← Book details Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 14

Sashe 3

Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ƙyar Maryam ta iya tashin Ali ya tafi masallaci sallar asuba, saboda nauyin da bacci yake yi masa, amma da ya idar da sallah sai da ya zauna a masallacin ya kunna data, ya dudduba saƙonni, lambar Baby Farha ya duba ya ga ba ta hau online ba, ya yi murmushi yana ayyana tana can tana bacci a cikin AC. Lokacin da ya dawo tana zaune a sallayar da ta idar da sallah, ya kwanta yana jira ta gama ita ma ta zo ta kwanta, ganin shiru ba ta da niyyar tashi ya sa shi cewa"Love me kike yi ne? Jiranki fa nake"

Nan take ta haɗe rai, dama ta san kwanan zancen shiyasa ta zaɓi ta yi zamanta har gari ya yi haske ta fita ta dafa shayi, sai ga shi dai ba ta tsira ba, ita kam tana son mijinta, tana kishinsa sosai, amma ta tsani ya neme ta a shimfiɗa, wannan shi ne babbar matsalarta, a zatonta rashin sabo ne da farko amma yanzu ga shi har auren ya yi wata shida a haka ake, ta sani ba ta ba shi haƙƙinsa yadda ya kamata, kawai yana ƙyale ta ne saboda a zauna lafiya kuma ta san yana shakkarta, hakan kuwa ya samo asali ne ta yadda yake bala'in sonta, sannan ya kasa maza da dama kafin ya same ta, ciki kuwa har da waɗanda suka fi shi komai na rayuwa, a lokacin an zuga Maryam sosai a kan aurensu, masu rufin asiri suna sonta amma za ta auri kafinta wanda zai kai ta gidan haya, ta ce ita ta ji ta gani.

"Ko ba zan samu ba?" Ya tambaye ta yana karaya da lamarinta, shi mutum ne mai ƙarfin sha'awa, wanda har yake ganin hakan shi ne ƙaddararsa, don tun da ya fara sana'a yake samun na kashewa ya fara neman mata bisa shawarar abokai, a yadda suke faɗa masa, ai shi saurayi ne ko a shari'a idan an kama shi ma bulala ce kawai, kuma yana yin aure zai daina, hakan ne ma ya sa shi dagewa ya yi auren don ya samu cikakkiyar nutsuwa da halalinsa, sai kuma Allah Ya haɗa shi da mace mai gudunsa, sosai abun yake ci masa tuwo a ƙwarya, don haka ya kasa yakice wa kansa wannan halayar, ko chart ɗin batsa duk yana yi ne saboda ragewa kansa damuwar nan da kuma sabo.

Haka dai ta je gare shi ranta babu daɗi, kuma ya san yau a haka za ta wuni da ƙuncin nan, shi yasa idan aljihunsa da nauyi yake gwammacewa ya tafi wurin matan banza inda za a faranta masa ya biya, a haka ne har bashin dubu goma ya shiga tsakaninsa da Reza, wanda ba dan haka ba da dubu biyar ɗin da ya ba ta jiya sai dai ya yi musu buƙatun cikin gida, ita kuwa ƙarya da yake yi wa ƴan mata a waya dama halinsa ne, ba ma zai taɓa iya dainawa ba.

Suna gama karyawa ya tafi aiki, ita kuma ta shiga harkokinta na cikin gida, tun tana gida sana'arta ce kitso da ƙunshi kuma har yanzun ma tana yi ba ta watsar ba, gidan nata ba ya rabo da mata, maƙotanta masu sana'a ma duk nan ne majalisarsu, ana kitso ana kitsa gulma, don ma dai ana shakkarta don ba ta da wasa, sai dai ko ba ta gama ba magriba tana yi ta rufe sana'a, ta gyara gida ta ɗora girki sannan ta yi wanka ta yi kwalliya, ta jira dawowar mijinta, idan da abin da ta tsana bai wuce duhu ya yi ta ganta ita kaɗai ba, da ƙyar ta amince da cewar sai takwas da rabi zai dinga dawowa gida, kuma tana gotawa za ta fara mita tana kiransa a waya, idan ta gaji sai ta rufe gidan ta jira shi a ƙofar gida. Yau ma kamar kullum, ta gama komai ta idar da sallar isha'i, ta kame tana jiran dawowarsa.

Tun da Ali ya fita da safe, wajen aikinsa ya wuce, ya shiga aiki tuƙuru, babu zancen kula kira da plashing ɗin da ƴan mata suke yi masa, yawanci waɗanda ba su daɗe da haɗuwa ba ne suke kiransa, amma duk wacce suka daɗe ta san da cewa Aliyyu ba ya haɗa aikinsa da komai, idan yana office ba ya ɗaukar wayarsa sai ya fito, da haka yake neman na kanshi domin ya samu asirinsa ya rufu, wajen aikin babu nisa da gidan iyayensa, a nan yake zuwa ya ci abincin rana ko a aiko masa, sai magriba ya tashi daga aiki, sallah ya yi ya shiga gidansu suka taɓa fira da ƴan'uwa, sannan ya tafi majalisar unguwar bai jima da zama ba Reza ta kira shi, ya ɗauki wayar kamar zai yi kuka ya ce"Reza idan kin yi haƙuri ma ai zan kira ki".

Ta ce"To ina jiranka...".

Ya katse ta da faɗin"Ki ƙara min haƙuri don Allah, wallahi ba su samu ba, sai dai ko gobe".

Ta ce"Ali kar fa ka mai da ni Æ´ar iska".

Ya yi dariya ya ce"To da mece ce?"

Ta ce"Dariya ma kake yi kenan! Wallahi idan ban zo gidanka na tona maka asiri ba shegiya ce ni, É—an iska ka yi auren ma ba ka daina cin bashi ba".

