Sashe 12
Wani Auren Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata yarinya ce take turo masa massages kala-kala, na kulawa, tun yana sharewa har ta kai ya fara mayar da hankalinsa a kan saƙonninta, duk ranar da ba ta turo ba sai ya yi ta tunanin dalili, akwai lokacin da ta yi kwana uku ba ta tura masa saƙo ba, duk ya kasa sukuni, motsi kaɗan ya duba wayarsa, ranar na ukn sai ya kirata a waya, sosai ta nuna farincikinta, kuma ta faɗa masa ba ta da lafiya ne, jiya aka sallamo ta daga asibiti, kamar wasa tun daga ranar suka fara yin waya da yarinyar da ta ce sunanta Ummu, ta iya kalamai masu tsayawa a rai, sosai yake mamakin kansa, don bayan Yusra bai yi tunanin zai sake iya soyayya da wata ba, sai ga shi cikin sauƙi ya faɗa soyayya da wacce bai santa ba, kuma ko hotonta za ta turo masa sai dai ta rufe fuskarta, to shi ma a yanzu bai shiryawa wani auren ba, shi yasa ya bar ta a je a hakan, amma yarinyar ta yi masa har zuciyarsa, sosai suke waya musamman ranar da Yusra take aikin kwana.
[2/17, 10:32 AM] Sadiya abdulrazak: Follow the AUTAR MANYA CHANNEL channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VakTcGc5Ejy40GSTWA0h
*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Serious buyers pls*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅
GIDAN HARUNA
Ƙiri-ƙiri Haruna ya ƙi cewa Halima ta dawo, duk da ta faɗa masa jikin da sauƙi sosai, ita kuma mahaifiyarta tausayinta take ji, shi yasa ta ƙyale ta ta dinga hutawa, Halima har mamaki take yi yadda kullum idan zai zo ganinta sai ya taho da leda sannan ya ba ta kuɗin kashewa, sosai hakan ya yi mata daɗi, ta fara tunanin mijinta ya fara samu sosai a kasuwa, amma ta saka a ranta duk da haka ba za ta dakatar da sana'arta ba, za ta ci gaba da yi don a taru a rufawa juna asiri.
Bayan kwana uku suka shirya da Zainab, har ma suka shirya yau ma za su haɗu a ɗakinsa, don haka da daddare ƙarfe ɗaya Zainab ta tashi saɗaf-saɗaf, ta shige ɗakinsa, ta saka sakata, suka fara sha'aninsu, bai fi minti goma da shigarta ba Baaba ta tashi don yin fitsari, ta ji ɗakin a buɗe duk da ta san da kanta ta saka sakata, kuma Zainab ba ta tashi fitsarin dare, sai ta yi tunanin ko yau ta tashi ne tana banɗaki, ganin butarsu a yadda ta ajiyeta ma bai sa ta yi wani tunanin ba, ta ɗauka ta je ƙofar banɗaki ta tsaya tana jiran fitowarta, jin shiru ba ta da niyyar fitowa ya sa ta cewa"Da mutum?" Ta ji shiru, ta bubbuga ƙofar nan ma shiru, sai ta leƙa a hankali tana haskawa ta ga wayam babu kowa, ƙirjinta ya bada sautin rass ta fara tunanin ina Zainab za ta tafi cikin daren nan? Ta shiga ta yi fitsarinta, ta yi zaure ta ga ƙofar gida a rufe tsaf, gabanta sai faɗuwa yake yi, ta dawo ta shiga ɗaki wai ta ƙara dubawa ko idonta ne ya nuna mata Zainab ba ta nan, amma ganin ko bargo babu a kan shimfiɗar ballantana a yi tunanin ta lafe a ciki ya sa ta saddaƙar wani abu ya samu jikarta, tuni ta fara hawaye, zuciyarta tana bugawa.
Kamar ta tashi Haruna ta faɗa masa halin da take ciki, sai kuma ta fasa, don tana tunanin samari ne suka hure mata kunne ta gudu bariki, sai ta miƙe zumbur ta shiga ɗaki ta duba kayan sakawar Zainab, ta gansu tsaf babu alamar an ɗauki wani abun, har hijjabin da ta yi sallar isha'i ma yana nan a inda ta bar shi, Baaba ta dawo tsakar gida ta zauna a kujera tana matsar ƙwalla.
A firgice ta ɗago jin an buɗe ɗakin Halima, ta miƙe tsaye don ta samu damar da za ta faɗawa Haruna, ya je ya dubo ko ba ta yi nisa ba ya faffalla mata mari ya dawo da ita, sai dai ta yi turus ganin mace ce ta fito, cikin sakan ɗaya ta yi tunanin ko Halima ta dawo tana bacci? Amma ganin wacce ta fito ɗin ta doshi ɗakinta gadan-gadan ya sa ta yi saurin kunna fitarta hannunta na rawa.
A firgice Zainab ta juyo ganin an haskata, ƙirjinta ya buga da ƙarfi ganin Baaba ce a tsaye. Baaba kuwa sakin fitilar ta yi, ta dafe ƙirji, cikin razani ta ce"Zainab! Me kika yi a ɗakin Halima?"
Cikin inda-inda ta ce"Caji na saka fa Baaba".
