← Book details Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 38

Sashe 4

Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kashe gari haka ta kasance tun wuri suka kimtsa suka fito inka gansu kanar wasu twins gwanin sha,awa yau ma Daddy ne yakaisu skull daga nan ya wuce GT Bank da acan yake aiki bayan an kare Assembly kai tsaye kowace daliba ajinsu ta nufa Dan daukar darasi Sajeeda da Ruky a tare suke tafiya har class dinsu kowace ta zauna a set din ta kamin class master yaxo yakira register daga nan kuma
Malami mai lesson ya shigo ya fara gabatar musu da lesson.

Maman Ussee😘

Naga sakonku nagode sosai da kulawa nasoyana Allah yabar zumunci.

🙎 YA RBiAWAH 🙎 1⃣0⃣
Maman Ussee

Time din break yayi Sajeeda da Ruky suka fito waje class sunayin break yayinda sauran student ke lamarin gabansa, Ruky nikuwa Sajeeda kinsan abinda yake bani mamaki a,a saikin fada wan nan malamin nan na daxu mai disga mutane din nan kinga yanda yabar ummy nata zuba surutu ya kyaleta amma na tabbatar da wani member din class ne daya sha zagi yau kuma na ga sai wani shige mata yake kodan yaga tafi kowa girmane a class din, hey are u jealous 😀 Ruky takai mata duka wane irin jealous kuma ni ina ruwana dashi kawai dai naga hakan baidaceba ne shiyasa na gaya miki OK to kawo takalminki na ajiye miki kije ki gaya musu ustaziya Rukayyatu 'YAR baiwa 😏 dalla Banason rainin hankali daga kawai na fada miki Abu shikenan sai ki wani canja min magana 😀😀😀 dariya sajeeda tayi hardasu kyalkyatawa kamar zata fado kasa aiko Ruky ta ji haushi ta kwashi kayanta fuu ta fice daga wurin hava ke kuwa sorry mana tsayani muje tare INA ko saurarenta bataiba ta fice class abinta sai daga baya ta saiko suka shirya kamin adawo break.

Sannu sannu.bata hana zuwa sai dai a Dade ba,a kai ba yau su Ruky zasu zana end of second term examination, a cikin skull kuwa bawanda baisan Sajeeda Abubakar &Rukayya Sa,eed ba komai nasu atare sukeyi duk Inda kagansu tarene ba abinda yake rabasu ko a gida ma hakan ne gasu da ilmi uwa uba kyau gasudai ba wani girmane dasu ba Dan daka gansu zaka yarinta karara a tare dasu sai dai sunada ladabi ga girmama na gaba dasu a class inkaji suna surutu to lallai Abu mai mahimmanci suke tattaunawa. Baruwansu da wasu frnds sudai barsu da karatu Dan kullun abinda Daddynsu yake jaddada musu kenan kosunyi fada to yanxun nan zakaga sun shirya al,amarinsu yana mutukar.birge jama,a ko unguwarsu bamai cewa sun tsokaneshi Dan su karatun ne kawai yasha musu kai alhmdllh cikin sa,a suka fara Rubuta exams dinsu har suka karashe akayi holiday,

Murna gurin Rukayya ba,a magana Dan dama ta matsu ayi Hutu Dan taje Raba dama Daddy yace da anyi Hutu zasuje tare suyi one week sai sudawo sabida islamiyarsu dayake sunyi nisa sosai, bayan sun dawo gida da kwana biyar suka daga sai Raba gabaki dayansu harsu Fadil da Abdallah ai kuwa kuxo kuga murna wurin Baaba kamarme taga yan jikokinta musamman ma Yar baiwa taga yanda tayi Haske ta goge hardasu kiba gwanin sha,awa kai lale marhabin da yan sokoto cewar Malan sa,idu nan nan kawai yake da 'ya'yan nasa yanajin wani farin ciki a ransa yarsa CE ta dawo haka tubarkallah masha Allah, bayan an nutsa kowa yaci ya koshi aka fara sabuwar fira yayinda suka gode sosai da namijin kokarin da Daddy yayi musu godiya suka ka rayi da fatan alkhairi, satinsu daya a Raba suka juyo yar baiwa kawai suka bari koshima badan sunsoba saidan rokon da Baaba tayine shi,isa suka barota ta kara sati sai Daddy yazo ya dauketa sukoma, bayan kwana biyu Baaba na zaune itada Rukayya suna tadi take tambayarta bawata matsala daiko eah bakomai lfy lau wllhi bakiga yanda ake bani kulawa ba sosai da sosai to madalla ai hakan akeso Allah dai yasaka musu da alkhairi Rukayya ta amsa da ameen amin shiyasa nake sonki Baabata dankin iya addu,a 😀 dariya Baaba tayi tace ja,ira har yanxu dai sakarcin naki nanan Ruky tace to in ban maki ba wanikeda shi Wanda yafiki ai kekadaice dagake. Bakari 🙊 tabdi wai yar baiwah yaushene kika iya surutu haka lallai zaman birni ya saka ki iya magana 😳ai baaba Dan baki zauna da Sajeeda bane haka take kamar parrot indai surutune uhum menene fara kuma me Ruky zatayi in banda dariya aikuwa Baaba takaimata duka ta goce tsaya kiji parrot akecewa inaga sai naje sake skull dinmu kin kara wayewa ja,ira kekam dai Allah ya shiryeki ta CE ameen tana murmushi.
Maman Ussee😘

