← Book details Yadin Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 15

Sashe 8

Yadin Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jiki na rawa ta bayar hada komai tayi tana haɗawa suka dinga kwasa suna zubawa a mota ko tsinki basu bar mata ba

tana kuka da danasani ta kama hanyar kan karofi tafiya take tana wayai waye har ta isa bugu ta shiga yi sosai inna zulai ta ke shara baccin ta ga wani irin mafarki da take me dadi we gata a makka tana ta ciye ciyen Kayan dadi irin su chocolate ga kuɗi masu yawa tasa hannu zata dauka ta farka tsaki ta shiga yi tana tsinewa wannan wanda ke buga musu gidan ganin abin yayi yawa yasa ta sa hannu ta dauko fitila ta kunna samha ta duba dake bacci cikin natsuwa buga mata tayi bakin ta dauke da salati ta tashi ta dube inna tayi shiru jikin ta na kyarma domin Allah ya dora mata tsoron inna zulai

A zafafe tace

"Ke tashi muje ki buɗa ƙofa daukomin ta ɓaryar can yasin sai na lodawa duk wanda na gani dan iskanci sai yanzu mutum zai shigomana gida ina cikin mafarki me dadi ga soyayyun kaji zubin makka,

Bayar da ta iya haka ta bita amma tsoro ne falranta suna zuwa tsakar gida tace

"Tsaya yar da aka katsan bacci me dadi yau sai kowa ya tashi bin ɗaki ɗaki ta fara tana tado da mutanen gidan cirko cirko sukai a tsakar gida Abba yace

"Inna lafiya tun ɗazu muke tambayar ki kinyi shiru?,

Banza tayi mai tace

"Ke samhatu zo mu buɗe kofar nan inga wake wannan bugun hukuma ,

Gaban Abba ne ya waɗi ya dubi yayansa isah yace

"Yaya isah hukuma fa naji inna na kira,

Shima al'ajabi ne ya kama shi yace

"To inda saboda ai nasaba da halin inna kai ne yau baƙo aciki,

imurana da Ali sai jan tsaki suke anta dasu daga bacci haka hamziyyah ma buɗewar su ke da huya inna ta ɗaga taɓarya ta bugawa haraja wani

ihu hajara ta saki ta shigo cikin gida a guje jiki ruɗo ruɗo da bulala ga malolo a gushi ga yanzu inna tana neman karya mata gadon baya ganin ta fita aguje bata iya sheda fuskar taƙameme wace ba ga farin mayafi tace

"samhatu nashiga uku anya ba gamo nayi ba ko vaki ga kamar mahaukaciya ba ko aljana ce ga farin mayafi Allah isa ba fatalwa na gani ba kuka tasa har da fyece majina Allah ya ɗora mata ƙin mutuwa,

Cikin sanyin murya me fidda daddaɗan amo tace

"Inna zulai baba hajara ce fa ,

Ae kafin ta karasa ta dena kukan tace

"Yau saina ci kundun uban hajara yasin sai ta biyani kuɗina da nake shirin karɓa ta tadani da wannan bugun binta tayi cikin gida kuwa ganin hajara sukai yawa an hullota nan fa aka kawo huta ai ali besan lokacin da yafara dariyaba yace

"Tab yawa anyi ɓarin mota a kanki,

Ƙasa tayi da kai da suka haɗa ido da Abba idon sa yayi ja kamar garwashi ta a shigo da taɓarya a hannuta tace

"Ke hajara kike kowa to wallahi tun muna shedar juna nida ke ki biyani kuɗi na nanfa ta kwashe komai na mafarkinta ta fada musu ta ƙara da cewa

"Kuna ganin zanyarda ne tayi min asara,

Cikin zolaya Ali yace

"Kuma fa da kin ɗiba da tuni sai de ki farka kiji dumus a hannunki Dan shi mafarki yana zama gaskiya wata ran balle mafarkin makkatu ai gaskiya ne,

