← Book details Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 38

Sashe 16

Yar Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

" Haka Rayuwarsu Takasance a Tsawon Satin nan Har Ranarda Ya Raba masu Girki Ya Kara tarasu Ya Musu Nasiha mai Ratsa jiki Wanda Rukayyah kawai ta Dauka Salma kam Biris tayi Dan Ita yanxu Kwata2 ta canja daga Sanin da Farouq yamata Salma ce Zata Fara yin Girki Wanda Farouq ya CE Duk mai yin Girki to A part Dinta Za,aci Abinci Hakan bakaramin Haushi yayiwa Salma ba Amma ba yanda ta iya Dole ta Hakura Dan tasan Halin FAROUQ Baya canja,, maganar sa " Shikuma yayi Hakan ne Dan A kara Samun Had'in kai A tsakanin su ,,
" Da Dare Salma ta Rangada Girki Mai Rai da motsi yayinda ta Ci uban make ,,upp kamar ba itaba ajima Anjima ,,ta Duba agogo haka Ta tsara komai sai wani Kisisina takeyi Farouq baidawo ba sai misalin 9 Bangaren Salma ya nufa Da murna ta Taresa Shikuma sai wani Biye mata yakeyi Dan Farouq Mutun ne maison a tarairayesa nan da nan ta Gama dashi Room dinsa suka Nufa ya Rage kayan Jikinsa . Ganin Abin na Salma bamai karewa bane yasa ya dakatar da ita yace Dear sorry kinsan yanxu Bamu kadai bane Jeki ki kira kanwarki muci Abinci Kinga tana Jiranmu badan Taso ba ta Tashi yayinda Shikuma yadawo sitting Room yana jiran Isowar su.
★ Rukayyah na Zaune A Dakinta Bayan ta karasa Sallah Isha Dan yau tayi Wanka karatun Al-Qur,ani mai Girma takeyi Da murya mai Dadi a gurin mai Saurare Salma tashiga Noking din Door Rukayyah bataji ba Dan Dayake karatun ya D'auke mata Hankali Abin ya matukar Tunxura Salma tace Lallaima wan nan Yarinyar dani take Zance murda kofar tayi tajita a Bude Sa kai ,, kawai tayi Mutuwar tsaye tayi Dan Yau itace Rana ta Farko data taba shigowa part din Rukayyah tun Kawota A cikin Zuciyarta tace Tab Wan nan Dukiya da aka zuba mata a gidan nan kamar wata yar Hamshakin mai Kudi A Hankali ta fara Notice din komai Har kitchen sanda tashiga bata Tsinkeba saida Tashiga Room din da take jiyo Saurin Kira,a natashi bako Sallama ta Bude tashiga Zare Ido Tayi dataga Wani Hadararen Royal Bed ,, Da kyar ta Hadiye Yawo Tare da gyaran Murya Rukayya bata Dago ba saida takai Aya ta dago da Murmushi a Fuskarta Lah Aunty Salma kece yau Shigo Zauna mana Yake Salma tayi tace No bazama Zanyi Abinci zaki fito muje muci Rukayyah tace OK ganinan zuwa Barin Room din Salma tayi Tana ta Magana a cikin Ranta lallai wan nan saina Tashi Tsaye yarinya kamar yar Tsana Hmmm Tabdi ,, tayi wucewarta zuwa nata part din Nidai Binta nayi Da Ido INA Kallon Ikon Allah 😀.
" Rukayyah Kara Feshe Jikinta tayi da Turare Aoud mai Dan Karen Kanshi kamin ta Dauki mayafinta ta Rufe Jikinta tana tafiyarta Hankali kwance Harta Isa Part Din Salma da Sallama tashiga ,, Part din Fuskarta D'auke da Murmushi Farouq ya Amsa shima murmushin yakeyi Gaidasa tayi tamin ta samu guri tazauna Batare da Bata lokaci Farouq yace muje muci Abincin ko Salma sai Hararan Rukayyah take Ganin irin Kallon da Farouq yake mata A Ranta tace Jarababa yaudai kya kwana ke kadai mayyah kawai( Jama,ah kujimin Salma Da Wani zance oh oh mata Da kishi ) Rukayyah batamasan tanayiba Samun Kujera tayi yazauna Abinta yayinda Salma ta fara zubawa kowa Abinci Tanayi tana Jan Hankalin FAROUQ Wanda Gabaki Daya ya Mutu a gurin Kallon Rukayyah Dakyar yasamu yayi control din Kansa ya kula Salma Bayan sun Kammala cin Abinci suka Dan Taba Hira Sama2 Rukayyah tayi musu Sallama Zata wuce Farouq yace Angel kona Rakaki ne Tace no Kayi zaman ka Badamuwa Salma tace wane irin karakata Halan dazata zo wanine ya Rako ta , no kinsan Yanxu Dare yakara yi kar taji Tsoro Turo baki Salma tayi Yace lallai nida naje kiranta Dazu wani ne ya Rakani Ganin Zata miyarda Zancen wani Abu yasa ya Dauko wata Caftar aka Basar da Zancen.

