← Book details Yadin Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 15

Sashe 9

Yadin Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aishi aure lokaci ne watakila gudun matan yake Ni da zan sami damar auran irin ku ai da naji dadi sai kuce lallai sai me kuɗi,

Hamziyyah tace

"Inbanda son zuciya irin naka ina mu ina kai,

Dariya yayi yace

"Hmmm hakane amma ai ba daganan soyayya take ba son gaskiya kaso mutum dan Allah,

Safira tace

"Hakane wallahi,

Dariya suka sa hamziyyah tace

"Ku ina yar wannan faƙirin kahun nan nawa sun dawo gidan mu an kwace mai gidansa akotu ina honourable Kabir shi ya karɓa to wallahi bana kaunar in buɗe ido ingan ta agidan nan namu shiyasa duk wani kƴara da da hantara duk na zuba mata ke wallahi ina shirin bawa inna kuɗi tace dole sai tayi auri wani almajiri kinsan fa akan kuɗi ba abin da inna ba zatayi ba ,

Surayyah tace

"Ai wallahi gwara da zaki haka wallahi kyau besan ida zashi ba ke nice da kyanta ae sai na gara samari,

Hamziyyah tace

"Wa ai shiyasa nake so tayi maza ta auri talaka dan kar taji daɗin rayuwa tafini,

Safira tace

"Gaskiya baki dai dai ba iya biyayya wallahi samha na miki bata damu da duniya ba amma ke da baba hajara baku da buri sai ganin ta shiga wahala,

Wani uban ashar hamziyyah ta danno tace

"Ke wallahi zan dena yawo da ke ,

Safira tace

"Ke dena mana sai me daga fadar gaskiya duk kinbi kin takurawa marainiyar Allah abinci sai kunga damar bata ita kanta yanzu inna zenaro bata kulata duk dan tafaranta muku daga nuratu sai anty salama take jin dadi ga mahaifin ta ya tafi gun fasa dutsai be san me ke faruwa ba Allah sarki yana neman arziki kuna gallazawa Yar sa tilo kuda daya kun hanata sakat,

Banza tayi mata shi kuwa ma'aruf kasa kunne yayi yaji abin da suke fadi sosai ya ƙagu su zo kan karofi har kofar gida zai kai su dan yaga wace wannan samha waya ta dauko ganin sun mata banza ta fara danna wa sai da yazo dai dai kan karofi yace

"Wanne lahi zan shiga?,

Nunamai tayi tace

"Nahannun damarka,

Shiga yayi duk kansu suka sauka shima sauka yayi ya dubi hamziyyah yace

"Dan Allah ko zaki temakamin da number wayarki?,

Wani kallo kana da hankali kuwa tayi mai tace

"Nayi maka kama da wacce zaka tsayar ai ko dai dai da manshafawata karya kake ka siya niwallahi wasu mazan suna ban mamaki su dinga dauko

wayan da suka fi karfin su dubeni ga kyau jiki duk madara amma banga laifin ka ma namu nagani da muka tari fakiri me warin hammata tun da nashiga a dai daita sahun ka nake jin wari na tashi ,

Sosai ya ji zafin a bin da tace amma ya danne duk kuwa da irin kamshin da ke tashi a adaidaitar sa saboda ta ƙara muzanta shi ta fadi haka

Surayyah ta matso kusa da ita ta rada mata magana akuɗin ne

Wata shewa ta saki tace

"Yar uwa haka za ayi kin bani good idea,

Safira ta shiga gidan kusa da gidan inna zulai saboda haushin abin da hamziyyah tayi

Hamziyya tace

"Malam Bara in hada ka da daidai da ka sadaki kawe muke buƙata,

Wani farin ciki ne ya mamaye Shi a zuciyar sa yace anzo gurin domin ko ba tace zata hada shi da wata ba zai dawo ya yi sallam da samha yace

"Nagode,

Dariyar mugunta ta saki ta shiga gida samha na zaune ta zuba ta gumi wata tsawa hamziyya ta sakar mata tace.......✍️

*YA ƊIN MGE*

*Oum Yasmeen*

*Part71-80

"Tashi muje,

Samha ta dago kanta tace

"Ina ?,

Ban sani ba ta jata tana turjewa har gaban ma'aruf tace

"Ga dai dai kai tashi ge cikin gida kunyace ta kama samha tace

"Ina huni,

Sosai ya yaba da dabi'un yarinyar yace

"Lafiya qalau nidai sunana ma'aruf jabir inkin amince dani a gaskiya bana so adau tsawon lokaci wallahi kallo daya da nayi miki kika shiga raina Allah i sa nayi miki ,

Ƙasa tayi da kanta kunya duk ta kamata tambas ba makusa a tare da shi ahalin da take ciki a cikin gida gwara ta rufawa kanta asiri tayi aure ko itama samu nutsuwa cikin sanyin murya tace

"Allah ya zaɓa mana abin da yafi alkhairi amma ka tambayi izinin kahu na ta nunamai inda shagon kahu yake,

Burgeshi tayi daman da irin yan matan nan da basu da mu da abin duniya ba yace

"To nagode sosai naga ruwar sunan ki kike min baki fadan ba ni na faɗa miki nawa,

Murmushi ta sakar mai har beautiful dimful ɗin ta ya lotsa tace

"Samha,

Jin gina yayi da adai daita sahun sa yace

"Sunan me dadi samha me kyau kin dace da fassarar sunan ki,

wasa take yi da yan yatsunta tace

"Nagode,

Wayar sa ya fito da ita duk a koɗe yana sane ya gotar da battery gyara wa ya shiga yi yana karantar yanayin ta sosai ta kara bashi mamaki domin ba abin da yake iya gani a fuskar ta na ƙƴamar sa yace