Turmi ta sama ta zauna tace

"Kai de bari ali wato a Makka na ganni fa ƙasa me tsarki shine wannan alimar ta dawo dani shigiya da fuska yawa funƙaso ,

dariya Ali da imurana sukai har da tafawa nan fa ta lura abin nasu iskanci ne ta ƙara xuba tujara iya son ranta

haushine ya kama kahu Ismail yace

"Haba inna yanzu muna baccin mu kin ta dawo ,

A fusace tayo kansa tace

"To wallahi isma'ilah zanci takazar ubanka kwarankwatsa dubu yau sai kun bani dubu dubu ke kuma dubu biyu zaki ban kai sule,

Cikin ladabi yace

"Na'am inna gani ,

Anya kuwa wannan ba yawan dare take ba a can kwartonta ya naɗa mata duka cikin sauri ta rufe baki tace

"Au na manta sule ba kyau fadar abin da baka gani ba Allah kar ka kamani ina neman tsari da babbakar tsire Allah natuba ka yafe min yanzu sai Allah ya dauki raina iyi sheda ,

Ahankali suka dinga zare jikin su suna tafiya suna kwanciya ba wanda ya kula baba hajara duk kuwa irin murƙususun da take taƙi fadar wanda yayi mata duka shikuwa Abba azuciyat sa yace

Allah shi ƙara tafiya akai aka barta Inna ma ta dena sababi ta koma ta kwanta...✍️

*YA ƊIN MGE*

*Oum Yasmeen*

*Part61-70*

Ganin kowa ya watsai ta tashi jikin ta duk yayi tsami ta shiga ɗakin inna zenaro kofar ta gani a kulle bata buga ba domin tayi hankali in aka kara buga mata tabarya ai ko tashi ba zatayi ba daƙin da malam sule ya nufa nan ta buɗe sai de me shima a kulle ba yarda ta iya haka ta sami gu ta zauna yarda ta ga rana haka ta ga dare

____________________

cikin fitar haiyaci take tuƙi wani wawan burki ta saki lokacin da ta nufo gate ɗin gidan su toni gaban motar ya lotsai bata biya ta kan barnar da tayi ba ta fito a burkice ta fara bugu cikin sauri baba me gadi ya buɗe ai bata tsaya watawata ta zabga mai mari tace

"Baka kula da aikin ka ga abin da kasa nayi dalla can matsamin,

Kumato ya riƙe yarinyar da aka haifa a gaban sa ce yau ta mareshi ya zamar mai dole ya bar gidan domin wata ran duka zata kai mai gudu ta shiga yi tana ganin momcy ta zunduma ihu ta zube a kasa tace

"Momcy na shiga ukku momcy ya cuce ni,

Saroro momcy tayi saukowar miemie kenan daga stairs tace

"Sister lafiya kike irin wannan kukan yawa daddy ne ya mutu?,

wayene suka ƙara zubo mata tace

"Momcy ba kanin jj bani,

Dafe kirji momcy tayi ta zaro ido duk ta gama fadawa kawayen ta tace

"Ke dan Allah,

Sabeerin kuka ta saki ta basu labari har da cewa wata ce ta ƙirani tace ta gansa a gidan su nuratu yar gidan isah

Tsaki miemie tayi ta zauna tace

"Au sai me dan kin gane ba kanin jj bane ba kina son SA ba?,

Wani banzan kallo tayi mata tace

"Daman ba tunyau na gane kina adawane dani saboda kin ga maza da yawa suna sona,

Tashi miemie tayi tace

"Wanne so bacin KO wanne shege yazo ki buɗe mai ya shiga inkuwa wannan shine so bana fatan wannan son,