🙎YAR BAIWAH 🙎1⃣1⃣
Maman Ussee😘

Satin Rukayya biyu daddy yazo yadauketa suka koma sokoto cike da kewar iyayenta musamman ma Baaba dasuka shaku sosai,
Haka Rayuwa taci gaba da kasancewa yau farin ciki gobe akasin haka dama ita rayuwa haka ta gada , amma a wurin Rukayya abin ba,a cewa komai Dan kullun cikin farin ciki take yayinda duk tayi sallah saita Roki Allah yasa kama daddy da aljannah hakama mummy dakuma iyayenta. Haka suka karaci holiday dinsu har ya kare duk Wanda yasan Rukayya ada idan yaganta a yanxu bazai ganetaba inhar ba farin sani yayi mata ba Hutu kwanciyar hankali haiba kwarjini duk sun baibayeta batada wala matsala a skull ma hakan ne Dan so dayawa tasha samun kyaututuka da dama awajen malamai kai harma da students akan baiwar da Allah yayi mata ilmi. Ba,a magana Dan ko quiz za,ayi to Ruky da sajeeda na ciki haka ma divert ko inter schools compotions za,ayi to dolene asaka yar baiwa ga tada da speach mai dadinji dakuma saurare takowane fanni gata ilmin addini Dan kuwa saura kadan ta Haddace alkur,ani mai girma, Sajeeda namatukar son Rukayya kamar yan uwanta na jini haka take jin ta kamar uwa daya uba daya suke ba,abinda Rukayya zata CE tanaso Sajeeda. Batace tana sonsa ba koda kuwa. Baimata ba a duniya inhar kanason kaga. Baccin ran Sajeeda toka taba Yar baiwa haka ma ko a wurin Rukayya batason ko kadan taga yar uwarta cikin damuwa kuma sajeeda bata taba jin haushi ko kyashin Rukayya tafita ilmi ba duk da dai itama tanada nata iya gwargwardo wadan da basu sansuba cewa ma suke yanbiyu ne kasan cewar tun bayan dawowar, Ruky a gidansu Sajeeda Daddy bai taba ban-ban ta musu kayaba kai harta takalmi da sarka iri daya ake saya musu hakan yayiwa mummy dadi sosai yanda Daddy yadauki Ruky kamar sajeeda baya taba nuna wani banbanci duk abinda zai iya yiwa sajeeda to tabbas zai yiwa Rukayyama, duk da yasha samun yan korafe korafe a gurin Abokanansa dakuma wasu amma indai ya fahimci ba maganar arzikice takawo kaba, tun daga ranar kun raba hanya dashi bayason sa 👀 ido Dan yasan duk abinda yayiwa Rukayya Dan Allah yayi kuma yanada tabbacin zaisamu ladansa a gurin Allah .
Haka abin yake ko a wurin mummy indai kawayenta suka fara kushe Rukayya nan da nan zata watse mutun komai dangartakar ta dashi kuwa ita a ganinta ko ba ita, ta haifi yar baiwa ba ai Abbanta ciki daya suka fito dashi kuma duk abinda zai cutar da Rukayya bata sonsa Dan tasan duk abinda tayi Dan zumuncine kuma Dan Allah da fatan samun lada a gun Allah. ( Anya a wan nan zamanin zaka iya samun Dan uwanka maisonka da kaunarka saboda Allah kuwa zumuncin yanxu sai a hankali kowa nasa kawai yasani Ya Allah kabamu ikon so da kuma kauna ga yan uwanmu, Ameen ya Ra bbi).
Rukayyace zaune a falo tana koyawa su Abdallah home work dinsu Sajeeda kuma na gefe tana Dan duba wani English litreture mummy kuma ta fita da yake yau ba Islamiya kowa na abinda yasa a gaba sallamar Daddyce ta sa kowannensu dago kansa sama Dan amsa sallama Sannu da dawowa Daddy, yauwa yaran Daddy sannunku da gida umman taku har yanxu bata dawo. Bane wan nan zuwa biki haka har yamma tayi gashi inaso muje gidan wani amininah da muka Dade bamu haduba baya kasar jiya yadawo muje muyimai. Barka da dawowa ko bakwaso 😊 sukayi ga aki dayansu Daddy muje basai munjira mummy. Ba kawai cewar Sajeeda yes Daddy kinji Abdallah , no gsky daddy ajira sai mummy tazo inyaso sai mubarshi sai anjima da dare muje Daz my gal shiyasa nake sonki dan kinada hankali ba kamar wadan nan ba Sajeeda ta turo. Baki fadil kuma gwalo yayi mata ta kaimasa doka ya goce ya boye bayan Sister Ruky plzz my sist kice karta dake ni to meye namin gwalo ai nima watarana Daddy zai yabeni bakaman kai ba ko little bro cewa da Abdallah eah hakane Sist kyalesu shida sister Ruky, muma watarana rana sai mun musu gwalo dat my bro oya give me five suka tafa ita dai Ruky murmushi kawai tayi itama tace da fadil leave them kaji sweet.bro dina itama sajeeda ta kwai kwayeta kaji sweet bro dina Ruky ta jefa mata pillown kujera ta gudu ita da Abdallah zuwa daki hmmmm Sajeeda da Ruky kenan everlasting friend

Maman Ussee😘

I love you All my fans 💋

🙎 YAR BAIWAH 🙎1⃣2⃣
Maman Ussee😘
Chapter 4 · 0% Book details