★ Sosai Salma tayi mamakin Ganin Irin yanda Farouq yaketa Rawar jiki Daya ,, kusanceta Kwata2 Batama yi Tunanin Samun irin Haka daga Garesa ba Baccima Kalilan yayisa Wanda Hakan ba karamin Dadi yayiwa Salma ba a Ranta tace wayasani koya Canye abinsa kamin a shigo karyar Banxa Anxo ana mana wani fankama ashema nafita sai Rawar jiki yakeyi akaina ina Amaryar Haka tata kitsawa Har Bacci ya kwasheta . Rukayyah Baiwar Allah Tun da tadawo part dinta tarasa Abinda kemata Dadi Saboda a kwanan nan tasaba sosai da FAROUQ yaugashi Zata kwanta ita Daya wata Zuciyar kecemata yanxu yana can Yana yiwa matarsa irin yanda yake maki wani Abune taji yataso mata Ganin Tunanin ta zaiyi yawa shaidan zaiyi tasiri akanta yasa Tace "A,uzubillahi minal shaidanirrajim" Ta Basar da Zancen kwanta wa tayi a beda dinta sai juye juye takeyi Ganin Rakasa Bacci yasanya ta Dauro Alwalah tashiga yin Nafillah Sallar dare Dan Neman Samun Zaman lafeeya da Kwanciyar Hankali Yauwa maccen Kwarai Diyar Albarka Saliha acikin mata nagaidaki Macce Tagari.

Maman Usseey😘

🙎 'YAR BAIWAH 🙎6⃣1⃣

*Maman* *Usseey*😘

★Washe Tun da Asuba Farouq yatashi Yata yar da Salma Kamin ya Fito ya Nufi Part Din Rukayyah Dayake yanada keys na kowane part . Bude Kofa yayi Yashiga a Hankali yake jiyo Sautin Muryan ta Tanata Karatun Cikin Murya mai Dadin Saurare Murmushi Yayi Yace Alhamdullah a Fili Wani Dadi ne ya Ziyarci Zuciyarsa ,, Saboda Tun Aurensa Da Salma baita ba Ganin ta Dauko Qur-ani ta Karanta Ba duk da Yana iya Bakin k'okarinsa Wurin Ganin tasamu Ilmi saidai Yau Yakasance Abu mafi Girma a Rayuwar sa Ana Karatun Qur-ani A gidansa Bayan shi Sabanin Wakokin da yasabaji A gurin Salma wata Soyayyar Rukayyah CE takara Shiga Zuciyarsa ,, Sosai da Sosai Da Sallama yashiga Room Dinta Zaune yaganta a Saman Sallaya Sanda takai Aya kamin ta Dago ta Amsa Sallamarsa Da Murmushi ta Gaidasa ,,Barka da Asuba ya Amsa Da Yauwa Hope kin tashi Lafeeya ,, Qlau Alhamdullah , yauwa Nixanje Massalaci dama Dan Natashe kine na manta Matar Tawa Malamace Abin Dariya yabata Tace wane Ni Daliba Dai yace koma Dai menene Allah ya karba ta Amsa Da Ameen Kamin ya Fito Dan Zuwa Massalaci ya sallaci Asuba.
★ A bakin Kofa sukaci karo da Salma wadda tayi labe tana Saurarensu Turo baki tayi Farouq yace Salma Ba Sallah nace Kije kiyi ba To ai gani nayi Ba ita keda Girki ba Amma kawani Zo Part Dinta Nifa Banaso A Shiga Hakkina ,, Hava Salma wan nan Wace irin Maganace Dukkan Ku Magana ne kuma ko wacce tanada Hakki akaina Dan Nazo naga Ya tashi Kuma Natayar Da Ita tayi Sallah shine Shiga Hakki Eah Shiga Hakkine mana Aida Kace Ni naje Na tasheta bakaiba Mtseww yaja Tsaki to Badani a Wan nan Tsarin. Ba Kuma dole kibi yanda Na tsara Gidana yayi ficewarsa yabarta saida ta Harari Kofar Part din Rukayyah kamin ta wuce nikuma nace A Banxa Harara A Duhu Dan Wadda kikayi Domin ita bata ma San Kinayi ba .

" Rukayyah bayan ta Kare Sallah Asuba Wanka tashiga tayi ta zauna ta tsara kwalliya kamin tadawo parlour ta Zauna ta kunnah T.v tanata Kallo Abinta wayarta CE tayi Kara ta Duba Sunan My Sist tagani Murmushi tayi tace Sajeeda early in d morning ko lafeeya Daukar wayar tayi Daga Dayan Bangaren Sajeeda tace Amarya Bakya laifi Ya Amarci Rukayya ta Amsa lafeeya Lou gashinan munayi good Dama Yau zan Fara Zuwa Skull Na shirya ne saina tunoki nace Bara nakira naji ki Rukayyah tace Ayya Sist Allah yabada zaman Lafeeya yasa A dace kinga Kallo ma nakeyi Amma Dai zaki biyo tanan ko Sajeeda tace Ban maki Alkawari ba But saidai nagani sun Dan Taba Hira daga Bisani suka Ajiye . wayar
Chapter 16 · 0% Book details