Tashi tayi tace

"Ni zaki fadawa bakar magana miemie?,

Momcy ta dafa tace

"Kwantar da hankalin ki hice ko baki basa kanki ba ,

Cikin sauri tace

"Eh,

gyaɗa kai momcy tayi tace

"To kwantar da hankalin ki zan samo miki me kuɗi wanda zamu jidadi,

Tsalle tayi ta rungume ta tace

"I love You momcy wallahi shi yasa nake sonki,

_________________________

Iya kwanan huya ma'ruf yayi domin sai dare yayi aka kawo huta kasa bacci yayi tuni tausayin talakawa ya ƙara shiga ransa sai bayan sallar asuba sannan ya ɗan kwanta shima be dadi ba ya tashi fitowa yayi waje ya zauna

yana latsa matatciyar wayar sa ni'ima ce ta fito sanye da riga da skirt na atamfa da misi tsin mayafi ta yafa a kafaɗa tana ɗanna wayar ta murmushi ya sakar mata yace

"Adawo lafiya,

Chak ta tsaya ta juyo tace

"Kai malam kai rayuwar ka inyi tawa zaran ba kallar yadin bane nayi maka kama da irin local yan matan nan tun jiya ya na ga take taken ka to wallahi shiga nutsuwar ka ,

Sagir ne ya wanke ta da mari yace

"Ni'ima ashe rashin kunyar ki har ta kai haka yanzu babban mutum irin wannan zaki wa haka to ai arziki na Allah ne wallahi ina jiye miki ranar da zaki aman YA ƊIN MAGE domin shi inka cishi sai kai amansa,

Ruƙe kunci tayi ta shiga gida tana kuka ma'aruf yace

"Me isa ka dake ta gaskiya banji dadi ba bakyau dukan mace kar ka ƙara Ni ne me laifi da nayi mata magana saboda kirkin mahaifin ka ina ganin ko zamu dai daita da ita to itama ta shiga sahun wayan can ,

Sagir yace

"Insha Allah bazan ƙara ba wallahi bata min rai tayi,

Ai kafin ya ƙarasa mama ta wanke shi da mari tace

"Bashakka wato sagir akan bare tsuntatce kake wa yar uwar ka haka to wallahi kai bako ni'ima ba sa'ar auran ka bace kar ka ƙara shiga harkar ta ,

Ƙasa ma'aruf yayi da kansa a zuciyarsa sa yace yanzu haka talaka ke shan wahalar neman aure ni kuwa nace

(Mata suna suka tara akwai wacce zata soka tsakani da Allah ba dan kuɗin ka ba ko kyahun ka ba )

Ma'aruf yace

"Insha Allah mama ki haƙuri,

Wani shegen kallo ta watsa mai tace

"Jeka can ka nemo uwarka,

Sosai ya ji zafin maganar ta amma sai ya danne yayi shiru

Sagir yace

"Dan Allah oga Kai haƙuri,

Murmushi yayi yace

"Bakomai,

Satin sa daya yana harkar adaidaita sahu yau yafi ta duk rigar sa akoɗe wasu kyawawan yan matane suka tare shi dayar ta yatsuna fuska tace

"Kan karofi zaka kai mu,

To yace ku shiga amma kuɗin ku dari ne

Banza sukai mai suka shiga hamziyya da taga rainin hankalin sa ya ishe ta tace

"Amfa da maka kowa faƙiri ne irin ka kaga mun ma kama da wayan da zamuyi cini ki,

banza yayi musu ya fara tafiya dayar tace

"Sister we kin kuwa jj har yanzu ba wanda yasan asalin fuskarsa gayan Nan sai kuɗi ba aure kisan su ukku ne maza biyu mace daya zata ga gata yasin,

Hamziyyah tayi sama da glasses ɗin ta tace

"Ke dan Allah kawata Wallahi Allah ya dora min son mutumin nan ,

Surayyah tace

"Ke hamziyyah ki ka de ai nima wallahi ina son sa da zan aure shi so nake ,

Jin abin da suke faɗi yace
Chapter 8 · 0% Book details