← Book details Yadin Mage Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 15

Sashe 5

Yadin Mage Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haba sani dillali jiya fa sai da naje gun D.P.O sabon da aka kawo na bashi cin hanci akan duk ƙarar da aka kawo mai ya koreta akan mu ka daure ka amshi sha takwas dubu goma kuma zanyi dan wani abubuwan da ita

Wanne D.p.o?"

Na kan gaggare mana a she shima namune daman ina tararrabi da ɗayan ya sauka ban san wa za akawo ba ashe dan uwan mune

aa aa lamarin nan yayi min daɗi kaga sai muyi ta sheƙa ayarmu

wallahi kuwa na shega ukku ina zan ɓoya kamar sabeerin nake gani ƙar ta ganni tace daman nu ba ƙanin jj bane me yaka hota gidan su ruma

yaro kenan ai komu daɗe ko mujima wataran halinka zai bayyana kawe ka mazai

Neman makafa yake amma lahin ba wani lungu da zai boya *…………✍🏼*

*YA ƊIN MAGE*

*by*

*OUM YASMEEN*

*Part 15-26*

Iya tashin hankali ya shi ga wani gida ya shiga ya ɓoye yayin da sabireen ta faka motar ta a kofar gidan inna zulai fitowa tayi tana hura hanci domin yau Allah ne kaɗe yasan irin tashin hankalin da ta zo da shi

cikin gidan kamar anjefota tsayawa tayi ta ruƙe ƙugu na inna zulai ta fito daga banɗaki hannunta ruƙe da buta ɗurƙusawa tayi zata ajiye butar hannunta sukai ido hudu da da sabeerin dafe kirji tayi tace

"Yar nema ashe ke ce kika shigo mana ba sallama ko wallahi kin tsoratani?,

Wani ƙallon ƙasƙanci sabeerin ta jefawa inna zulai tace

"Ina zeenaru ?,

Ɗagowa inna tayi domin jikinta yayi sanyi duk masifarta sai yau ta nemeta ta rasa yo ta haɗu da yaran zamani masu ido a tsakiyar ka hannunta tasa ta nuna mata ƙofar ɗakin zeenaru

Ya mutsa fuska sabeerin tayi ta kau da kai tace

"Am granny kiramin ita bazan iya shiga wannan gunba namayi ƙoƙarin iya shigowa gidan nan ko ya akai kuke iya rayuwa a gidan nan,

Banza inna zulai tayi mata ɗokin ƙofar ɗakinta ta zauna ta zuba ta gumi wai yau ƴar bilyaminu ce take aiƙenta har tana ƙƴamatar ta kahu isane ya shigo yace

"Aa yau manyan baƙine a gidan namu ,

Wani kallon tara saura kata tayi mai ta saki ƙwai ya bada wani ƙas ƙass tace

"Yauwa isah waccar matar ta nunamin ba tasan inda matarka take ba amma kai nasan zaka iya sani ina neman ta ita da shegiyar yarta me ƙwacan saurayi ,

Kan kahu isane ya kulle duban inna yayi yana jiran yaji me zata ce

Ganin sun zama yawa andasa su ala Dole sabeerin ta ɗaga murya tace

"Zeenaruuu zeenaaaruuu!!,

Jin wannan kiran na mafarauta baba zeenaru da nuratu suka fito baki ta buɗe zatayi magana tace

"Sabeereen ce agidan nan lallai yau muna da manyan baƙi,

wani irin taku take na isa ta ƙarasa gabansu cikin raini da nuna ƙasƙanci sabeereen ta nuna baba zeenaru da yatsa tace

"Ki dahalla rufe min baki daman nazo ne akan ki jawa yarki ƙunne akan saurayi na in taƙi wallahi hukumace zata rabamu da ita zan iya ɓatar da ita kuma na ɓatar da banza ,

Cikin mamaki da tashin hankali baba zeenaru tace

"Sabeerin lafiya meke faru wallahi kin sani a duhu wa kike magana haka ?,

Bura'ubancan ni sabeereen yar Alhaji bilyamin nake magana kina cewa baki gane me nake magana akai ba to ina nufin saurayin nuratu

