← Book details Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 14

Sashe 9

Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"ÆŠan sanda ne". Ta faÉ—a tana ajiye wayar ta zauna tana dafe kai, don ta tsani a katse mata bacci.

Ba ta lura da daskarewar da Aliyyu ya yi ba, sai da ta ji cikin tashin hankali ya ce"ÆŠan sanda fa kika ce! Hajiya me na yi miki?"

Ta kalle shi ta kwashe da dariya ta ce"Aliyyu kenan!"

ANA TA TAMBAYATA WAI WANI AUREN NA KUÆŠI NE? E NA KUÆŠI NE, A KAN NAIRA 300 KACAL!

08028966015
[8/19, 5:28 PM] Sadiya Abdulrazak: *WANI AUREN*

BY
SADIYA ABDULRAZAƘ

FIRST CLASS WRITERS

PAGE 6

https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h

*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Serious buyers pls*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅

ALI

Sosai ya shiga tashin hankali, kamar zai yi kuka ya ce"Hajiya me na yi miki don Allah za ki saka mini da wannan?"

Ta yi dariya ta ce"Ni kuwa ko butulu ce ai ba zan saka maka da sharri ba a yau, ko don faranta min da ka yi, haka kake da tsoro? Idan ka fita yanzu za a iya kama ka da laifin yawon dare, shi yasa zan saka ÆŠan sanda ya mayar da kai har gida".

Ya sauke ajiyar zuciya duk da haka bai samu nutsuwa ba, Hajiya ta ce"A gaskiya Aliyyu wannan matar taka ta yi dace, ina ma ina da damar yin wani auren! Ai da kai zan aura, don Allah gobe ma ka zo ka ji?"

Ya ce"Hajiya kenan, ki bar ni na fara fita daga bala'in da na shiga yau, kafin komai ya biyo baya".

Ta ce"Bala'i kamar ya?"

Ya ce"Daga baya zan ba ki kabarin wace ce matata". Suka yi shiru, har Ɗan sandan ya kira ta ya ce ya ƙaraso, suka fita tare Ali ya hau bayan babur ɗinsa ya kai shi har ƙofar gida, ƙirjinsa yana ta bugawa ya ɗakko waya ya kira lambar Maryam yana haɗawa da ƙwanƙwasa gidan.

Maryam da ba ta daɗe da yin bacci ba ta tashi a firgice jin ƙarar wayarta, tana dubawa ta ga shi ne, ƙwanƙwasa gidan da ake yi ne ya tabbatar mata da dawowarsa, ta duba lokaci ta ga ƙarfe biyu da mintuna, ta yi huci mai zafi zuciyarta tana ƙuna, ta sakko ta buɗe loka ta ɗakko mukullin shago ta shiga falo ta ɗakko tabarma tana buɗe gidan ta watsa masa ta mayar da sakata.

"Maryam!" Ya kira sunanta yana buga ƙofar, amma ko waige ba ta yi ba, ta koma ɗakinta, zama ta yi a kan gadon tana tunanin wace rayuwa mijinta yake son faɗawa? Zargi ne kala-kala yake ɗarsuwa a ranta, ciki har da na neman matan, amma ta saka a ranta ko ma mene ne ya zo ƙarshe daga yau, ta share hawayen da ya zubo mata, duk yadda yake buga gidan ba ta sake bi ta kansa ba, ta kwanta da baƙinciki tare da fargabar sabuwar rayuwar da ya ɗakko.

Shi kuwa Ali sosai ransa ya ɓaci, don tun da take cewa za ta ba shi tabarma ya kwana a waje bai taɓa zaton za ta iya aikatawa ba, sai ga shi ya ga zahiri, haskawa ya yi ya ɗauki mukullin ya buɗe ƙaramin shagon dake manne da gidan, ya shiga da bisimillah, duk ya yi ƙura don ba a taɓa kwana a cikinsa ba ma, haka ya shimfiɗa tabarma ya zauna, ya yi jugum yana nadamar wannan rayuwar da yake yi, ga shi aurensu ko shekara bai yi ba za su fara samun matsala, ya san gobe Allah ne kaɗai ya san irin bidirin da za su sha da Maryam, sai dai duk rintse ba zai yarda ta tafi gida ba, idan ta je ta faɗi dalili a ka titsiye shi da tambayar inda ya je me zai ce? Da wannan tunanin ya kwanta ya yi matashi da hannunsa, sai dai ya kasa bacci duk da babu sauro, tunani yake yi yanzu ya baro lafiyayyiyar katifa a makeke gado cikin AC, cikin abin da bai fi minti talatin ba rayuwarsa ta canza ga shi kwance a tabarma cikin ɗaki mai ƙura.

Tashi zaune ya yi, ya lumshe ido yana tuna duk abubuwan da suka wakana a daren na yau, tsakaninsa da Hajiyar da ko sunanta ba ta faɗa masa ba, yana buƙatar kuɗi kuma ya ga alamar zai samu alkhairi sosai ta wajanta, muddin ya kwantar da kai, saboda haka dole a yi ɗaya cikin biyu, ko dai ya nunawa Maryam dole ta yarda da cewar ya samu sabon aikin dare na gadi a wani kamfani ko kuma ita Hajiyar ta yarda ya dinga zuwar mata da rana, sai ya dinga tashi daga aikinsa da wuri, idan ya tara abin da yake nema sai ya rabu da ita, da wannan tunanin zuciyarsa ta nutsu, ya ɗakko waya ya kira ta don ya sake yi mata godiyar kuɗin, sai dai ba ta ɗauka ba, ya kunna data yana duba saƙonni, sai wajen uku da rabi ya yi bacci.