Baaba ta ce"Bantan ubanki ke da cajin" Sai ta ƙaraso ta rufe ta da duka, kafin ta saketa ta fashe da kuka, ta shige ɗaki. Ita ma Zainab ɗin shigowa ta yi, ta zauna rakuɓe a gefe tana hawayen nadama, can Baaba ta ce"Zainab yanzu shahararki a iskanci ta kai har da na gida? Har cikin gida, da mijin maƙociyarmu? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!".
Zainab tana kuka ta ce"Ki yi haƙuri Baaba, wallahi iya yau ne kawai, kuma mun yi na farko mun yi na ƙarshe".
Baaba ta ce"Amma wannan yaron an yi É—an banza, Allah sarki Halima ashe ba ta yi dacen miji ba, kaico! Da halinku ke da shi É—in, sai Allah Ya sakawa Halima".
Sai kuma ta tashi, ta je ta fara ƙwanƙwasa ɗakin Haruna, don Zainab tana fita ya saka sakata, ya yi lakur saboda yana jiyo tattaunawarsu sama-sama, gabansa ya faɗi da ƙarfi da ya ji ana buga ƙofar, kamar kar ya buɗe sai kuma ya daure zuciyarsa ya buɗe, cikin karaya ya ce"Baaba ce da daren nan?"
Baaba ta ce"Haruna ka ji tsoron Allah! Ka sani akwai mutuwa, akwai hisabi, sannan zina bashi ce, kuma duk wanda yake cin amanar aure ba zai yi kyakkyawan ƙarshe ba in sha Allah!".
Cikin ƙarfin hali ya ce"Mene ne ya faru ne Baaba?"
A fusace ta ce"Uwarka ce ta faru da ubanka! Me ya kawo Zainab É—akinka da daren nan?"
Ya ce"Wai Zainab? Wallahi zuwa ta yi, ta ce min wayarta babu kuÉ—i, na kira mata Halima za ta tambaye ta wani abu, akan sana'ar da take taya ta".
Baaba ta ce"Ita kuma ta ce caji ta saka, babu komai Haruna duniya ce ta fi bagaruwa iya jima! Idan ni da Halima muna da hakki akan cutarwar da kuke yi mana Allah Ya saka mana tun a duniya".
Daga haka ta shige ɗakinta, ta bar shi riƙe da ƙofa, jiki a mace kamar kazar da ta taka wuƙa ya dawo ya zauna a kujera yana dafe kansa, ya jima a haka sannan ya tashi ya saka sakata ya koma ya kwanta.
Washegari safe Zainab ta tashi ta shiga harkokin wainarta kamar ba a yi komai ba, saɓanin Haruna da ya kasa fitowa sai da suka yi chart ta faɗa masa babu komai ya maze kawai, kuma haɗuwa yanzu ma suka fara, ta samo musu wata dabara, wannan ne ya ba shi ƙwarin gwiwa ya saki jikinsa, har ya fice daga gidan.
Ita kuwa Baaba ƙarfe goma na safe ta shirya ta tafi gidan su Halima, suka gaisa ta cewa babarta ta zo tafiya da Halima ne, Umma tana murmushi ta ce"Ai Baaba gani na yi har yanzu bai ce ta koma ba, shi yasa na barta ta ƙara hutawa".
Baaba ta ce"Haba Æ´ar nan, ku kuma ai ya kamata ku gane kara ce yake yi, sai ka ce laulayin kanta ne farau? Kuma fa Æ´ata Halima ai jaruma ce, ni dai yau da ita zan koma gidan nan Allah kuwa".
Umma ta ce"To kin ji dai Halima, sai ki tashi ki shirya, bari na je kasuwa na yi miki Æ´ar siyayya, idan na dawo sai ki bi Baaba ku tafi, ka samu mai kula da lamarinka ma ai abun murna ne, mun gode Baaba".
Bayan ta tafi kasuwa suka dinga fira da Halima tana ta jaddada mata ta riƙe mijinta, ta dinga saka ido sosai a kan shi saboda ƴan matan zamani ba su da kirki, a haka har Umma ta dawo, Baaba ta saka ta a gaba suka koma.
Ita kanta Baaba sai da ta yi mamakin yadda Zainab ta nuna ko a jikinta, ita ta gyara mata ɗakinta fess tana ta yi mata sannu. Haruna bai san da dawowarta ba, da yake akwai mukulli a hannunta, sai dawowa ya yi ya tarar da ita, ya ɗan ji daɗi saboda dama yana shakkar dabarar Zainab duk da shi ma ya san ba abu ba ne mai sauƙi yadda ya saba da ita su rabu lokaci ɗaya, amma tun da Baaba ta san komai ya zama dole su canza taku idan ma za a kuma ɗin, da wannan ya saki jiki da Halima har suka taɓa fira kafin ta yi bacci.
GIDAN ALI
A cikin satin Ali ya zowa da Maryam sabon labari, na cewar wani kamfani a can Enugu zai ɗauke su aiki na sati ɗaya, kullum dubu goma, kuma su ne za su yi musu kuɗin mota,masauki da abinci bakiɗaya, ganin ta ɓata rai ya sa shi tausasa murya ya ce"Maryam don Allah idan na zo mana da abun alkhairi ki daina gwasale ni, ki dinga yin fatan alkhairi kawai, kwana bakwai fa kacal za mu yi, dubu saba'in ina laifi? Ba sai na yi miki kayan sallah a ciki ba?"
Ta ce"Ni fa ba aikin ne ba na so ba, garin ya yi nisa, kuma har kwana bakwai".