Ali ya ce"Ni dai ki yi haƙuri, tsautsayi ne ya ja ni, da ba ki zage ni ba".

Ta ce"Ka nemi kuÉ—ina ka ba ni".

Ya ce"Gobe zan kawo miki in sha Allah!" Suka ajiye waya.

Ya fito daga sallar isha'i kenan sai ga kiran Maryam, yana É—auka ta ce"Na ji shiru, wallahi yunwa nake ji yau, don Allah ka dawo da wuri".

Bai ce komai ba ya kashe wayar, ya buga babur É—insa, abokansa suna ta yi masa tsiya, Madam ta yi kira, shi dai ya É—auki hanyar tafiya gida, yana takaicin yadda take kafa masa takunkumin nan, sai ta ce ba ta iya cin abinci ita kaÉ—ai, kuma ta yi ta kiransa tana ce masa yunwa take ji, ya dawo su ci.

Tana zaune tana kallo a waya ya same ta, ta yi masa sannu, ta kai masa ruwa ya yi wanka, sannan ta kawo musu abinci, suna cikin ci sai ga kira a wayarsa, sai da gabansa ya faɗi saboda harƙallar rashin gaskiya da yake yi, indai aka kira shi a gaban Maryam sai ya ji faɗuwar gaban nan, da ya ga abokinsa Hamza ne mai kiran sai ya ji dama-dama, ya ɗaga yana cewa"Hamza ya ne?"

Daga can ɓangaren Hamza ya ce"Wallahi aboki wani kaya ne mai zafi ya samu, sai ka gani dai ka fito muna bayan layinku".

Ƙirjinsa ya ba da rass, ya kalli Maryam wacce ta dakata da cin abincin ta kafe shi da ido, don duk a abokansa ta fi tsanar wannan Hamzan, tun da ta lura ya fi maƙale masa, kuma tana jin sautin wayar ta ji ana magana da kurman baƙi, ta fara tunanin wane kaya ne me zafi mijinta zai siya?

Tsam ya tashi zai fita, yana hello hello, alamar babu network, bai ankara ba ya ga Maryam ta ruƙo rigarsa ta zaunar da shi, ta yi masa nuni da abincin dake gabansu.

Cikin karaya ya ce"Hamza wai katakon ne aka samu masu kyau?"

Hamza ya ce"Kai dalla Malam ina yi maka zancen kaya kana ce min katako, wata mai zafi aka samu fa, kuma wallahi babu tsada..."

Da sauri Ali ya katse shi da faÉ—in"Au shadda? Ai sai ka ce min wannan shaddar da zan siya wa Maryam an samu, ka tsaya kwana-kwana?"

Hamza ya ce"Kana gida ne?"

Ali ya ce"Ina gida, amma ka ajiye min gobe za mu yi magana, duk da ba ni da kuÉ—in ma". Suka yi sallama, ya kalli Maryam yana sauke ajiyar zuciya, suka ci gaba da cin abincin tana auna maganganunsu a zuciyarta.

Yau ma dai gajiya ta yi da ƙarar radionsa ta je ta kwanta, hakan ya ba shi damar dulmiya duniyar wayarsa, ya yi mamaki da har Baby Farha ta fara yi masa zancen yaushe zai je gidansu? Hakan ya ba shi tabbacin ba ƴar ƙarya ba ce, don ƴan ƙarya yana cewa zai je suke kawo masa uzuri har a bar zancen, ya faɗa mata zai zo cikin satin, sai kuma ya fara tunanin kayan da zai saka, don hotunan da ya tura mata sun kwana biyu, yanzu kayan sun sha wanki, ya fara tunanin dole nan gaba ya fara aron kayan sakawa kafin ya ɗinka sababbi, da wannan tunanin ya yi bacci, bayan ya gama tashin kan ƴan mata da ƙarya.

GIDAN SADIQ

Yau tun magriba ya rufe shagon, ya je ya kwaso ƴaƴansa, saboda ba ya son barinsu a maƙotan nan don dai babu yadda zai yi ne kawai, gida suka shiga ya canza musu kaya, ya wanke unifom ɗin, sannan ya saka musu tuwo, shi ma ya saka, suna gamawa ya ɗakko littafansu babu home work sai ya yi musu bitar karatu, ya kunna musu surar da suke a islamiyya, suna saurara har bacci ya ɗauke su, a gida ya yi sallar isha'i, ya yi musu shimfiɗa suka kwanta ya tofe su da addu'a, sannan ya kira lambar Yusra har sau uku ba ta ɗauka ba, tun jiya yake cikin yanayi na buƙatuwa, amma babu yadda zai yi kamar dai gwauro, sau da yawa yakan yi tunanin duba shawararwarin da mahaifiyarsa take ba shi akan aikin Yusra, ko dai ya mata tilas ta ajiye ta kula da gidanta, ko shi ya ƙara aure, amma idan ya tuna yadda take da kishi sai ya kau da zancen, saboda yana ƙaunarta, ba ya son abin da zai kawo rabuwar kai a tsakaninsu, duk da ya san ba za a taɓa dawwama a haka ba, don hanyar da gidansa ta ɗakko ba mai ɓillewa ba ce, da wannan tunanin bacci ya ɗauke shi. Sai wajen sha ɗaya ya ji ringin ɗin wayarsa ya duba ya ga ita ce, kamar ya share sai kuma ya ɗaga don wataran takan dawo cikin daren ta ce ta gudo, jin tana tambayarsa ya gidan yara sun yi bacci? Kawai sai ya kashe wayar ma duka ya ci gaba da baccinsa.
Chapter 3 · 0% Book details