"Samin number ki kinga in Zan zo in sanar da ke ko ?,

Cikin muryar ta me dadin saurare tace

"Bani da waya ,

Be wani mamaki ba saboda ko suhailat autar su daga gani ta girmi samha sai dai samha ta nuna mata girman jiki doba da irin kuma rayuwar da take ciki hakan ma wata damace da zai ƙara gwada ta yace

"To kiyi min addu'a inna fita in samo kuɗin da zan siyi wata in baki tawa duk da sai a hankali wallahi da ƙƴar nake iya jin magana in ankira ni ,

Farin ciki tayi da haka har fusƙarta bata ɓoye ba tace

"To Nagode,

Shiga adaidaitan sa yayi yace

"To samha sai gani na biyu amma yau da daddare zan zo gun kahun ki ,

To tace tashi ga gida tun da samha ta fita take zagaye har dan leƙosu tayi tana ganin ta hamziyyah tace

"Yau she yace zai toro domin wallahi Allah sai kin aure shi in kuma ba haka ba in zuga inna ta kore Ku',

"Kinga ciwon mahaifinki zai dawo baƙin ciki ya kwantar da shi sai dai ki bara Ku ci ,

Murmushi samha tayi tace

"Aunty hamziyyah ko baki faɗi haka ba yayi min arziki nufin Allah ne sau da dama masu kuɗi talakawa ne daga baya Allah ke azurta su wanda Allah be bawa a nan duniya ba sai kai mai fatan samun lahirar sa me kyau

wahala bata ɗorewa ko da kika gansa akwai irin da damuwar sa da take da mun sa ƙar ki ga Mutum cikin daula kiyi fatan damake ce shi yasan wanne hali yake ciki ko wa da irin baiwar sa

alhmdllh zai fi ta nemo halak sannan me kuɗi da talaka duk daya suke agun Allah Wallahi tun da Allah ya bashi iƙon fita ya nemo yafi wani me ƙuɗin da ba'asan sana'ar shi ba kuɗi ba shi ne kwanciyar hankali ba soyayya kulawa ganin girman iyaye infi karfin ci sha suttura ganin darajata da ta iyayena

wallahi shine kwanciyar hankalin aure amma inki ka rasa wannan to wallahi kina ganin kuɗin ƙiriƙiri baki da da kwanciyar hankalin ci wani ma kuwa ba zaki gansu ba sai dai ya kashewa gadangarun bariki me yakai wannan ta kai ci ,

Saroro hamziyyah tayi tana kallon samha yau she yarinyar nan har ta raina ta da zata faɗi magana ta mayar mata tace

"Kee Ni kike fadawa haka ?,

Surayyah tace

"Me kike jira fin ciko shegiya ki naɗa mata duka yar bura'uba,

Ai kuwa nan suka taru suka na ɗa mata duka a haka inna zulai ta dawo ta same su tace

"Ke hamziyya lafiya?,

Daina dukanta tayi tana haki tace

"Inna kinga yarinyar nan mu zata tozarta wani me rufin asiri ne yazo yace yana son ta we baza aure shi ba talaka ne tun da har ta sami me sonta ai saita yar da duba da irin rayuwar da suke ciki kama haya ma ya gagare su duk sun zo suna cinye mana abinci shine ta cemin we itama sai ta sami me kuɗi sannan zatayi aure ai ba akaina take ba,

Janyota inna tayi ta ruƙe mata kunne tace

"Dan uban ki aure kamar anyi angama ne ko be fito ba zan sami musaƙi ko me ramgamin gata irin ki inbashi ke ya aura ai yanzu rayuwar Nan kwarya tabi kwarya ake wazai aure ki danma kin samu ance anason ki shegiya saura kadan ki koma zabiya,

kuka ta saki wannan wacce irin rayuwa ce wallahi ko zata kwana bata ci ba ta gwamma CE ta aure shi duk tsanani ma tana fatan samun canjin rayuwa duk da a yanzu ba zata ce tana son sa ba ko ƙinsa har yanzu usman ne a birnin zuciyar ta

__________________

*GIDAN HONOURABLE Kabir*

Jibson kawe kake ji ana faɗi ga wani uban kida dake tashi kai kaice a gidan gala kake na Lagos ba a gida ba duk wacce zaka ganta da mummunar shiga wacce ta sha bamban da addinin mu da al'adar mu mazan kuwa wani irin banzan askine a kansu ana cikin haka motar

*Alhaji kabir Hashim tamburawa*

tadanno kai sosai yayi mamaki irin wannan kiɗa dake tashi ajiye jarida yayi a gefe yace

"driver sa ya tsaya domin ba zai iya jiran har yayi horn a buɗe ba tsayawa yayi ya fita ya kwankwasa aikuwa aka buɗe beyi wata wata ba ya tura kai sakar baki yayi besan iskancin jabir yakai haka ba yau a gidan sa ga wasu

yan mata da suke rungumaisa yawa zasu shiga jikin sa tambas duk wanda yace tukunyar wani bazata tafasa ba tasa ko ɗimi ba zata yi ba yanzu ya dawo daga gidan ministan harkokin waje Attahiru wanda dansa yake auran mujibbah sai ya sha giyar sa ya bugu sai ya zo ya naɗamata duka yayi yayi ya sake ta yake abin nayi mai ciwo wai shi salim zai zaga a gaban ubansa amma yace
Chapter 9 · 0% Book details