Kamar an dasa kahu isah yana tsaye yana kallon iƙon Allah yace

"Sabeereen muga photon sa iya sani na nuratu bata da saurayi me kuɗi tunda yanzu rayuwar kwarya tabi ƙwaryane ,

Wata harara sabeereen ta watsa mai ta nuna mai zaro ido yayi yace

"We Abdul me wankin mota dan gidan malam shehu me wankin hula to ai nadade da rabasu saboda ba dan arziki bane so yake ya lalatamin yarinya ,

Turusss sabeerin tayi tuni zuciyar ta ta shiga kaiwa da komowa daman ashe ƙarya yake mata biri yayi kama da mutum intace ya nuna mata pic ɗin jj yace ai baya son photo ko saudaya bata taɓa ganin family pic ɗin su ba maganar nuratu ce ta katsai mata tunani tace

"Aunty sabeereen kenan au ke daman baki san waye saurayin naki ba kika zo kina tada jijiyoyin huya ?,

Duban nuratu tayi tace

"Da hallacan matsamin yar marasa tarbiya,

Kahu isa zuciyarsa ta zo iya huya besa lokacin da ya ɗaga hannu ya mari sabeereen ba yace

"Sabeereen Ni ne mara tarbiyya to tarbiyyar da aka bani ita aka bawa mahaifin ki bilyaminu,

Cikin sauri Inna zulai ta tashi tace

"Isah zan ɓatar maka yi haƙuri sabeereen so kake ɗan balangwan nan da ake kawo mini a dena kawo min kai da ɗan uwan ka me mutuwar zuciya ba abinda kuke min,

Daman yasan za'a rina we ansaci zanin mahaukaciya yace

"Inna hi haƙuri yabar gidan Ita kuwa sabeereen kuka tasa tana tsinewa baba zeenaru da Kahu isah tabar gidan fuuuuu ta tada motar ta

______________________

Tun asubar fari ta tashi ta gyara gidan wanka tayi tasa wata atamfa brown colour da adon milk duk ta ɗan ji jiki hijabinta tasa ta fita gidan me koko da ƙosai fitowar ta ke nan suka haɗu da Usman yana goge a napep ɗinsa da sauri ta ɗauke ƙanta ta shiga gidan me koko

ta sami lahi raƙuɓewa tayi tana jiran lahi yazo kanta hankalin ta ya kasu kaso biyu tana tunanin ko abba ya tashi ne ko har yanzu yana bacci ga damuwa da tayi mata yawa

ji tayi me sai da koko da kosai tace

"Na nawa zaki siya,

Kuɗin ta ciro tace

"Kokon hamsin ƙosai dari biyu,

Amsa tayi ta ƙirga mata nanah ce ta shigo tana ganin samha tace

"Inna delah kina da tsakin kuka ki sauri ki zuba a huta tun kafin a lashe miki masu siyan koko da ƙosai dan ni wallahi nafi ƙarfin mace ƙurwata da ɗaci,

Me ƙosai ta yi dariya tace

"Uhmm aikuwa bara in sauri in sallami mutum ,

Hawaye suka taru a idaunta miƙa hannu tayi ta ƙarɓa yau daban ace tana da wasu kuɗin ba bazata amshi wannan koko da ƙosan ba juyawa tayi ta bar gidan da dan saurinta wani irin ƙuncine ya mamaye zuciyar ta ta rasa in da zata tsoma ranta taji dadi dai daita nutsuwar ta tayi ta shiga gida

Abin mamaki baya ƙarewa inna hajara da ita da abokanan iya shegenta har sun fito ta fara suyar waina kenan ba zata kotun ba kenan ganin bata da me bata amsa tayi sauri ta shiga gida mahaifinta tagani a zaune cikin murna tace