Da safe ƙarfe shida ya farka, ya fito ya ci gaba da buga gidan, ta ƙi buɗewa, ya kira wayarta sai ta ɗauka, ya ce"Maryam ki buɗe min alwala zan yi".

Ta ƙashe wayar, ta zo ta buɗe, ya shigo a sanyaye ta kalle shi ta kau da kai, ya yi alwala ya yi sallah, yana zaune a falo ya ga ta ɗora tukunya, sannan ta koma ɗakin gado, ya tashi ya bi ta, yana shiga ya ga tana birkito kayan cikin sif tana watso su kan gado, ya ƙarasa ya tsaya a gabanta ya ce"Maryam mene ne haka? Wai me yasa kike sha'awar yin yaji ne? Ko ba ki san abun kunya ba ne? Yanzu ko cewa na yi ki tafi gida sai ki tafi ɗin? Sai ka ce kin manta da muna da magauta masu jiran su ga ranar da za ki yi nadamar aurena? Haba Maryam, komai fa nake yi dominki ne, na san tun farko na yi kuskure da na ɓoye miki abin da ya kamata a ce kin sani".

Ganin ta ba da ni nutsuwarta, ya sa na zaunar da ita, ni ma na zauna na ci gaba"Maryam tsakani da Allah wani aiki ne na samu, na gadi da za mu dinga yi ni da a Hamza a wani kamfani, mu ne masu night duty, to shi ne dalilin kai wa daren da na yi jiya, ba a tashi ba ma na gudo saboda na san ba za ki samu nutsuwa ba, tun da ba ki san inda nake ba".

Har yanzu ba ta ce komai ba.

Ya ce"Gani na yi kuÉ—in da za su dinga biya da kauri shi yasa, kin ga fa kullum dubu uku, kin ga ai za mu toshe wani wajen ko?"

Sosai ta yarda da shi, amma ba ta jin za ta yarda da wannan aikin daren, ta kalle shi ta ce"Yanzu saboda dubu uku za ka dinga kwana a waje kullum? Da rana kuma ka tafi wani aikin? Shi kenan ba ka da lokacin hutu? Shi baccin da wane lokaci za ka dinga yi? Tara shi za ka yi ya zame maka matsalar da sai ka sha maganin da ya ninka dubu uku sau goma? Ina ta faÉ—a maka zafin nema ba ya kawo samu, saboda haka ka kwantar da hankalinka, indai ni ce kar ka damu, ba ga shi ina sana'ata ba? Idan nauyin gidan ne ya maka yawa zama ya kamata mu yi mu tsara komai na san ta inda zan rage maka nauyi, ko magi da kayan miya ne, ba wai ka É—auki wannan matakin ba".

Ya ji daÉ—in yadda ta yarda da shi sosai, ya ce"Na gode Allah da ya ba ni mace ta gari, Maryam Allah Ya biya ki da gidan aljanna, yanzu dai aikin ne ba kya so ko?"

Ta ce"E gaskiya ban yarda da shi ba".

Ya ce"Dama shi komai ɗan maslaha ne, in sha Allah na haƙura, sannan Maryam ni ban amince ki taimake ni da abin da yake nauyina ba, zan dinga yi miki komai daidai ƙarfina, fatana dai mu samu zaman lafiya da farinciki mai ɗorewa".

Tana murmushi ta ce"Allah Ya dawwamar mana".

Ya ce"Yanzu dai tun da komai ya wuce shi kenan babu sauran rigima ko?"

Ta ce"Da saura fa".

Ya ce"To me kuma ya faru?"

Ta ce"A gaskiya wannan majalisar taku ba na sonta kwata-kwata, kawai ana idar da sallar magriba ka dawo gida mu zauna ina buƙatar ganinka, mu yi fira na yi maka kwalliya kuma ka samu isasshen bacci".

Ya yi dariya ya ce"An gama ranki ya daÉ—e, in sha Allah yau ana magriba za ki gan ni".

Daga haka ta fita ta sauke shayinta, suka karya ransu fes, ya fita aiki cikin kwanciyar hankali.

GIDAN SADIQ

Da Sadiq ya dawo ta yi masa bayanin duk yadda komai zai kasance da ƴar aikinsu, ya amince ba don ransa yana so ba, sai dai a zauna lafiya kawai. Washegari da safe Yusra ta tafi aiki, don ta riga yaran fita a gida ta bar su da Sadiq, wajan ƙarfe takwas yana shago sai ga yarinya ta shigo, ta gaishe shi, ya yi zaton ma wani abu za ta siya, ganin ta yi shiru tana sunkuyar da kai ya ce"Me kike so?"

Ta ce"Mukulli na zo karɓa, ni ce Kursum, sabuwar mai aikinku".

"Ok" Ya faɗa yana kallon yanayinta, sannan ya ɗakko ya ba ta, ta duƙa ta karɓa ta ce"Na gode, sai anjima". Ta fice.
Chapter 9 · 0% Book details