na lura kuna kaunar junanku fiye da tsammani."

Jin tambayar ya k'ara sanya Malam dariyar farin ciki

"Bazaka gane ba Harisu,kaunar da muke yiwa junanmu ta samo asali tun daga iyayenmu da suka rasu,saboda karfin zumuncin ne,yasa mahaifina sanyamin sunan mahaifin liman din,wato Hussein yayinda shima yaci sunan nawa mahaifin Abdulmalik. Bayan haka,Allah Ya riga ya sanya mana kaunar junanmu fin tsammani Harisu. Wanda muke burin wataran mu kulla zumuncin da zai d'orar. Saidai kasan a zamanin nan ba'a yiwa yara dole,amma har gobe bamu bar burin wasu cikin jikokinmu ba su share mana wannan hawayen."

Haris yayi murmushi,baffa ya katse tunaninsa

"Ina fatan kayi abunda akace ya kawoka?"

Haris ya hade fuska

"Na rasa wacce zan zab'a domin na lura jikokin naka akwai yanga. Duk kama sukeyimin da juna ma."

Sukayi dariya,Baffa yace

"Ja'iri,ko kanawan dabo ba zasu nunawa mutanen Kazaure kyawawan yan mata ba shiyasa har zuwa yau ka kasa zab'en matar aure. Kada ka damu ka nutsu ka zab'a bazan bari Aliyu yayi maka dole ba."

Daga haka suka tab'a hirarsu ta zumunci kafin Haris yayi mishi sallama ya fice zuwa d'akinsa. Hankalinsa yakai ga wayoyinsa wanda ya barsu suna chaji,ya dauko yana dubawa. Missedcalls har fin goma,shida kuwa na kanwarsa ne. Yayinda daya na Abba sai kuma daddy daya kira sau uku. Hankalinsa yafi raja'a ga na kanwarsa. Yana shirin kira ya hangi sak'onta. Tun soma karantawarsa ransa yayi mummunan b'aci,jikinsa har rawa yakeyi. Wai Kb wane irin d'an akuya ne? Meyasa baya shakkar b'ata ran mutane? Ya lalubi layin Yasmeen ta daga tana kuka alokacin tana kwance a gadon mami(Maman kb wacce ta gama fusata).

Cikin kuka tace "Yayana kaga text dina? Yayana ka ceci rayuwata bazan iya yinta ba saida Kabir. Na shiga uku."

Ya runtse ido yanajin bakin ciki har ransa

"Wacece yarinyar?" Shine kawai abunda ya nemi sani.

"Baby yake yawan ambato."

Tuni idanun Haris suka bud'e,Baby?!! Akanta Kb yake cin zarafin kanwarsa? Kawai sai ya kashe wayar a fili ya furta

"Na rantse da Allah Kabir bazaka tab'a aurar Tasleem ba. Daga kai har ita zan nuna maku ni Haris na isa."

A fusace yasa kai,bai zarce ko'ina sai d'akin BAFFA......!

'YAR BARIKI

©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)

(46)

"Ya wajen yayan naki? Ai farko mun damu da rashin samunki a waya. Wancan zuwan da sukayi na karshe yace min kin koma makaranta da zama anan Kano kuma ya hanaki yawan amfani da waya a dalilinsa nason ganin kin mayarda hankali ga karatu, har ina fad'a ina cewa me zaisa a wannan zamanin baligar mace tabar gaban mahaifanta ta koma jami'a da zama. Haba Tasleem,shi Khalid(Abba waziri,mahaifinta) din baiga kuskuren yin hakan ma? Koda dai na yarda da tarbiyyar da kika samu wajen maryamu amma hankalina bai kwanta ba Tasleem,nafison ganinki a d'akin mijinki."

Baby dake sauraron dogon bayanin kakarta,a gefe idanunta yana kan wannan 'yar budurwar mai matukar kama da ita tunaninta kuwa ya raja'a akan zuk'i tamallen da Yaya Abdullah ya shararo ya gaya musu. Kenan cewa yayi tana makaranta? Ikon Allah kenan. Ta numfasa ta kauda maganar

"A ko'ina Allah kan tsare bayinSa inna,kubar damuwa. Wai wacece wannan duplicate din tawa?"

Inna ta dubi yarinyar duk da bata gane turancin ba saidai ta fahimci baby bata ganeta ba.

"Lallai ma 'yar nan,keda har aike kikayi na sutura a kawowa kanwar taki tana jaririya? Aisha humaira ce fa,taci sunan aminiyar uwar taki. Lallai baki kyauta ba tasleem."

Tasleem idonta ya cika da kwalla,inna ta katseta da cewa

"Ai kusan sa'annine da takwararki,ko wannan zuwan nasu na karshe karkiso kiga har tasleem karama ta kusa kamota a tsayi."

"Wacece mai sunana?"

Anan kuma inna ta tsaya cak tana dubanta,wannan karon mamakinta da shakku sunfi na koyaushe domin kuwa tun zuwan Tasleem take lura da yanda ta chanja duk da tasan yanga da nuna aji halinta ne saidai zuwa yanzu ta soma zargin kodai Tasleem bata wani zumunci da yayan nata.

"Kinga abunda yasa banason makarantar kwana ko? Kada dai kicemin bayan mu da kika daina zumunci damu,yayan naki ma bakya zuwar mishi hutu kamar yanda ya fadamana ne? Nayi mamakin jin cewar kin manta da d'iyarsa."

Sai lokacin Baby ta farga da kuskurenta,ta wayance ta hanyar dariya duk da har lokacin tana fushi da yayan nata hakan baisa ta karyatashi ba.

"Kai inna,karatu fa yayi zafi duka duka munkai wata bamu hadu ba,inada matsalar yawan mantuwa ni ki gayawa liman ma ya nemar mini maganinsa."

Inna tace "Assha,naga alamun hakan kuwa. Tabbas dole ki nemi magani da kuruciyarki da komai wannan cuta ce babba. Saiki bar yin fitsari a inda kike wanka,domin shima yakan jawo larurar yawan mantuwa. Zan kuwa gayamishi."

Tasleem ta janyo hannun humaira wacce ta kammala cin tuwon dare,ta rungumeta kafin ta sumbaci goshinta.
Chapter 27 · 0% Book details