"Abba da kanka ka zauna?,

Murmushi yayi yace

"Samha iƙon Allah yau ji nayi yawa an ƙunce min wani abu a jikina kin ga aikin addu'a ko ina zaune naga wani kadangare ya fito gada ginin can da ya tsage yana ƙoƙarin cizon ƙafata shine na dinga karanto ayoyin neman tsari daga shedanu ko abokin gaba Allah ya bani sa'a na dauki sandar can na buga mai ina buga mai ya mutu ya buɗe bakinsa ga laya can ta fito a bakin sa shine fa na iya tashi har bayi na shiga,

Wani farin ciki ne ya mamaye zuciyarta tace

"Alhmdllh dukkan wani tsanani baya tabbata face Allah ya yaye shi,

Murmushi yayi yace

"Hakane samha Allah ya kawo mana mafita,

Tashi tayi ta nemo kofi ta zuba koko ta miƙa mai da ƙosai ta dauki nata

_________Hyde park Chicago - America

Yau an tashi da sanyi ga wata irin dusar ƙanƙara da take sauka tafiya yake cikin titin Woodlawn avenue tsayar da motar sa yayi kusa da robie house

ya dauki wayar sa yayi yan danne danne ya ƙara a kunne ba adade ba ya dauka cikin harshen Hausa yace

"Assalamu alaikum sa'id nazo kana ciki ne ?,

Daga can akace

"Wa'alaikassalam JJ ina ciki gani nan fito wa ,

Okay yace ya kashe wayarsa ba adade ba sai ga wani magidanci ya fito ba haushe zam motar ya buɗe ya shiga gidan gaba yace

"J.j kaga dan kasuwa yawa wani sarki,

Furzar da iska yayi ya cire facemask ɗin fuskar sa duk da motar sa baƙin glass ne amma ko mene da lilin da yasa ya rufe fuskarsa tambayar da nayi Wa kaina kenan amma ba me bani amsa yace

"Sa'id bazan ɓoye maka damuwata ba kasan yanzu naje shopping naga wasu mutane na bina da alama akwai wanda yake bibiyata sai de ya makaro nan ba kamar Nigeria bace ungo wannan ya dauko wata envelope yace ga number motar nan da picture motar kaimin binkice sannan a yau zani Nigeria zan bar ƙasar Nan ,

Ƙarɓa yayi yace

"Yauwa ma'aruf kenan ka dau shawarata wallahi in ba ta haka ba ba zaka taɓa samin wacce zata soka dan Allah ba wata ma za'a iya hada baki da ita akashe ka tunda kasan su Alhaji Abubakar ashirye suke su ɓatar da dukiyar su akan ka saboda ka fisu yawan masu siyan Kayanka da dilloli,

lips ɗinsa ya cize na ƙasa ya lumshe idanuwansa so nake in ganshi amma ba dama inaso inga wane j.j ɗin nan iya gefin fusƙarsa na gani yace

"Okay ai zalinci baya ɗorewa ina nan ina binkice akan su insha Allah na kusan gano inda ake kai dukiyar talaka abin mamaki shine kasan manfetur ɗin nan a kasar mu ake haƙoshi amma we ga yarda yayi tsada ya kamata shuwagabannin arewa su farka sudena ibarmana kuɗi su kai kashashan waje kasan jiya an kirani anmin gargaɗi in fita daga sabgar su sannan in rufe gidan jaridata in ba haka ba zan ƙi gani ,

Iska ya furzar me huce yace

"Amma ma'aruf kasan mutanan basu da imani ina zargin su suka turo yasmeen gunka dole ka ƙara sa ido a kan manir sosai kasan in basu same damar cutar da kai ba zasu ba iya cutar da shi ,

tissue yasa ya goge fuskarsa ya cire glass ɗin sa yace

"Ni yanzu ma hankali na be kwanta ba da zamanshi a Pilsen nan zai dawo da zama,

Okay no problem

Fita yayi tada motar sa yayi cikin sirri ya nufi international airport ya hau prevent jack sai kano

__________________________
Chapter 5 · 0% Book details